Ina ga lokacin da zamu
gaya wa kanmu gaskiya ya yi. Halin da al’umma kasar Hausa suka samu kansu ya ta’azzara.
Duk wanda zai ce Arewa ba a cikin talauci da fatara da jahilci, ya yaudari kansa,
kuma bai yi wa kasar Hausa adalci ba. A yadda magabata suka fada idan mutum yana
da wata cuta kuma ya ki yarda yana da ita to ya shiga ukuba, kuma samun
saukinsa abu ne mai wuya a gurinsa. Amma da zarar ya yarda yana da ciwon, to
ana tsammanin sauki ya samu. Ko ba komai ya san me yake damunsa kuma zai tashi
ya nemi magani.
Babu dadi ga yadda wasu
tsirarrun mutane ke kokarin gurbata tunani jama’a, watakila don neman suna ko
wata bukata tasu ta daban da su suka santa. Amma ina mai tabbatarwa irin
wadannan mutane cewa idan guguwar canji ta taso bubu wani abu da zai iya tare
ta. Allah ubangiji shi ne zamani kuma shi yake juya zamani yadda ya so.
Mai martaba Sarkin
Kano, Muhammad Sanusi II, ya yi jawabai a kan fahimtarsa bisa halin da muke
ciki da yadda za a samu waraka. Kuma bana jin ya ce lalle sai an bi abin da ya
fahimta. Bukatarsa ita ce a zauna a
kalli abin da ya kawo da idon basira. Abin da ban ji dadi ba shi ne yadda aka mayar da abin cin mutunci da
tozartarwa da izgilanci. Mai makon abin ya zamo bisa doron ilimi da tattunawa
ta fahimta tsakanin shugabanni da malamai da sauran al’umma.
Ban ga dalilin da jama’a
zasu yi tariyar baya ba su dauko wata mahawara tsakanin mai martaba Sarki da marigayi
Sheikh Jafar Muhammad Adam, rahimullah. Wannan ya nuna jahilci da kokarin tada
zaune tsaye. Muhawara ce aka yi lokaci mai tsayi da ya shude, kuma wanda suka
yi ta suka fahimci junansu abin ya wuce kafin rasuwar Malam. Shin suna ganin
sun yi wa Malam adalci da suka bijiro da wannan al’amari wanda ba shi da alaka
da abin ake ciki a yanzu?
A satin da ya gabata mai
martaba Sarki ya tura ‘yarsa Shahida ta wakilce shi a kan taron tunawa da ‘yan
matan Chibok da aka sace aka yi garkuwa da su. Ga masu hangen nesa sun ga
wannan wakilci a matsayin abin da ya dace, kasancewar taro ne da zai waiwayi batun
yaran wadanda suke kusan sa’oi ga Shahida. Ni ina ganin hikimar wannan zai
tunawa jama’a cewa iyayen wannan yara sun tura ‘ya’yansu neman ilimi, kuma
burinsu su samu ilimi kamar yadda Shahida ta samu har ta iya yin wannan
wakilci. Ashe mutane jira suke su ga ta inda za su yi cin mutuncinsu, sai wanda
suke zato bai halarta ba. Wannan yasa suka juya ta wani bangaren cewa suturar
da yarinyar ta sa ba su dace ba. Ashe dama yanzu ba irin kayan da ‘ya’yan mu da
kannen mu da yayyen mu mata suke sa wa ba?
Mai
martaba ba zai zamo ma’asumi ba, a matsayinsa na adam yana da tashi gazawar.
Amma a wannan hali muna bukatar gudunmawarsa don fitar da A’i daga rogo. Ai tun
tuni dama mutanen Kano mutane da basa karbar sauyi cikin sauki (conservative),
ba jayayya a wannan. Amma idan har suka karba suna rinjayar sauran bangarori na
kasar Hausa. Ina ji a jikina wannan guguwa da ta taso zata yi tasiri wajen
sauya tunanin jama’a da tabbar al’umma ingantatciya.
A
ganin wasu jama’a shi mai martaba Sarki bai kamata ya shiga wannan al’amari ba.
To, wai idan irinsu ba su shige mana gaba ba su waye zasu tsamo arewa daga
halin da take ciki. Wadanda ake sa ran su zasu yi wa Arewa gata sune wadanda
suka kara jefa ta a rami. Tun da magabata irin su Ahmadu Bello (Sardaunan
Sakkwato) suka gabata, shugabannin da suka gajesu ba su yi wa Arewa abin da ya
kamata ba. Da sun rike matsayinsu na magadan su Sardauna da Aminu Kano da ba mu
shiga wannan hali da muke ciki ba. Arewa ta rasa jagoranci na gaskiya. A yau su
wanene shugabannin Arewa? Ban ga wani shugaba ba da zai fito ya ce a yi gabas,
gaba daya mutane su bi kamar yadda muke gani a kabilu kamar na yarabawa. Shin
irin wadannan mutanen da basu tsinanawa Arewa komai ba ake sa ran za su goyi
bayan sabon tunani?
Lokaci ya yi da za a daina kallon maganar gaskiya a matsayin siyasa. Komai a ce siyasa kamar mu muka fi kowa siyasa, amma mun rike kaho wasu tsirari na tatsa. Duk siyasar ta mu yau kusan shekara hamsin da bakwai da karbar mulkin kai amma har yanzu bamu iya samar da ilimi da lafiya da abin yi ga dinbin al’ummar mu ba. Su kansu alkaluma da ake fitarwa da suka nuna tsananin talauci da fatara gami da rashawa da cin hanci da suka yi mana katutu, wasu na ganin siyasa ne ko kuma tonon asiri. Ya ilahi, dama haka ake gina kishin kasa a kasashen da suka cigaba har muke sha’awarsu?
Lokaci ya yi da za a daina kallon maganar gaskiya a matsayin siyasa. Komai a ce siyasa kamar mu muka fi kowa siyasa, amma mun rike kaho wasu tsirari na tatsa. Duk siyasar ta mu yau kusan shekara hamsin da bakwai da karbar mulkin kai amma har yanzu bamu iya samar da ilimi da lafiya da abin yi ga dinbin al’ummar mu ba. Su kansu alkaluma da ake fitarwa da suka nuna tsananin talauci da fatara gami da rashawa da cin hanci da suka yi mana katutu, wasu na ganin siyasa ne ko kuma tonon asiri. Ya ilahi, dama haka ake gina kishin kasa a kasashen da suka cigaba har muke sha’awarsu?
Muhammad
Sanusi II, shi ne Amir na Kano wanda Allah ya dorawa shugabancin mutanen Kano.
Babu wanda yake tantama cewa a matsayinsa na Sarkin Kano Allah zai tambaye shi
yadda ya gudanar da mulkin talakawansa duk cewa kundin mulkin kasa ya karbe
musu cikakken iko. Wai ance Sarki ya rage magana, amma kuma jama’a kullum na
turereniya kai kukansu gare shi na irin cin zarafi da tauye hakkin dan adam da
yake faruwa. Na tambata duk wanda ke cike da tausayi da imani idan ya ji irin
kwadon da ake damawa a wannan sashi na kasar nan sai zuciyarsa ta koka.
Kamar
yadda na ce mai martaba Sarki ba ma’asumi ba ne, mutum ne kamar kowa; amma kuma
Allah ya yi masa baiwa ta ilimi. Wannan ba yana nufin ina kare shi ba ne ido a
makance. A’a, akwai abubuwa da yadda ya fahimce su mun yi mun yi hannun riga da
shi. Misali, maganar samar da tashar jirgi ta zamani mai amfani da lantarki na
kalle ta a matsayin cigaba ga jihar Kano. Bana ganin bashi ne da za a karba a kashe
wajen biyar albashi ko wata sharholiya, na kalli yunkurin a matsayin abin da
zai samar da aikin yi sannan ya biya kansa bashin da aka ci masa. Amma ba na
shakkar mai martaba masanin tattalin arziki ne wanda ya nuna basirarsa lokacin
da duniya ta shiga masassarar tattalin arziki a shekarun baya; wanda Najeriya ba
ta ji radadin abin ba kamar sauran kasashe, sannan yunkurinsa ya tallafi bankunan
mu daga durkushewa. Wannan ba zai sa na kasa yi masa uziri don jin mai ya taka
da nashi ra’ayin.
Amma
ina mamaki a wannan zamani har wasu na tunanin a hana mai martaba Sarki magana.
Haba! A wannan karni na ashirin da daya, lalle muna da sauran aiki. Gaskiya wata
guguwa ce ta taso wanda Allah ne yasan inda za ta tsaya. Masu rike da madafan
iko akoyaushe ba sa son kan talakawa ya waye don gudun bore. Haba, Kano ce fa
wanda Malam Aminu Kano ya rayu a cikinta. Yau Malam Aminu Kano ya cika shekaru
talatin da hudu da rasuwa, amma abin kunya ne a ce irin wannan al’amari na
faruwa. Malam ya rasu ya bar riguna guda uku, mutumin da bai yarda an sa masa
janareto ba don kar ya damu makota da kara kuma bai basu wuta ba. Maganar Malam
akoyaushe ita ce talakawa da yadda za su samu waraka. Yau ina akidar NEPU wanda
tasa aka azabtar da kashe da yawa daga magoya bayan tafiyar. Shin zamu koma
lokaci ne da mata irin su Gambo Sawaba suka sha azaba da duka wanda har ya yi
sanadin fashewar mahaifarta?
Mutanen
Arewa na bukatar mutanen da zasu fada musu gaskiya ko mun dacinta. Arewa na
bukatar mutanen da zasu karfafi ilimi da bawa mata hakkinsu da musulunci ya
basu. Arewa na bukatar mutane da zasu taimaka wajen yakar zaman kashe wando da shaye-shaye
da miyagun ayyuka. Ba yadda za a fita daga wannan kangi idan shugabanni ba su yi
yunkurin samar da ilimi ga ‘ya’yan Arewa ba. Irin wannan yunkuri ne yasa mutane
irinsu Awolowo suka samu soyayyar mutanensu saboda ganin amfanin abin da suka
shuka.
A
lackar da aka gabatar don tunawa da Malam Aminu Kano a wannan shekara na ji
dadin abin da mataimakin gwamnan Kano Prof. Hafizu Abubakar ya ce yayin
jawabinsa. A cewarsa idan zamu gayawa kan mu gaskiya mun shiga wannan hali ne
ba wai kawai don watsar da akidar Malam ba kawai, har da watsi da dokikin
Allah. Wannan magana ce da ba kowane shugaba ba ne zai yarda da ita. Masu iya
magana na cewa ita karya fure ta ke bata ‘ya’ya, don haka duk wani kyalkyal na
fure da kamshinsa kar ya rude mu.
Daga
Zaharaddeen
Ibrahim Kallah
Zaharaddeen Ibrahim Kallah marubuci ne cikin harshen Hausa da Turanci. A halin yanzu shi ne shugaban Kungiyar Marubuta ta Najeriya, reshen jihar Kano.