Wednesday, 16 September 2020

Tun Ran Gini Tun Ran Zane: Lalacewar Tarbiyya Da Inda Aka Dosa

A yau mun wayi gari rayuwa a ƙasar Hausa ta sauya, tarbiyar yara ta lalace. Kawaici, yakana da kara da aka san mu da su, sun ɓalɓalce. Wannan ya sa muka shiga ruɗani, har ta kai muna neman manta su wane ne mu. A lokaci guda, fatara da talauci, sace-sace da zaman banza suka yi mana katutu.

A ƙasar Hausa, a ƙarni na 19 zuwa wani lokaci a ƙarni na 20, za ka ɗorawa tsohuwa kwarya cike da kuɗi ko gwala-gwalai daga wani ɓangare na gari zuwa ƙarshensa, ba tare da wani ya tare ta ba ya kwace. Amma yanzu ta kai akan bainar idon jama'a ne za a yi maka kwace ko fashi, babu wanda zai kawo maka ɗauki.

Shekaru kamar biyu baya, na ji muryar wani matashi yana kuka a gidan Freedom Radio, yana cewa a bakin ƙofar mata cikin cunkosa jiran a basu hannu, wasu matasa suka sa masa wuƙa akan ya basu wayar salularsa. 

Matashin ya yi ƙoƙarin yi musu gardama, ya fara kururuwa yana kiran ɗaukin jama'a, amma babu wanda ya kawo masa ɗauki. Nan suka yanke shi a hannu suka yi awon gaba da wayarsa. Hakan ya sa ya shigo gidan radiyon yana kuka, yake cewa "Kai jama'a, kamar ba garin musulmai ba."

Haƙiƙa da gaskiyarsa, garin Kano garin musulmi ne da aka gina shi abisa doron dangantaka da kyakkyawar makwabtaka. Abin da ya shafi makwabcinka ya shafeka gaba da baya. Tun daga tarbiyar yara, kasuwanci da tattalin arziƙi, da addini, tsaro da sauran abubuwan da suka shafi zamantakewa. 

To, amma yanzu abin ba haka yake ba. Tun da Turawan mulkin mallaka suka shigo Daular Usmaniyya, muka fara yin watsi da kyawawan ɗabi'u da al'adunmu. 

Duk wannan abin da ake, Turawan Birtaniya sun yi mulki ne na bayan fage, wato 'Indirect Rule'. Sun fahimci a lokacin irin matsalolin da za su fuskanta idan suka taɓa mana addini da al'adu.

A yau a karan kan mu, mun yi watsi da waɗannan kyawawan ɗabiu, mun rungumi na baƙin haure. Duk nacin mu fa, ba za mu iya zama Turawa ba, ko yin abin da suke a al'adunsu. Sai dai idan za mu sauka daga tsari da tarbiyar musulunci da ta iyaye da kakanni.

A wajen tarbiyyar 'ya'yanmu, a yau makwabci ba zai iya saka baki akan tarbiyar ɗan makwabcinsa ba. Sannan yaran makwabta za su iya zama ba karatun boko bare na addini, ba tare da damuwar makwabci ba.


Ta ɓangaren sana'a, ba ma koyawa 'ya'yan makwabta yadda za su dogara da kansu. Rayuwa ta zama kowa ya iya allonsa ya wanke.

Da yawan 'yan boko da suka zama baƙaƙen Turawa na jin haushi talakawa da ba su rungumi tsarin rayuwa na zamani ba. Ina da matata ɗaya da 'ya'ya uku, amma makwabcina ya tara mata huɗu da 'ya'ya ashirin a gidan haya, wanda wasu ma tare suke kwana da yaransa a ɗaki ɗaya.

Shi ma talaka na jin haushin 'yan boko kan cewa ba su da tausayi, kuma suna yi masa buƙulun jin daɗi ɗaya da yake morewa, na ya yi jima'i yadda yake so.

Wannan ya haifar da rashin jituwa da watsi da juna, har da kai an raunana makwabtaka, an wargaza harsashin tarbiya. 

Mun san yadda manzon Allah, Annabi Muhammadu (S.A.W) ya dinga bijirowa da sahabbai mihimmanci makwabtaka, har suka yi tsammani zai ce makwabci zai iya gadar makwabcisa.

Duk wannan sakacin da riƙon sakainar kashi da muka yi, shi ya kai mu ga halin da muke ciki a yanzu.

A yau matasa da suke da mafi rinjaye na yawan al'umarmu ba su da sana'a, uwa uba ba su samu cikakkiyar tarbiya ba. Wannan shi ya ƙara assasa shaye-shayen miyagun kwayoyi da suke taimakawa wajen aikata muggan laifuka.

A yanzu a garuruwanmu, musamman Kano da take babban birni kuma cibiyar mutanen Arewa, sace-sace da kwace a gurin waɗannan matasa ya ƙara ta'azzara. Akan wayar da ba ta fi N15,000 ba, za a iya kashe mutum. Satin da ya gabata mun ji labarin yadda aka kashe wani bawan Allah a unguwar Jan Bullo. Unguwar da ake ganin mazaunanta akasari ba talakawa ba ne tiƙis. 

Ta kai yanzu ana bada shawara ga mutane da su kiyayi bin wasu tituna a Kano a wasu lokuta, musamman lokutan da ƙafa ta ɗauke.

Bai fi sati biyu ba, ƙanina ya shigo babur ɗin A Daidaita Sahu, inda ya samu wata budurwa a ciki. Matuƙin babur ɗin na tare da abokinsa, wanda suke sawa a gefen direba. Suna tafe, sai wannan yarinya ta ce za ta sauka. Bayan ta sauka ne, mai babur din yake cewa abokinsa ai budurwar ga irin wayar da take riƙe da ita. 

Buɗar bakin da abokin zai yi, sai ya ce. "Ai ba ka gaya mun ba, amma wallahi da mun kwace ta." 

Jin haka ƙanina ya ce akwai mai sauka, nan ya sauka daga babur ɗin.

Wannan ita ce irin rayuwar da matasanmu ke faɗawa. Shin a haka za mu cigaba, shin me zai faru nan da shekaru ashirin masu zuwa? 

Dole mu sake tunani matuƙar muna son samun mafita.

Ana bawa mutane shawara akan yadda za su kare kan su, amma gaskiya abin ya wuce haka. Dole masana da shugabanni da duk.masu ruwa da tsaki su zauna babban taro da zai waiwayi matsalar da muke ciki, a tattauna tare da fitar da hanyoyi na ilimi da za a magance matsalar matasa. Sannan dole a zaɓi mutane da za su iya aiwatar da abin da aka fitar a bayan taron.

Duk inda za a kai a kawo, sai an yi ƙoƙarin kyautata zamantakewar mu, sannan a tsara yadda 'yan boko da masu arziƙi da talakawa za su fahimci juna, su yi aiki tare.

Dole ne mu fitar da yadda matasanmu za su samu ilimi da sana'oi. Mutumin da ya shekara sittin ko sama, idan bai samu abin da zai ci ba, zai yi wuya ya ɗau makami. Domin ba shi da ƙarfin jiki da zuciyar da zai yi haka. Amma matashi mai jini a jika, abu ne mai sauƙi a gun sa.


Zaharaddeen Ibrahim Kallah

zikallah@gmajl.com

Twitter/Instagram @zikallah


Kafuwar Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo


A watan Janairu, 1939 aka fara buga jaridar 'Gaskiya Ta Fi Kwabo'. An yi tunanin kafa ta ne don a yi martani ga farfagandar da Jamus da Hitler suke yaɗawa a yaƙin duniya na biyu da ake gwabzawa. 

An nemi Abubakar Imam ya zama editan jaridar, wanda a lokacin yana koyarwa a Katsina. An ƙara masa albashi daga fam shida da silai goma zuwa fam takwas, don a ƙarfafe shi ya karɓi aikin.

Jaridar ta maye tsohuwar jaridar da ake da ita a lokacin mai suna, 'Jaridar Nijeriya Ta Arewa' (Nothern Nigerian Newsletter), wacce ake buga ta a maɗaba'ar Gwamnatin Gargajiya ta Kano (Native Authority Kano). 



Mr L.C Giles da yake shugaban gudanarwa a Literature Bureau ya nemi shawarar Abubakar Imam ko za a sa wa jaridar suna 'Kwabo Kwabo' ko 'Kawo Kuɗi' ko kuma 'Daɗin Nazari'. Amma da Abubakar Imam ya iso Zariya, ya bada shawarar raɗa mata suna 'Gaskiya Ta Fi Kwabo' wanda shi ne sunan da aka amince da shi.

Jaridar ta fara da ƙafar dama, domin ba ya ga mayar da martani ga farfagandar Jamusawa, an shigo da labarai da rahotannin gida, wanda suka shafi wayar da kan talakawa akan ayyukan gwamnati da na masarautu. 

Zadeen Kano

Monday, 14 September 2020

Tasirin Marubuta Da Gudunmawarsu A Ƙani Na 21


Tun lokacin jahiliyya, marubuta na da mihimmanci a al'umma. Domin kowacce ƙabila na da marubutanta na musamman. A wannan lokaci, duk ƙabilar da ba ta da marubuta, yakan zama abin gori da koma baya a gare su. 

Da rubutu ne, musamman waƙa suke isar da saƙonni. Koda an taɓa ƙabilarsu, kafin a ce abu ya kai ga ɗaukar makami, marubuta ne za su fara mayar da martani.

An yi wani fitatcen mawaƙi kafin zuwa musulunci a ƙasar Larabawa da ake kira Zuhayr Bin Abi Sulma, wanda ya fito daga Banu Muzaina. Wata waƙa da ya rubuta akan haɗa kai da daina ɗaukar fansa akan yaƙe-yaƙen Larabawa ta yi shaharar da ta ɗaga mutunci da martabar ƙabilarsu. Wannan waƙa sai da aka rubuta ta da ruwa gwal aka rataye a ɗakin Ka'aba. Wanda a baya ƙabilarsu ba ta kai matsayin waɗanda suke cikin mawaƙan da ake rataye rubutunsu a Ka'aba. Saboda ɗaga darajar ƙabilarsu, sai da ya zamo duk wata bazawara a wannan ƙabila an aureta. 

Marubuta sun kasance mutane ne masu daraja a al'umma, saboda sune fitila dake haskawa al'umma yadda rayuwa ta sa gaba. Mutane ne masu hikima da fikira tare da hangen nesa. Akoyaushe suna ƙoƙarin nazartar al'umma, walau ta hanyar karace-karance ko ta nazari, kula, bibiya da tariyar baya.

A wannan zamani ma haka abin yake, domin samuwar marubuta ya taka rawa a tarihin cigaban duniya. Marubuta iri-iri sun bayar da gudunmawa, waɗanda suka ƙunshi marubutan wasan kwaikwayo, rubutun zube ko na waƙa. Kai har da marubuta a ɓangaren aikin jarida da marubutan da ba na rubutun ƙirƙira ba.

Irin waɗannan gudunmawa ta shafi ɓangarori da dama da suka shafi tattalin arziƙi, da siyasa, zamantakewa, addini da al'ada, tsaro, da ilimin sana'oi, ilimin kimiyya da fasaha da sauransu.

A wannan ƙarni na 21, abubuwa sun sauya a tarihin duniya. An shiga wani zamani da Turawa suka yi wa laƙabi da globalisation, wanda aka ɗauki duniya kamar wani ƙaramim ƙauye ne da kowanne ɓangare ya san me ɗan uwansa yake ciki, ko kuma abin da ya shafi mutum ɗaya ya shafi mutane da yawa. 

A yau, a wannan duniya da muke ciki, matsalar tsaro ta shafi kowanne ɓangare. Domin idan wata ƙasa ta shiga rikici da yaƙe-yaƙe, kafin wani lokaci sai ka ji ɓullar su a wata ƙasa. Misali, ƙasar Libya ta shiga halin yaƙi da taɓarɓarewar tsaro, wanda kafin wani lokaci, rikici da yaƙe-yaƙe sun yaɗu a wasu sassa na Afirika dake maƙwabtaka da su.

A yau matsalar sace-sace, fashi da makami, da satar mutane, fyaɗe da shaye-shaye ya zama matsalar kowa. Abubuwan da a tarihi wasu yankuna ba su san da su ba, yanzu sun addabe su. Ko a wannan lokaci da cutar Korona ta ɓulla a ƙasar Chana, ta gama game duniya, saboda cigaban da aka samu ta kowacce fuska da kasancewar duniya abu ɗaya.

A cikin wannan tafiya da ake ta sabuwar duniya a ƙarni na 21, samun bayanai da ilimi ya zama kamar ƙiftawar ido, duba ga cigaban da aka samu a kafofin sadarwa na yanar gizo da fasahar zamani a ɓangaren na'ura mai kwakwalwa. Wannan cigaban ya game kowanne ɓangaren rayuwar al'umma.

A wannan lokaci, wacce irin gudunmawa marubuta za su bayar wajen cigaban al'umma? To, gudunmawar da za su bayar ba ta da banbanci da wadda magabata suka bayar a baya. Amma a wannan zamani dole salo da tsarin isar da saƙon ya banbanta. Dole marubuta su tafi da zamani, idan suna son yin tasiri a wannan tafiya ta sabuwar duniya.

Da farko dai sai marubuta sun tafi da kafofin sadarwa na zamani da ake da su irin su Facebook, Twitter, Youtube, Instagram, linkedin, whatsapp da sauransu. A yau akwai ɗinbin manhajoji da ake hada-hada a cikinsu, wanda rubutu na kan gaba a wannan tafiya.

A cikin waɗanna kafofin sadarwa, akwai miliyoyin al'umma, wanda babu irin sharar da ba za ka samu ba. Don haka, wajibi ne marubuta su banbanta da ɗinbin mutanen dake cikin wannan kasuwa. To amma, ta ya ya za su banbanta kansu a cikin tarin mutanen dake cikin wannan tafiya?

A nan dole ne matsayinsu na masu ilimi da bincike, kuma fitilar al'umma ya yi tasiri a zuciyarsu. Wannan shi ne zai yi musu alƙibla, ya zamo duk wani abu da zai fito daga maɗallin kwamfutarsu ya zamo rubutu ne da ya sha banban da game gari. 

Dole a samu bincike, nazari, kula, bin diddigi da bibiya a cikin rubutunsu. Wannan shi zai zama gishiri ko magin rubutu, wanda zai gamsar da mai karatu.  

A nan ban yi amfani da kalmar gishiri da magi a yadda ake fassara kalmomin a rubutu ba. A'a, ina nufin dukkan abubuwa da zai gamsar da mai karatu, ya tsima shi tare da riƙe shi ko jan hankalinsa, da bashi ainahin hoton abin da marubuci ke son isarwa.

Idan kana rubutu akan rashawa da cin hanci, za ka yi nazari sosai tare da bin diddigi, yadda idan rubutun ya fito, ƙarya ne wanda aka yi akansa ya musanta. Wani marubuci Abdulaziz A. Abdulaziz, ya yi rubutu akan wata tsohuwar minista a Najeriya akan sahihancin takardun da suka sahale mata hidimar ƙasa. Wannan rubutu  da ya amsa sunansa, sai da ya yi sadadiyar wannan minista ta yi murabus. 

Haka ma wani marubucin ɗan ƙasar Ghana Anas Aremeyaw Anas da ya kware akan rubutun bincike da bin diddigi, ya bankwaɗo aikin rashawa da cin hanci a ɓangaren wasanni, wanda hakan ya yamutsa hazo sosai. Wannan bincike na shi ya sa wasu shugabanni da masu horarwa suka rasa kujerunsu. 

Irin wannan salo yakamata marubuta su yi amfani da su wajen bada gudunmawa ga al'umma. Ana da buƙatar marubuta su yi rubutu akan abin da ya shafi mulki da gudanarwa, siyasa, shari'ah, tsaro, ilimi, kasuwanci da sauransu. Akwai abubuwa na daɗi da rashinsa sosai a wannan ɓangarori. Yin rubutu zai nusar da jama'a tare da kawo sabon tunani na cigaban da aka samu a duniya.

Wannan rubutu zai iya kasancewa na ƙirƙira, ko ba ƙirƙirarre ba. Idan ka yi rubutun ƙirƙira, dole ya kasance ka gabarta da jigonka akan dukkanin tsanikan rubutu, sannan a ƙarshe ka fitar da mafita ta hanyar da tsari da dokoki suka amince  da su. 

A ƙarni na 20 an ga irin gudunmawar marubuta irin su James Hadley Chase (Rane Lodge Brabazon) da Sidney Sheldon da Abubakar Imam da Chinua Achebe da Wole Soyinka suka bayar akan rayuwar da ake ciki a wannan lokacin. Marubuta a ƙarni na 21, sai a ce muku ga fili ga mai Doki.


Daga

Zaharaddeen Ibrahim Kallah 

zikallah@gmail.com

Twitter/Instagram @zikallah


Cin Dawisun Hakimi


Wani Hakimin ƙauye ne ya kai wa abokinsa Hakimi da yake hakimci a cikin birni ziyara. Shi wannan Hakimin birni yana da arziƙi da wadata sosai. 

A lokacin da Hakimin ƙauye ya isa gidan abokinsa, an yi masa tarba ta arziki. Don an kawo masa wani nama, wanda da ya tauna sai ya ji kunnesa ya motsa, saboda daɗi. Amma kuma ya rasa wane irin nama ne. 

Nan ya dubi abokinsa ya ce. "Ranka ya daɗe, wannan wane irin nama ne? Shi ba na kaza ba, ba kuma na zabo ba."

Hakimin birni ya yi murmushi ya ce. "Naman ya yi maka daɗi kenan, naman Ɗawisu ne."

Ya gyaɗa kai, "Gaskiya naman ya yi, amma a ina kake samun naman Ɗawisu?"

Hakimin ya ɗan kyalkyale da dariya sannan ya ce. "Akwai wani mutum da yake kawo mana, idan kana so sai a ce ya kawo maka."

"A, ina so. A ce ya kai min guda huɗu gida." Hakimin ƙauye ya nemi a kai masa.

Bayan 'yan kwanaki da zuwansai birni, sai rannan aka ce ga mai Ɗawisu ya zo daga birni, abokinsa ya aiko mai sayarwar kamar yadda suka yi alƙawari. 

Lokacin da aka shigo da shi, ko tambaya bai yi ba sai ya ce a je a yanke ɗawisan har guda huɗu gaba ɗaya. Zuwa can Hakimi ya tashi don ya ga yadda ake yankan. Ya tarar an yanka guda ɗaya, an ɗauko na biyu kenan an danne za a yanka, sai Hakimi ya tambayi mai sayarwa. "Nawa ne kuɗin kowanne?"

Mai sayarwa ya ɗago, hannunsa na riƙe da wuka ya ce. "Allah ya baka nasara, naira dubu arbain ne kowanne."

Ba tsammani sai ji aka yi Hakimi cikin ƙaraji ya ce. "Ɗaga shi, ɗaga shi dan ubanka."

Ashe shi Hakimi ya ɗauka Ɗawisun ba wata tsadar kirki ba ce da shi.

Mai sayar da ɗawisu ya ɗaga Ɗawisu yana cike da mamaki.

Cikin mazurai, Hakimin ya dubi mai Ɗawisu ya ce. "Ka kwashe kayanka, shi ma wanda ka yanka a kaiwa Ranka ya daɗen ya biya, tun da shi ya saba ci."

Lokacin da Hakimin birni ya ji labari, sai ya yi dariya har da kwalla. Tun daga wannan rana idan suka haɗu da abokinsa Hakimin ƙauye, abin da zai fara gaya masa shi ne. "Ɗaga shi dan ubanka."


(c) Zaharaddeen Ibrahim Kallah

zikallah@gmail.com

Twitter: @zikallah


Saturday, 5 September 2020

Duniya Makaranta

Allah ya bamu ikon cin jarabawarsa. Ita rayuwa, gwagwarmaya ce gaba ɗayanta. Lokacin da Abubakar Imam da takwarorinsa suka tafi Birtaniya a jirgin ruwa, sun samu aƙalla wata ɗaya akan ruwa.

Kullum sai dai su ci su sha, sannan su kwanta. Anan ne Abubakar Imam ya fahimci ashe gwagwarmayar rayuwa tana da daɗi. Ba su da matsalar abinci ko.makwanci, amma kuma duk sun takura. 

Duk wani hali da za mu shiga yana cikin gwagwarmayar rayuwa. Wani ya zage ka, ko a taka, ko a ja kaima ka ja, duk ba sabon al'amari ba ne. 

Mun yi imani za mu cigaba da gwagwarmaya, domin ita ce tushen rayuwa. Haƙika Allah maɗaukakin sarki yana tare da mu, matuƙar ba mu juya masa baya ba.

Zaharaddeen I. Kallah
zikallah@gmail.com
@zikallah