Wednesday, 26 August 2020

Ranar Hausa: Amfani Da Harshen Hausa A Manyan Tarukan Afirka


 A yau 26 ga watan Agusta, 2020 ake bikin Ranar Hausa ta duniya. Wannan biki ana yinsa a duk ranar 26 ga watan Agusta na kowace shekara. 

Harshen Hausa na daga cikin manyan harsuna a duniya, wanda a halin yanzu shi ne harshe na 11 da aka tabbatar a duniya yana mai ɗinbin masu magana da shi.

Wani mizani da ake amfani da shi wajen gane cigaba da ɗaukakar harshe, shi ne adabin wannan al'umma. A yau Hausa na da ɗinbin rubuce-rubuce tare da marubuta maza da mata. 

Tarihin rubuce-rubucen Hausawa yana da faɗi kwarai, domin magabata irin su Usman Dan Fodiyo da Nana Asma'u da Abdullahi Gwandu da Muhammad Bello da sauransu sun yi waƙe cikin harshen Hausa, a ƙoƙarinsu na yayata addinin musulunci. Rubuce-rubucensu na cikin rukunin adabi a ɓangaren waƙe.

Ko lokacin da Turawan mulkin mallaka suka shigo ƙasar Hausa, sun ɗabbaƙa rubutun adabin Hausa na zamani, inda aka fara samun ƙirƙirarrun labarai. Duk da cewa marubuta irin su Abubakar Imam da Tafawa Balewa 'yan boko ne, amma an nemi su yi rubutunsu cikin harshen Hausa. Wataƙila hakan ne zai ba wa Turawa dama su fahimci Hausawa idan suka yi rubutu da harshensu, fiye da su yi amfani da harshen aro.

A wannan ƙarni na 21 da muke ciki, harshen Hausa ya samar da marubuta da zai yi wuya a kawo adadinsu cikin sauƙi. Duk da koma bayan da ake ganin mata na da shi a duniya a ɓangarorin rayuwa, zan iya cewa a duniyar rubutu sun yi nisa a ƙasar Hausa. Misali, a kaf Najeriya, babu wata jaha da za ta yi tarayya da jihar Kano a ɓangaren marubuta mata.

A wannan shekara ta 2020, taken bikin Ranar Hausa ta bana shi ne "Buƙatar Majalisar Ɗinkin Duniya da Ƙungiyar hada kan ƙasashen Afirka ta AU da ma Ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka ta ECOWAS su mayar da harshen Hausa a matsayin na sadarwa a ƙungiyoyin."

Wannan yunƙuri zai taimaka wajen haɓaka tattalin arziki da al'adun yanki, duba ga yadda ake amfani da harshen a yankunan nahiyar.

Wannan ranar dai ta samo asali ne a shekarar 2015, a lokacin da ma'aikacin sashen Hausa na BBC, Abdulbaki Aliyu Jari da wasu abokansa na shafukan sada zumunta, musamman Mazhun Idris suka ayyana wannan rana ta 26 ga watan Agusta a matsayin Ranar Hausa, wanda masu magana da harshen Hausa suke fitowa su tattauna akan harshen tare da kallon cigabansa ko ƙalubalen da yake fuskanta a wannan ƙarni.  

A shekarar 2018 ne aka fara gudanar da bukuwan Ranar Hausa a  zahiri, wanda aka yi shi a gidan Ɗan Hausa dake Kano da wasu ƙasashe a faɗin duniya.

A ƙarshe ina taya ɗinbin Hausawa a faɗin duniya murnar wannan rana, wacce take da mihimmanci wajen ɗabbaƙa harshe, al'adu da tattalin arzikin ƙasar Hausa. Zai yi kyau mu raya ranar ta yin rubutu cikin harshen Hausa da yayata shi. Shi dai kayan aro ba ya rufe katara.

Zaharaddeen Ibrahim Kallah

zikallah@gmail.com