Tuesday, 7 January 2020

Murucin Kan Dutse...


(Tsakure daga wani sashe na sabon littafina)

Babi Na Bakwai

Babu kakkautawa ruwan bamabamai ake daga sojojin ruwa na Najeriya, wanda cikin kwana uku babu sararawa. Wai da an ji shiru, an dauka bako ya tafi ko kuma makamansa sun kare, sai a ka ji sabon hari. Ashe wannan wani salon yaki ne na sojojin Najeriya, wannan salon nasu ya sha banban da abin da suke zaton abokan hamayyarsu zasu zata.

Da farko dai sun san cewa manyan sojojin Biyafara suna gaba da mafi yawan sojojinsu, bayan wannan sun halarci makarantu na horon sojoji a Birtaniya da Amurka da Indiya zuwa Ghana tare. Don haka suna kyautata zato duk wani motsi da suka yi, watakila wannan yayyen nasu dake cikin Biyafara su fahimta. Hakan yasa dole su yi takatsantsan.

Ga yadda abubuwa suke tafiya kamar an yi yamma da kare ne, domin yayyen nasu sun gaza fahimtarsu a wannan lokaci. Wannan luguden wuta da ake ashe ana so a bawa rundunar Isaac dama ne ta isa James Town. Shi ma Akininde dake tsaunin Bonny zai yunkuro da tashi rundunar ya kawo wa Isaac dauki. Haduwarsu zai taimaka a kama James Town cikin sauki. Hakan kuwa aka yi, cikin kankanin lokaci rundunar ta 3MCDO ta danna da qarfin tsiya ta mamaye wannan gari.

Wai duk wannan dawurwura da ake ashe dai ba ita ba ce ainahin abin da ake son cimmawa, duk dai salon yaudara ne na yaki. Wannan dabara kuwa ta kara tabbatarwa sojojin Biyafara cewa lalle sojojin kasar Najeriya na kokarin cin Fatakwal ne daga Tsaunin Bonny, domin dai ga su sun danno har sun shigo James Town.

Hakan yasa suka sakankance suka firfito daga maboyarsu, musammam irin gwalalo da a kan gina saboda buya ga harsasai da ruwan bama-bamai. Cikin wannan dauki babu dadin da ake ta yi, wannan bataliya ta Najeriya ta dauke hankalinsu ga sharrin da ake kulla musu. An ce dama yaki dan zanba ne, wannan duk wata dabara ce da zata bawa ainahin sojojin Najeriyar dake tafe cikin surkikiyar daji su 35, 000  su samu damar isowa garin Oron, wanda daga nan ne zasu gangara zuwa kogin Opobo.

Amma fa dole su zamo a shirye, kuma su kula. Domin yayin da suka ba wa kogin Opobo baya, sojojin na Biyafara za su so su tarfa su, yadda idan wuta ta yi wuta su yi kokarin dannasu har sai sun dangane da ruwan dake bayansu. Watakila za su so yin abin da suka yi wa runduna ta biyu ta Najeriya, wanda suka yi kokarin sulalowa ta cikin kogin Naija a kokarinsu na shiga Asaba. Runduna ta biyu ta samu nasarar haurowa da wasu daga cikin makamansu, amma yayin da sojojin na ‘yan tawaye suka tarfa su sun kasa kare kansu, wanda da yawansu sun mutu ko dai da harsashi ko kuma sun nutse a ruwa.

Sojojin na Najeriya na samun karfin gwiwa, musamman yadda abubuwa ke tafiya daidai kamar yadda aka tsara, illa ‘yan kananan matsaloli da sukan yi kokarin magance su. Duk inda suka bullo sukan fito ne ba tare da abokan gaba sun sani ba, don haka cikin ruwan sanyi suke kama su.

Ai kuwa a cikin wannan yanayi na rashin takamaimai me yake faruwa tawagar su Sanusi ta karaso cikin duhun dare ga kuma ruwan sama da ake tafkawa. To amma kuma abin ka da baki da basu san dawan garin ba, maimakon su sauka a Oron kamar yadda aka tsara, sai sojojin suka sauka a Tsaunin Parrot, wanda yake hannun riga da Oron xin. A wannan lokaci sojojin ruwa na Najeriya sun shiga kwana na uku suna sakin wuta, wanda dole a sanar da su cewa sojojin sun iso, amma sun sauka a Tsaunin Parrot kuma ba kamar yadda aka tsara ba. Dole a sanar da su sojojin na yunkurin haurawa su karasa Oron, wanda hakan na nufin sai sojojin ruwan sun tsahirta da sakin wuta su dan sha ruwa. Hakan sai ya bawa su Sanusi damar haurawa suka shiga ainahin inda ake son su sauka.

A lokacin da sojan ruwan suka tsahirta, abin fa bai tsaya haka ba sai sojojin sama suka dauki na su ta wani salo da kwata-kwata hankalin abokan gaban zai karkata daga Oron. Ka san ginshikin sojojin dake tafe za su haura ne ta cikin ruwa, inda za a yi amfani da kwale-kwale. Don haka sai an yi da gaske, kar abokan gaba su far musu a wannan lokaci. Hakan yasa ba a yi sakaci ba, aka ba wa sojojin sama ta su damar.

Sojojin saman sun shiga nasu barin wuta ta bangaren arewa zuwa Uyo da kuma yamma da kogin Opobo. Hakan zai sa runduna guda biyu dake fuskantar abokan gaba ta dauke hankalinsu, su zaci sune ainahin babbar rundunar Najeriya, inda ake kyautata zato za su rike wuta suna mai fuskantar Oron, da kuma gabas da ita ta bangaren wani karamin gari da ake kira Okopedi, su ma su rike wuta.

Innalillahi Wa’inailahir Rajiun, wanda bai san yaki ba shi yake nemansa. Babu abin da kake ji sai qarar manyan-manyan bindigu. Wasu bindigun kana jin kararsu ka san bindugun nan ne da ake kira 2 Inch da kuma 81 mm mortars. Su kuma abokan gaba kasancewar sun san cewa zai yi wuya a shammace su ta baya, saboda yanayin gurin da ba zai ketu ba suka sakankance har ba su girke manyan bindigu kirar 2 inch da 81 mm mortars. 

Ana cikin gwabza wannan yaki, kamar daga sama sai sojojin ‘yan tawaye suka ji wani sabon hari da karar bindigu ta inda ba sa zato, su waiwaya haka sai suka ga wata runduna ce mai tarin yawa ta vallo ta bayansu tana tafe kamar bakin gajimare. Lahaula Walaquwata Illabillah, ta ina wadanna sojojin masu tarin yawa suka faso kamar aljannu. Su dai a iya saninsu babu wata hanya takamaimiya saboda ruwa da yanayi na chabi da bishiyoyi na kurmi. Wani gurin ma idan ruwa ya yo ambaliya, ya kan hadiye mutum har wuya, ko kuma irin wannan tabon mai kama da ruwan gam da kan shanye mutum a hankali yana ji yana gani.

Zaharaddeen Ibrahim Kallah

Wednesday, 19 April 2017

GASKIYA DACI GARE TA



Ina ga lokacin da zamu gaya wa kanmu gaskiya ya yi. Halin da al’umma kasar Hausa suka samu kansu ya ta’azzara. Duk wanda zai ce Arewa ba a cikin talauci da fatara da jahilci, ya yaudari kansa, kuma bai yi wa kasar Hausa adalci ba. A yadda magabata suka fada idan mutum yana da wata cuta kuma ya ki yarda yana da ita to ya shiga ukuba, kuma samun saukinsa abu ne mai wuya a gurinsa. Amma da zarar ya yarda yana da ciwon, to ana tsammanin sauki ya samu. Ko ba komai ya san me yake damunsa kuma zai tashi ya nemi magani.  

Babu dadi ga yadda wasu tsirarrun mutane ke kokarin gurbata tunani jama’a, watakila don neman suna ko wata bukata tasu ta daban da su suka santa. Amma ina mai tabbatarwa irin wadannan mutane cewa idan guguwar canji ta taso bubu wani abu da zai iya tare ta. Allah ubangiji shi ne zamani kuma shi yake juya zamani yadda ya so.  

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya yi jawabai a kan fahimtarsa bisa halin da muke ciki da yadda za a samu waraka. Kuma bana jin ya ce lalle sai an bi abin da ya fahimta.  Bukatarsa ita ce a zauna a kalli abin da ya kawo da idon basira. Abin da ban ji dadi ba  shi ne  yadda aka mayar da abin cin mutunci da tozartarwa da izgilanci. Mai makon abin ya zamo bisa doron ilimi da tattunawa ta fahimta tsakanin shugabanni da malamai da sauran al’umma.  

Ban ga dalilin da jama’a zasu yi tariyar baya ba su dauko wata mahawara tsakanin mai martaba Sarki da marigayi Sheikh Jafar Muhammad Adam, rahimullah. Wannan ya nuna jahilci da kokarin tada zaune tsaye. Muhawara ce aka yi lokaci mai tsayi da ya shude, kuma wanda suka yi ta suka fahimci junansu abin ya wuce kafin rasuwar Malam. Shin suna ganin sun yi wa Malam adalci da suka bijiro da wannan al’amari wanda ba shi da alaka da abin ake ciki a yanzu?

A satin da ya gabata mai martaba Sarki ya tura ‘yarsa Shahida ta wakilce shi a kan taron tunawa da ‘yan matan Chibok da aka sace aka yi garkuwa da su. Ga masu hangen nesa sun ga wannan wakilci a matsayin abin da ya dace, kasancewar taro ne da zai waiwayi batun yaran wadanda suke kusan sa’oi ga Shahida. Ni ina ganin hikimar wannan zai tunawa jama’a cewa iyayen wannan yara sun tura ‘ya’yansu neman ilimi, kuma burinsu su samu ilimi kamar yadda Shahida ta samu har ta iya yin wannan wakilci. Ashe mutane jira suke su ga ta inda za su yi cin mutuncinsu, sai wanda suke zato bai halarta ba. Wannan yasa suka juya ta wani bangaren cewa suturar da yarinyar ta sa ba su dace ba. Ashe dama yanzu ba irin kayan da ‘ya’yan mu da kannen mu da yayyen mu mata suke sa wa ba?  

Mai martaba ba zai zamo ma’asumi ba, a matsayinsa na adam yana da tashi gazawar. Amma a wannan hali muna bukatar gudunmawarsa don fitar da A’i daga rogo. Ai tun tuni dama mutanen Kano mutane da basa karbar sauyi cikin sauki (conservative), ba jayayya a wannan. Amma idan har suka karba suna rinjayar sauran bangarori na kasar Hausa. Ina ji a jikina wannan guguwa da ta taso zata yi tasiri wajen sauya tunanin jama’a da tabbar al’umma ingantatciya. 

A ganin wasu jama’a shi mai martaba Sarki bai kamata ya shiga wannan al’amari ba. To, wai idan irinsu ba su shige mana gaba ba su waye zasu tsamo arewa daga halin da take ciki. Wadanda ake sa ran su zasu yi wa Arewa gata sune wadanda suka kara jefa ta a rami. Tun da magabata irin su Ahmadu Bello (Sardaunan Sakkwato) suka gabata, shugabannin da suka gajesu ba su yi wa Arewa abin da ya kamata ba. Da sun rike matsayinsu na magadan su Sardauna da Aminu Kano da ba mu shiga wannan hali da muke ciki ba. Arewa ta rasa jagoranci na gaskiya. A yau su wanene shugabannin Arewa? Ban ga wani shugaba ba da zai fito ya ce a yi gabas, gaba daya mutane su bi kamar yadda muke gani a kabilu kamar na yarabawa. Shin irin wadannan mutanen da basu tsinanawa Arewa komai ba ake sa ran za su goyi bayan sabon tunani? 

Lokaci ya yi da za a daina kallon maganar gaskiya a matsayin siyasa. Komai a ce siyasa kamar mu muka fi kowa siyasa, amma mun rike kaho wasu tsirari na tatsa. Duk siyasar ta mu yau kusan shekara hamsin da bakwai da karbar mulkin kai amma har yanzu bamu iya samar da ilimi da lafiya da abin yi ga dinbin al’ummar mu ba. Su kansu alkaluma da ake fitarwa da suka nuna tsananin talauci da fatara gami da rashawa da cin hanci da suka yi mana katutu, wasu na ganin siyasa ne ko kuma tonon asiri. Ya ilahi, dama haka ake gina kishin kasa a kasashen da suka cigaba har muke sha’awarsu?

Muhammad Sanusi II, shi ne Amir na Kano wanda Allah ya dorawa shugabancin mutanen Kano. Babu wanda yake tantama cewa a matsayinsa na Sarkin Kano Allah zai tambaye shi yadda ya gudanar da mulkin talakawansa duk cewa kundin mulkin kasa ya karbe musu cikakken iko. Wai ance Sarki ya rage magana, amma kuma jama’a kullum na turereniya kai kukansu gare shi na irin cin zarafi da tauye hakkin dan adam da yake faruwa. Na tambata duk wanda ke cike da tausayi da imani idan ya ji irin kwadon da ake damawa a wannan sashi na kasar nan sai zuciyarsa ta koka. 

Kamar yadda na ce mai martaba Sarki ba ma’asumi ba ne, mutum ne kamar kowa; amma kuma Allah ya yi masa baiwa ta ilimi. Wannan ba yana nufin ina kare shi ba ne ido a makance. A’a, akwai abubuwa da yadda ya fahimce su mun yi mun yi hannun riga da shi. Misali, maganar samar da tashar jirgi ta zamani mai amfani da lantarki na kalle ta a matsayin cigaba ga jihar Kano. Bana ganin bashi ne da za a karba a kashe wajen biyar albashi ko wata sharholiya, na kalli yunkurin a matsayin abin da zai samar da aikin yi sannan ya biya kansa bashin da aka ci masa. Amma ba na shakkar mai martaba masanin tattalin arziki ne wanda ya nuna basirarsa lokacin da duniya ta shiga masassarar tattalin arziki a shekarun baya; wanda Najeriya ba ta ji radadin abin ba kamar sauran kasashe, sannan yunkurinsa ya tallafi bankunan mu daga durkushewa. Wannan ba zai sa na kasa yi masa uziri don jin mai ya taka da nashi ra’ayin. 

Amma ina mamaki a wannan zamani har wasu na tunanin a hana mai martaba Sarki magana. Haba! A wannan karni na ashirin da daya, lalle muna da sauran aiki. Gaskiya wata guguwa ce ta taso wanda Allah ne yasan inda za ta tsaya. Masu rike da madafan iko akoyaushe ba sa son kan talakawa ya waye don gudun bore. Haba, Kano ce fa wanda Malam Aminu Kano ya rayu a cikinta. Yau Malam Aminu Kano ya cika shekaru talatin da hudu da rasuwa, amma abin kunya ne a ce irin wannan al’amari na faruwa. Malam ya rasu ya bar riguna guda uku, mutumin da bai yarda an sa masa janareto ba don kar ya damu makota da kara kuma bai basu wuta ba. Maganar Malam akoyaushe ita ce talakawa da yadda za su samu waraka. Yau ina akidar NEPU wanda tasa aka azabtar da kashe da yawa daga magoya bayan tafiyar. Shin zamu koma lokaci ne da mata irin su Gambo Sawaba suka sha azaba da duka wanda har ya yi sanadin fashewar mahaifarta? 

Mutanen Arewa na bukatar mutanen da zasu fada musu gaskiya ko mun dacinta. Arewa na bukatar mutanen da zasu karfafi ilimi da bawa mata hakkinsu da musulunci ya basu. Arewa na bukatar mutane da zasu taimaka wajen yakar zaman kashe wando da shaye-shaye da miyagun ayyuka. Ba yadda za a fita daga wannan kangi idan shugabanni ba su yi yunkurin samar da ilimi ga ‘ya’yan Arewa ba. Irin wannan yunkuri ne yasa mutane irinsu Awolowo suka samu soyayyar mutanensu saboda ganin amfanin abin da suka shuka.

A lackar da aka gabatar don tunawa da Malam Aminu Kano a wannan shekara na ji dadin abin da mataimakin gwamnan Kano Prof. Hafizu Abubakar ya ce yayin jawabinsa. A cewarsa idan zamu gayawa kan mu gaskiya mun shiga wannan hali ne ba wai kawai don watsar da akidar Malam ba kawai, har da watsi da dokikin Allah. Wannan magana ce da ba kowane shugaba ba ne zai yarda da ita. Masu iya magana na cewa ita karya fure ta ke bata ‘ya’ya, don haka duk wani kyalkyal na fure da kamshinsa kar ya rude mu.

Daga
Zaharaddeen Ibrahim Kallah

Zaharaddeen Ibrahim Kallah marubuci ne cikin harshen Hausa da Turanci. A halin yanzu shi ne shugaban Kungiyar Marubuta ta Najeriya, reshen jihar Kano. 
                                                                                                                                    

Friday, 4 September 2015

TARON BIKIN MARUBUTAN HAUSA NA DUNIYA



Wasu daga cikin mahalarta taron

Marubutan Hausa sun xauki xamara don gudanar da bikin marubutan Hausa na duniya. A ranar Asabar ne 6 ga Yuni, 2015 aka gudanar da zama na farko na shire-shiryen gabatar da taron. Tunanin shirya wannan biki ya taso ne bayan tattaunawa tsakanin marubuta ta kafofin intanet, wanda ya biyo kafa kwamitin da zai jagoranci taron karqashin Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON. Ana sa ran taron zai haxo marubuta daga faxin duniya musamman qasashen da suke na Hausawa da makwabtansu. 

A yayin qaddamar da kwamitin, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, ya yi bayanin amfanin ranar ga marubutan Hausa. A cewarsa taron zai haxa tsofaffi da sababbin marubuta don tattaunawa da musayar ra’ayin a kan cigaban adabin Hausa. A yayin taron ana sa ran za a yi bajakolin littattafai sannan a gabatar qasidu da taron sanin makamar aiki da karance-karance qirqirarrun labarai da waqoqi.

Marubuta daga Kano da Katsina da Kaduna da Jigawa na daga cikin waxanda suka samu damar halarta taron qaddamar da kwamitin da tattaunawa. Hakazalika, qungiyoyin marubuta na daga cikin waxanda za su taka rawa a wajen ganin nasara shirin. Ana sa ran za a yi taron a watan Oktoba na wannan shekara a garin Kano. An zavi Kano ta kasance garin da za a gudanar da taron saboda matsayin jihar wajen raya adabin Hausa, musamman ta vangaren haziqan marubuta da jihar ke da su da kuma rubuce-rubuce da kasuwancin littatafai. 

Akwai fatan cewa bayan an gudanar da taron za a samu cigaba a harkar rubutun Hausa ta yadda za a shigo da sababbin tsare-tsare da zasu inganta harkar. Musamman yadda marubuta ke kuka na lalacewar harka a wannan lokaci. A halin yanzu marubutan Hausa ba kowa ba ne yake iya sayar da koda kofi dubu biyu na litatttafansu duk da xinbin al’aummar da qasar Hausa take da ita. A Kano a shekarun baya, akwai marubutan da sun sayar da kofi sama da dubu xari shida na littafinsu a lokacin da ake ganin Kanon ma ba ta tunbatsa ba. 

An shiga wani qarni da matasa ba sa son karance-karance, duk da cewa wasu na ganin matsalar ba ta rashin karance-karance ba ce. Amma maganar gaskiya matasa a yanzu sun fi mayar da hankalinsu wajen hawa kafofin yanar gizo ko intanet da kallon fina-fina, wanda hakan ya kawo naqasu ga harkar ilimi da adabin ma. Sanin kowa ne babu alummar da zata cigaba matuqar matasan ta basa karatu.
Ina ganin lokaci ya yi da gwabnatin jihar Kano tare da hukomomi na ilimi za su haxa kai don jagorantar farfaxo da harkar rubutu, ta yadda za a qarfafi marubutan mu na gida da su yi rubuce-rubuce masu nagarta, da yin tsare-tsare da zasu inganta harkar. Misali, sanya gasar rubuce-rubuce, xaukar nauyin yin wasu rubuce-rubuce masu fa’ida da tarurrukan qarawa juna sani. 

A wannan duniya da muke ciki ta bani gishiri in ba ka manda, ba abin da ake buqata illa gudunmawar da kowace al’umma za ta iya bayarwa na cikar da duniya gaba. Allah ya taimaki rubutu na marubuta gaba xaya.

Daga,

Zaharaddeen Ibrahim Kallah

Wednesday, 2 September 2015

Ganawar Marubuci Farfesa Yusuf Adamu da Daliban Kwalejin Sa'adatu Rimi

A Ranar Lahadi (12-7-2015), daliban Sashen Hausa na Kwalejin Sa’adatu Rimi suka karbi bakuncin Farfesa Yusuf M. Adamu, tsohon shugaban kungiyar Marubuta ta kasa (ANA) reshe Jihar Kano. Taron ya gudana ne bayan daliban da ke (part time) na kwalejin sun yi nazari a kan littattafin Farfesan mai suna Idan So Cuta Ne, wanda aka rubuta tun a shekara ta 1989.
Farfesa Yusuf Adamu na rubutu cikin harshen Hausa da Turanci, ya fitar da littattafai masu yawa wadanda suka hada da Ummul-Khairi da Maza Gumbar Dutse da Gumakan Zamani. A littattafansa na Turanci akwai Butterfly and Other Poems da Animal in the Neighbourhood da Landscapes of Poetry da They Can Speak English da A flat World da sauransu.
Taron ya kayatar matuka, domin ba ya ga marubucin, wasu daga cikin marubuta sun halarta wadanda suka hada da Zaharaddeen I. Kallah da Dokta Faruk Sarkin Fada da Kabiru Yusuf Anka. Sannan akwai da yawa daga cikin malaman Sashin Hausa na kwalejin, karkashin jagorancin Shugabar Sashin, Dokta Bilkisu Yusuf, wadda Dokta Mahe Isa Ahmed ya wakilta.
A yayin jawabin maraba, Dokta Mukhtar Sadauki ya sanar da cewa wannan rana ita ce rana ta karshe da daliban suka gama daukar darasi a kan wannan fanni, hakan yasa suka gayyaci marubucin littafin da aka nazarta wato Farfesa Yusuf M. Adamu don ya amsa tambayoyi daga daliban.
Farfesa Yusuf Adamu ba boyayye ba ne a bangaren rubuce-rubuce, domin yana daga cikin jiga-jigan da suka haifar da Adabin Hausa na zamani. Tun bayan da kamfanin wallafa littattafai na NNPC ya dakatar da buga littattafan Hausa, marubuta na wannan zamani suka shiga mawuyacin hali na rashin samun kafar da za su isar da sakonninsu. A cikin wannan hali ne marubuta irin su Talatu Wada da Farfesa Yusuf Adamu da Ado Ahmad Gidan Dabino da Sunusi Shehu Daneji da dan’Azimi Baba da su Balaraba Ramat da su Adamu Muhammad da Alkhamees D. Bature da Bala Anas Babinlata da sauransu suka jagoranci nakudar Adabin Hausa na zamani. Hakika zan iya cewa gudunmawarsu ta taka rawa wajen dawwamar da Adabin Hausa har ya zama a raye zuwa wannan lokaci. A yau idan ana maganar marubutan da suke rubutu cikin harshen uwa, yana cikin wadanda suka yi fice. Wannan abin alfahari ne ga duk mai kishin yare da al’ada ta Hausa.
Farfesa Yusuf, yayin gabatar da tarihinsa da tarihin fara rubuce-rubucensa, ya gabatar da yadda ya fara sha’awar sauraron labarai da tatsuniyoyi, wadanda sun taimaka wajen zamansa marubuci. A cewarsa, mahaifinsu kan dauke su lokacin hutu zuwa wasu garuruwa, inda bayan sun dawo yakan ummarce su da su rubuta abin da suka gani. Da haka ya fara rubutu, inda ya rubuta littafinsa na farko Maza Gumbar Dutse, sai kuma Idan So Cuta Ne… da ya rubuta shi a cikin mako guda. A cewarsa, har yakan zana yadda yake son wani abu daga cikin bayaninsa ya kasance ya yi rubutu.
Hakika wannan dan gajeran tarihi zai haska wa wadanda suke da sha’awar zama marubuta da su yi koyi da shi, su fahimci suna da baiwar rubutu. Na san da yawa daga cikin mutane suna da wannan baiwa amma ba su sani ba. Misali, akwai mutane da idan suna ba ka labari sai ka rantse suna nan aka yi abu, ko kuma ka ga wadanda ke da sha’awar sauraron tatsuniyoyi da labarai, babu shakka hakan na nuna cewa za su iya zama kwararrun marubuta.
Kamar yadda na ce a baya, taron ganawa da daliban ya yi armashi kwarai, domin ya ba su dama sun yi tambayoyi ga Farfesa sannan sun gana da wasu daga cikin marubutan Hausa. Hakan ya sa an yi musayar ra’ayi da fito da wasu muhimman bayanai a kan adabi. Daga cikin abubuwan da aka duba sun hada da alakar marubuci da labarin da ya rubuta. Wasu daga cikin mahalarta taron sun yi duba ga wannan bangare. Misali, marubucin Idan So Cuta Ne… dan boko ne wanda ya kai matsayin Farfesa, hakan ya yi tasiri a cikin littafinsa na amfani da ’yan boko a cikin taurarin labarinsa. Kusan kowa yana yin boko, illa wasu kalilan da ba ’yan boko ba wadanda su ma sun taka rawa wajen fito da jigon labarin.
An kawo misalai na Abdulmalik da Salisu da Zairo a wasu daga cikin ’yan book, sai kuma Hajiya Bilkisu a matsayin wadda ba ta yi boko ba, kuma hakan ya kawo matsala ga Abdulmalik da Farida a kan soyayyarsu.
Daga cikin abubuwan da daliban suka tambaya, har da abin da ya ja hankalin marubucin ya yi wannan littafin. Yayin ba da amsa, marubucin ya ce ya jima yana jin ana maganar duk wata soyayya da aka jima ana yi a karshe zai yi wuya a yi aure. Kasancewar yana da wacce yake so kuma sun jima tare sai ya fara tunanin abin da zai faru idan haka ta faru, wannan ne ya sa ya fara tunanin yadda zai ba kansa hakuri. Wannan ne ya sa ya rubuta littafin Idan So Cuta Ne…
daliban sun yaba wa marubucin a kan cewa an rubuta littafin tun 1989 amma sai a dauka a wannan lokaci aka rubuta shi. An kuma yaba masa yadda littafin ya kasance tsaftatacce da al’umma za su amfana da shi.
Sauran baki su ma sun tofa albarkacin bakinsu a kan taron. A nasa bangaren, Zaharaddeen Kallah ya nuna farin cikin kasancewa a wurin taron, musamman saboda sha’awa da daliban suka nuna na nazarin Adabin Hausa. Ya kuma ba su shawara da su yi alfahari da harshen Hausa wanda a halin yanzu ya dauki hanyar shahara sosai a fadin duniya. Ya nemi daliban su kasance masu dabi’ar karance-karance da nazarin littattafai, wanda hakan zai taimaka musu matuka, musamman ga wadanda ke da sha’awar zama marubuta.
Dokta Faruk Sarkin Fada kuma ya yaba wa Sashen Hausa na kwalejin saboda wannan abu da suka shirya wanda zai taimaka wa daliban a cikin karatunsu. Ya yi kokarin fahimtar da daliban tasirin rubutu, musamman da aka samu wata daga cikin daliban marubuciya ce. A cewarsa yana da kyau mutum ya yi rubutu ba kawai don abin da zai samu ba, sai don manufarsa a rubutu wanda ilmantarwa da gyara al’umma ke ciki. Ya ce da yawa daga cikin marubuta sai sun bar duniya sannan rubutunsu ke shahara. Ya ba da misali da Muhammad Ikbal daga tsohuwar kasar Indiya da Pakistan wanda rubutunsa ya yi tasiri wajen kawo juyin juya hali a kasar Iran, bayan tsawon lokaci da rasuwarsa. Duk da cewa Ikbal bai taba zuwa Iran ba, rubutunsa da aka fassara ya yi tasiri sosai a can. Wannan ya sa a yanzu har maulidinsa suke gudanarwa saboda jin dadin abin da rubutunsa ya yi. Daga karshe sai Dokta Faruk ya ba da gudunmowar littattafansa guda uku da ya buga da Hausa ga Sashen Hausa na kwalejin.
Taron ya zo karshe da jawabin godiya daga bakin Dokta Mahe Isa Ahmed, wanda ya gode wa Farfesa Yusuf Adamu saboda lokacinsa da ya ba da na amsa gayyatarsu. Ya kuma gode wa sauran marubuta da suka halarci taron, a inda ya nuna aniyar sashen na kulla alaka da kungiyar Marubuta ta Najeriya (ANA) reshen Jihar Kano don ciyar da adabi gaba.
Hakika wannan alaka da kwalejin marubuta za su yi farin ciki da ita, musamman don za ta kasance hanya da za a taimaki juna. A bangaren dalibai zai kasance hanyar nazari da horar da su a harkar nazari tare da ganawa da marubuta. A bangaren marubuta da suke bukatar manazarta don rubutunsu ya ci gaba da rayuwa, su ma abin alfahari ne. Tabbas wannan yunkuri abin maraba ne musamman a wannan lokaci da ake neman yin wancakali da koyar da harshen Hausa a makaratun sakandire na kasar nan, wanda haka kan iya kawo barazana ga harshen gaba daya.
Zaharaddeen Ibrahim Kallah, tsohon sakataren kungiyar Marubutan ta Najeriya ne reshen jihar Kano, sannan ma’aikaci a Jami’ar Bayero, Kano. dinik2003@yahoo.co.uk

Friday, 16 January 2015

YADDA ZAHARADDEEN YA ZAMA SADAUKI MAI DUNIYA II

Ci gaba daga makon jiya
Yadda Zaharaddeen ya zama Sadauki Mai Duniya.

Matan nan su kai nasarar mamaye gidajen sarakan Kwairanga in da a karshe su ka kare musu kallon sirri a ranar wani biki na al'ada da Kwairanga ke gudanarwa duk shekara a ka turo maza mayaka daga Damanga, ' yanmata sukashayar da sarakai giyasu bayan sun sha sun bugu su ka hadu su ka cinyesu da yaki da rana tsaka, su ka karkashe mutane su ka nufi fada wajen Sarki, in da ya nuna jarumtarsa a shafi na 9 ' Maharan Damanga su ka yi ca kan Sarki Haruna, shi kuwa gogan naka ko in kula sai faman kirari ya ke yana cewa "Sai ni dan mutan Kwairanga kadangaren bakin tulu, a kar ka a kar tulu a bar ka ka bata ruwa, ruwan dare dama duniya na kwairanga sai dubu ta taru, ai kuwa nan da nan suka taru a kansa su ka kame Sarki Haruna Kabir su ka tafi da shi garinsu su ka daure, cikin matansa kuwa akwai wata da a ke kira Hassana wacce ta haye doki ta kubuta ta gudu tare da goyon danta Usman, 'yar Wani sarki sadauki jarumin gaske ne a wata kasa da a ke kira Yammaniya. Bayan ta sanar da mahaifinta yadda a ka tarwatsa kasar maigidanta Sarki Haruna, sai ya jajanta lamarin kuma ya dauki aniyar horar da Usmanu don ya daukarwa mahaifinsa fansar abinda a ka yi masa.
Sarki Haruna kuwa ya na daure a can wani kurkukun karkashin kasa a kasar Damanga in da ya shafe shekaru cikin wahala da azabtarwa iri-iri, yayin da kuma Zubaida daya daga cikin matan da a ka tura Kwairanga su ka yaudarar da sarakai ta kamu da ciwon son sa ta dinga zuwa har cikin firsuna ta na taimakonsa tare da shan alwashin sai ta fitar da shi daga halin kuncin da ya ke ciki.
Usman na da shekaru bakwai a ka fara shigar da shi daji a na gogar da shi ilimin yaki tun daga kan fada da mutane har zuwa dabbobi tare da koya masa dabarun fada da takobi da mashi da iya harbi da kwari da baka da sauransu.
Ya na da shekaru goma sha biyu ya kware sosai ya zama sadauki a fagen yaki duk kasar yammawa an sallama masa har su na yi masa kirari a shafi na 12 su na cewa " Usman Mai duniya na Kaura yalli, gwaggon biri makashin maza".
A lokacin ne a ka sanar da Usman labarin mahaifinsa da irin wulakancin da Damangawa su ka yiwa masarautarsa.
Ai kuwa Usman Mai duniya ya shirya tare da abokinsa Sabi'u wanda su ka taso tare dan Kaura yalli wato kawun Usmankenan, su ka nausa daji.
Shi kuwa Sarki Haruna Kabir Zubaida ta kubutar da shi daga gidan kurkukun sun shiga duniya, in da suka yi aure daga bisani wahalar da ya sha a kurkuku ta kwantar da shi ciwo.
Jarumta
Usman kuwa tun shigarsu daji ya ke nuna jarumtarsa in da ya kashe Gada suka cinye a shafi na 23, sannan ya gwabza yaki da wasu 'yan rawar wuta a shafi na 26, ya yi gumurzu da Sarkin fawa a shafi na 27. Sun buga gumurzu da mayakan garin Dawaki a shafi na 32 in da su ka biyo bayansu, maimakon Usman ya gudu sai su ka tsaya suna cafe mashi da kibbau, in da ya ke yi wa kansa kirari, "Kai arna ba ku sanni ba ne? Ni ne Usman Mai duniya, gwaggon biri makashin maza ni ne hadari malfar duniya". Nan ya afka musu ya karkashe su.
Haduwarsu da aljani wanda ya ba Usman takobin kakansa da suka ara su kai yaki a shafi na 33-34.
Usman ya shiga gasa a kasar Zainawa in da ya yi dauki ba dadi da mayaka abokan takara a shafi na 36.
Sannan ya gwabza da sarkin yakin garin Kaura Malle wanda manyan baraden nahiyar ke shakkar arangama da shi saboda rashin tausayinsa, amma Usman bai saurara ba sai da ya fatattaka jikin Kaura Malle ya cinye gasar a shafi na 37-39.
Ya taimakawa Sarkin Zainawa sun yaki mutanen kasar Dawaki in da ya gwabza da manyan mazaje da kauraye a shafi na 55 sannan ya yi gumurzu da Sarkin Dawakin in da ya gwada masa cewa jarumta fa ba a karami take ba kuma ba a babba ta ke ba, a wajen mai zuciya ta ke.
Usman da Sabi'u sun gwabza gumurzun yaki da mayakan kasar Damanga a Kasar Dadin kowa a shafi na 88/90.
Sun sake kutsawa yaki kasar Kwairanga daukar fansa domin bayan ture Sarki Haruna Kabir sai Sarki Sakimu ya dora kaninsa Mantau a gadon sarautar kasar, a shafi na 101/103, su Usman Mai duniya da Sabi'u sun kawar da Sarki Mantau yayin da Sarki Haruna ya koma kan gadon Sarautarsa da Damagawa su ka tsige shi.
Jarumtar kwarai mai nuna bajinta da ban sha'awa ta mayakan hadin gwiwan kasar Dadin kowa da Zainawa da Kwairanga da kuma Kaura Yalli na kasar yammaniya ta yi arangama da rundunar mayakan Kasar Damanga domin daukar fansa a kan Sarki Sakimu wanda ya addabi yankin a shafi na 105/110 wannan gumurzu shi ne ma fi hatsarin gaske da sarakunan su ka yi. Mata ma ayarin gimbiya Sailuba sun buga gumurzu karkashin Batulu in da su ka karkashe mazajen Damanga.
Usman ya yi arangama da Sarki Sakimu in da su ka yi ta dauki ba dadi ga juna har dai Usman ya sassare masa hannuwa biyu tun daga kafada duk da ganin an kassara Sakimu Zakin Hamada mayakansa ba su saduda sun gwada tsabar taurin kai da masifa sai da Usman mai duniya ya shayar da su ruwan kokon mutuwa, jini ya dinga kwarara, hannuwa da kafafuwa iri-iri kawuna kuwa ba adadi sannan 'yan tsirarun Damangawa su ka sallama, a ka ja Sarki Sakimu zuwa kasarsa ta Damanga gaban talakawansa da ya ke yiwa zalunci ya ke kashewa da izza a ka kashe shi, a ka ba talakawa zabi su ka zabo wanda su ke so a ka nada musu.
Soyayya,
Sarki Haruna ya yi soyayya da Zubaida a shafi na11/12, 21/24 wacce soyayya ce mai cike da tausayi tare da nunawa juna kauna In da a karshe su ka yi aure.
Usman mai duniya da Gimbiya Sailuba 'yar sarkin Zainawa a shafi na 40/42, 47/48
Soyayya ce ta sadaukarwa da nuna tarairayar juna.
Sabi'u ya yi soyayya ta hakika da Safara'u 'yar hakimin Dawaki a shafi na 27/29 in da ya yi takara da dan Galadiman garin.
Usman ya yi soyayya da Aisha a kasar Dawaki.
Littafin ya cika burin taurarin na daukar fansa tare da kai su karagar sarauta da kuma auren matayen da su ke so.
Bugu
Babu laifi a bisa bugun littafin da kuma wallafuwarsa a dunkulallen littafi guda daya da kasantuwarsa mai sahihiyar lambar bugu ISBN.
Tsarin shafuka ya tsaru.
Zanen bango ya dakko hoton ainahin gumurzun da ke cikin labarin.
Kura-kurai
An ce komin iyawarka da kallo mai kallon ka ya fi ganinka, duk irin kokarin da a ka yi wajen kiyaye dokoki da ka'idodin rubutu an dan samu hadewar wasu kalmomi da ya dace a rarrabasu a shafi na 4 koina maimakon ko'ina
a shafi na 5 suka maimakon su ka.
Irin wadannan kananan kura- kurai dai a kan same su tsilla-tsilla cikin littafin.

YADDA ZAHARADDEEN YA ZAMA SADAUKI MAI DUNIYA

Daga Sa'adatu Baba Ahmad Leadership Hausa
31/01/2014

Hira da Marubuci Zaharaddeen Ibrahim Kallah tare da Sharhin Littafinsa Sadauki Mai Duniya....
Ya ya sunanka?
Suna na Zaharaddeen Ibrahim Kallah
Kadan daga cikin tarihin ka?
An haife ni a unguwar Fagge da ke Kano, na yi makarantar firamare na a makarantar firamare ta Giginyu wanda daga nan kuma na koma firamare ta Race Course da ke filin sukuwa a Kano. Bayan nan na wuce makarantar sakandire ta Stadium don yin karatuna na gaba da firamare. Da na qare ne sai na je kwalegin share fagen shiga jami’a ta CAS, Kano. Daga nan ne na samu shiga jami’ar Bayero da ke Kano in da na yi digiri na karanci abin da ya shafi ilimin zamantakewar xan adam tare da siyasa (Sociology/Political Science). Na yi hidimar qasa ta a jihar Kwara wanda na koyar a wata sakandire da ke Patigi. Bayan nan na fara aiki da NGO na wani lokaci kafin na koma Jami’ar Bayero da aiki. A Bayero na koma na yi digiri na biyu a vangaren karatun ci gaban duniya wato (Development Studies).
Wacce shekara ka fara rubutu?
Na fara rubutu a shekara ta 1995 bayan na qare sakandire, xan zaman da na yi kafin na cigaba da makaranta na ga ya dace na fara rubutu.
Wacce shekara ka fara wallafa littafi?
Kafin fara buga littafi na rubutu na ya fito ne a littattafai na gamayya na turanci a wajen 2002, littafin Hausa kuma sai a 2006 littafina “Ciki Da Gaskiya” da muka yi qarqashin hukumar A Daidaita Sahu ya fito.
A matsayinka na marubucin Hausa da turanci, wanne rubutune ya fi ma sauki da ba ka sha'awa a cikinsu?
A matsayina na Bahaushe babu rubutun da ya fi mun sauqi kamar rubutu da Hausa, a cikinsa ne na fara rubutu da kuma shi ne na buxi ido. Tun a firamare a lokacin ina Monita na kan karantawa ‘yan ajina Littattafai irinsu “Ilya Xan Mai Qarfi”da “Magana Jari Ce”.
Zuwa yanzu me ka fahimta game da salo da harshe?
Salo na nufin tsari na rubutu da marubuci ya yi amfani da shi wajen isar da saqonsa. Salon da ake amfani da shi ya danganta da marubuci, wani kan yi amfani da salo mai sa karsashi da jan hankali, wani kuma kan yi amfani da salo mai wahalar da mai karatunsa.
Harshe hanya ce ta isar da saqonni, wanda ta qunshi kalmomi da suke bada ma’ana. Marubuci na amfani da harshe don isar da saqonsa ga jama’a wanda ya qunshi tunani da falsafa.
Wadanne marubuta ne gwanayenka a marubutan Hausa?
A vangaren rubutun Hausa ina da gwanaye kamar su Bala Anas Babinlata da Nazir Adam Saleh da Ibrahim Sheme da Bature Gagare da Yusuf M. Adamu
A marubutan turanci fa?
A Turanci akwai Sidney Sheldon da Abubakar Gimba da James Hadley.
Littafinka Sadauki Mai Duniya ya bambamta da littattafan wannan zamanin, menene sirrin?
Littafin Sadauki Mai Duniya labari ne da ya waiwayi shekaru sama da xari biyu baya a lokacin da ake yaqe-yaqe a qasar Hausa. Kafin na fitar da littafin sai da na nazarci salo daban-daban musamman littattafai tsofaffi da suka kawo tarihi da adabi na shekaru aru-aru. Da wannan ne na yi qoqarin fitar da littafin Sadauki Mai Duniya.
Wacce kungiya ka ke ciki?
Ina cikin Qungiyar Marubuta ta Najeriya (ANA) reshen jihar Kano, a halin yanzu ni ne Magatakardarta. Sannan ina cikin wasu qungiyoyi da dama waxanda ba na marubuta ba, waxanda suka haxa da na cigaban alumma.
Sharhin Littafin Sadauki mai duniya....
Sadauki mai Duniya Littafin da ya kere sa'a.
marubuci Zaharaddeen Ibrahim Kalla.
Shekarar bugu-2010
Jigon labari- Jarumta
Yawan shafuka- 150
Bugawa da yadawa- madaba'ar iya ruwa Zaria Road, Kano Nigeria.
ISBN- 987-987-087-880-3
Rabona da karanta wani labari na jarumta wanda har na ke ganin jarumtakar ta kai Sadaukantaka tun wani Fim da na gani na shekaru dari uku na Sarki Liyonaidas na kasar Sparta wanda ya fuskanci barazanar murkushewa idan har k'asarsa ba ta yi mubaya'a ba ga Sarkin Zaksia ba Azskiz wanda azzalumin shugaba ne da babu Sarki mai karfinsa a duk duniya a kuma zamaninsa. Sun yi jayayya da Liyonaidas in da ya gaza zubda Liyonaidas wajen kare martaba da 'yancin k'asarsa. Sun gwabza yaki ga juna amma jarumta ta hana Liyonaidas ya yi hakuri ya janye duk da kuwa Sarki Azskiz ya fi shi karfi tare da jama'a. A karshe dai an kashe Sarki Liyonaidas da dubban masu da kibbau amma wajibi ne a jinjinawa jarumtarsa da gwarzantakarsa.
A lokacin da na ke karatun littafin Sadauki mai duniya na yi ta kamanta jarumtar Usman mai duniya da Sarki Liyonaidas yadda a 'yan shekarunsa na kuruciya ya shiga daji ya kashe Karen ruwa shi ma Usman mai duniya 'yan shekarunsa na kuruciya ya shiga daji ya kashe Goggon biri.
Sadauki Mai Duniya
Wannan littafi ya kunshi labarin wasu masarautu guda biyu masarautar Kwairanga wacce ke karkakashin mulkin sarki Haruna wanda ke gudanar da mulkinsa cikin jarumta da adalci da tausayin talakawa. Yayin da daya masarautar Damanga wacce Sarki Sakimu ya ke gudanar da mulkinta cike da zalunci da izza, ya maida rayukan talakawansa tamkar na fari saboda kisan kai da mugunta, sannan duk wani mikirci tare da kulla salon dabarun yaki ya iya, Sarki Sakimu na da dabi'ar bakin ciki a duk lokacin da ya ji labarin kasar da arzikinta ya kafu ko kasar da ta shahara a fagen yaki ya kan so ya yaketa ta dawo karkashin mulkinsa ko ta wacce hanya ne.
Lokacin da Sarki Sakimu ya ji labarin masarautar Kwairanga ya yi tunani ya ga ba zai iya yakarta ba sai ya shirya makirci ya tura wasu kyawawan mata wadanda kyaunsu ya kai kyau su ka je fada a zuwan 'yan gudun hijirar yaki wanda su ka ce Damangawa sun kashe iyayensu da mazajensu, a taimake su da wurin zama. Sarki Haruna Kabir dai zuciyarsa ba ta kwanta da lamarin ba saboda ya gansu tsaf-tsaf ba wahala ko gajiyar tafiya a tattare da su amma 'yan majalisarsa su ka nuna ba wani abu. Matan nan su kai nasarar mamaye gidajen sarakan Kwairanga in da a karshe su ka kare musu kallon sirri a ranar wani biki na al'ada da Kwairanga ke gudanarwa duk shekara a ka turo maza mayaka daga Damanga, ' yanmata sukashayar da sarakai giyasu bayan sun sha sun bugu su ka hadu su ka cinyesu da yaki da rana tsaka, su ka karkashe mutane su ka nufi fada wajen Sarki, in da ya nuna jarumtarsa a shafi na 9 ' Maharan Damanga su ka yi ca kan Sarki Haruna, shi kuwa gogan naka ko in kula sai faman kirari ya ke yana cewa "Sai ni dan mutan Kwairanga kadangaren bakin tulu, a kar ka a kar tulu a bar ka ka bata ruwa, ruwan dare dama duniya na kwairanga sai dubu ta taru, ai kuwa nan da nan suka taru a kansa su ka kame Sarki Haruna Kabir su ka tafi da shi garinsu su ka daure, cikin matansa kuwa akwai wata da a ke kira Hassana wacce ta haye doki ta kubuta ta gudu tare da goyon danta Usman, 'yar Wani sarki sadauki jarumin gaske ne a wata kasa da a ke kira Yammaniya. Bayan ta sanar da mahaifinta yadda a ka tarwatsa kasar maigidanta Sarki Haruna, sai ya jajanta lamarin kuma ya dauki aniyar horar da Usmanu don ya daukarwa mahaifinsa fansar abinda a ka yi masa.
Sarki Haruna kuwa ya na daure a can wani kurkukun karkashin kasa a kasar Damanga in da ya shafe shekaru cikin wahala da azabtarwa iri-iri, yayin da kuma Zubaida daya daga cikin matan da a ka tura Kwairanga su ka yaudarar da sarakai ta kamu da ciwon son sa ta dinga zuwa har cikin firsuna ta na taimakonsa tare da shan alwashin sai ta fitar da shi daga halin kuncin da ya ke ciki.
Usman na da shekaru bakwai a ka fara shigar da shi daji a na gogar da shi ilimin yaki tun daga kan fada da mutane har zuwa dabbobi tare da koya masa dabarun fada da takobi da mashi da iya harbi da kwari da baka da sauransu.
Ya na da shekaru goma sha biyu ya kware sosai ya zama sadauki a fagen yaki duk kasar yammawa an sallama masa har su na yi masa kirari a shafi na 12 su na cewa " Usman Mai duniya na Kaura yalli, gwaggon biri makashin maza".
A lokacin ne a ka sanar da Usman labarin mahaifinsa da irin wulakancin da Damangawa su ka yiwa masarautarsa.
Ai kuwa Usman Mai duniya ya shirya tare da abokinsa Sabi'u wanda su ka taso tare dan Kaura yalli wato kawun Usmankenan, su ka nausa daji.
Shi kuwa Sarki Haruna Kabir Zubaida ta kubutar da shi daga gidan kurkukun sun shiga duniya, in da suka yi aure daga bisani wahalar da ya sha a kurkuku ta kwantar da shi ciwo.
Jarumta
Usman kuwa tun shigarsu daji ya ke nuna jarumtarsa in da ya kashe Gada suka cinye a shafi na 23, sannan ya gwabza yaki da wasu 'yan rawar wuta a shafi na 26, ya yi gumurzu da Sarkin fawa a shafi na 27. Sun buga gumurzu da mayakan garin Dawaki a shafi na 32 in da su ka biyo bayansu, maimakon Usman ya gudu sai su ka tsaya suna cafe mashi da kibbau, in da ya ke yi wa kansa kirari, "Kai arna ba ku sanni ba ne? Ni ne Usman Mai duniya, gwaggon biri makashin maza ni ne hadari malfar duniya". Nan ya afka musu ya karkashe su.
Haduwarsu da aljani wanda ya ba Usman takobin kakansa da suka ara su kai yaki a shafi na 33-34.
Usman ya shiga gasa a kasar Zainawa in da ya yi dauki ba dadi da mayaka abokan takara a shafi na 36.
Sannan ya gwabza da sarkin yakin garin Kaura Malle wanda manyan baraden nahiyar ke shakkar arangama da shi saboda rashin tausayinsa, amma Usman bai saurara ba sai da ya fatattaka jikin Kaura Malle ya cinye gasar a shafi na 37-39.
Ya taimakawa Sarkin Zainawa sun yaki mutanen kasar Dawaki in da ya gwabza da manyan mazaje da kauraye a shafi na 55 sannan ya yi gumurzu da Sarkin in da ya shafe shi a doron kasa........
Za mu ci gaba a sati mai zuwa.....

Thursday, 9 February 2012

SOYAYYA A KASAR HAUSA

Soyayya wata aba ce mai qarfi da tasiri a zukatan jama’a, wanda ke kawo farin ciki da nutsuwa a tare da masu gudanar da ita. Qarfin soyayya kan iya kawo rikici da fitina wanda zai iya girgiza al’umma. A kan iya faxawa rikece-rikice ko yaqi a kan soyayya. Soyayya ita ce ke kawo zaman lafiya da cigaban al’umma. Ita kalmar soyayya ba wai ta tsaya ba ne tsakanin namiji ko mace, ta qunshi duk wata qauna dake tsakanin al’umma.
Malam Bello Sa’id a cikin littafinsa Dausayin Soyayya ya bayyana ma’anar So da “Qawa-zuci, ko tsananin qauna da buqatar kusanta ga wani mutum, ko wani abu daban.” Anan zamu iya tabbatar da haka a nau’in soyayya daban-daban. Misali Soyayya tsakanin xa da mahaifi, ko jika da kakarsa ko miji da mata ko mutum da karansa, ko bawa da ubangijinsa da sauransu.

Idan muka yi duba a wannan zamani a qasar Hausa, kalmar soyayya ana yi mata duba akan wani abu na kyama wanda wasu mutanen sukan ji kunyar a ce suna soyayya. Ko tsakanin miji da mata, wasu na ganin sun faxi idan suka dinga nuna qauna ga matansu ko mazansu. To abin tambaya anan shi ne, shin akwai kuwa soyayya a qasar Hausa? Babu wasu isassun bayanai da za su tabbatar cewa akwai ingantatciyar soyayya wanda ta amsa sunanta soyayya a qasar Hausa, koda kuwa a xaruruwan shekaru da suka shuxe. Asali dai a qasar Hausa mutum kan auri mata ba tare da ya santa ba ko ta san shi, balle a kawo batun soyayya. Da yawa daga cikin iyaye da kakanni da suka yi aure kamar shekaru hamsin da suke wuce, da yawansu sai da suka shiga dakin matansu suka fara ganinsu. Amma duk da haka aurensu kan xore, a kan iya cewa “mutu ka raba”. Duk da cewa ba za’a ce babu birbishin soyayya a qasar Hausa ba, sai dai a ce ba ta da karfi ko tasiri. A inda akan iya ganin soyayya a qasar Hausa bai wuce kamar a dandali ba, in da samari da ‘yan mata kan haxu. A irin wannan guri saurayi kan fara nunawa budurwa soyayya, wanda idan sun aminta da juna sai budurwa ta nuna ta ta soyayyar. Ko a wannan lokaci da yawa daga cikin samarin ba sa iya furta soyayyarsu ga wadanda suke so, sai ta hanyar abokansu ko kuma qawayen waxanda suke so. Mafi akasari ko an samu fahimtar juna soyayyar ba a buxeta koda bayan aure.

Idan muka yi duba a wannan zamani akwai ‘yanci na auren soyayya, akwai birbishi na soyayya a cikin al’umma, amma duk da haka mutuwar aure a qasar ta Hausa ya yawaita. Wannan yasa dole a qara tunani cewa akwai kuwa soyayya a qasar Hausa?

Kamar yadda na yi bayani ita soyayya kan kawo farin ciki da nutsuwa, wanda idan har soyayya ta amsa sunanta soyayya mai yin ta na begen zama da wanda yake so. Sannan idan ya ga wanda yake so ko ya kalle shi zai ji wani farin ciki, koda maganarsa kuwa ya ji. Idan har soyayya ta kai soyayya babu maganar cutar da wanda ake so, babu zancen ka kaurace masa ko ka yi nisa da shi. Asali ma koda tafiya ka yi, begen wanda ka ke yi na damfare a zuciyarka wanda zai dinga bijirowa a duk wasu daqiqoqi ko sa’oi kwatankwacin son da ake. Idan akwai so a kan yi haquri da wanda ake so koda kuwa yana batawa masoyinsa. Wannan yasa hausawa ke cewa “so hana ganin laifi”
Zuciya kan ximauta idan ta rasa wanda ta ke so, ko kuma wanda ake so ya qaurace ma ta. Wasu mutanen idan har suka rasa wanda suke so, to suma qarshen zamansu a duniyar ya zo.

Idan na dawo kan batu na akan soyayya a wannan zamani, zamu ga cewa akwai abubuwa da suke nuna akwai soyayya. Wataqila saboda finafinai da littafai da ilmi da wayewa da ake samu ya sa a kan kamanta. Amma maganar gaskiya ba wai soyayya ba ce ke samuwa ba, illa kawai sha’awa. Duk da cewa sha’awa kan rikixe ta zama soyayya, amma kafin a kai ga haka a kan ci karo da wasu matsaloli. Misali namiji kan ga mace ya ji sha’awarta saboda wasu siffofi na ta, sai zuciyarsa ta raya masa yana son wannan mace. Anan sha’awa ta yi tasiri a tare da shi, sannan samuwar soyayya a tsakaninsu ba abu ba ne mai sauqi koda kuwa za su kasance tare. Mafi akasari akwai wasu abubuwa a aikace wanda za su taimaka wajen samuwar soyayyar. Waxannan abubuwa sun banbanta daga mutum zuwa zuwa mutum, ko daga jinsi zuwa jinsi. Misali idan na auri mace saboda kyan qirjinta, sai ya kasance ba na samun wasu abubuwa daga gareta, kamr tarayraya da damuwa da ni, to ba lalle ba ne wannan sha’awa da nake mata ta rikixe ta zama soyayya. Domin me yuwa ni ina da bukatar a tarayraye ni a nuna an damu da ni, ko a nuna ana tausayina. Wanda idan da ya kasance cewa ana tarayrayata da kula da ni kamar kwai, wannan sha’awa za ta rikixe ta koma qauna mai qarfi.

A qasar nan akwai qabilu da dama, amma idan aka yi duba sai a ga mutuwar aure tafi yawa a qasar Hausa musamman a gurin bahaushe. Baya ga wannan addini musulunci ya bamu dama na auren mace har guda huxu, amma duk da wannan garavasa ba ma iya jure zaman aure. Sai kuma can waxanda mace xaya suke aure a rayuwar su ba sa fuskantar wannan matsala. Akwai wata samina da muka tava shiryawa a Qungiyar Matasa da Cigaban Mahalli (YEDA) a kan dalilan mutuwar aure a qasar Hausa. Tunanin wannan samina ya zo mana bayan wani mai unguwa da ya kawo mana kukansa cewa a iya unguwarsa daga watan Janairu zuwa watan Agusta an samu mutuwar aure har tamanin da uku (83). Wannna ba qaramar masifa ba ce da ke bukatar a yi ma rubdugu. Abin lura ana shi ne muna cikin babbar matsala ta mutuwar aure.

Dalilan mutuwar aure na da yawa wanda warware wannan matsala sai an yi duba na gaskiya ba tare da son rai ba. Amma tushen warware wannan matsala na ga samun tabbatatciyar soyayya. Sai mutanen mu sun daina tunanin So ba gaskiya ba ne, sai mutanen mu sun fara nuna halaye na soyayya. Halayen da suka haxa biyayya, da amana da tausayi da kwalliya da kamun kai da aiki da hankali da tunani mai kyau da bai wa mace haqqinta da kuma adalci da kunya da mutunci da son addini tare da aiki da shi, da dogaro da kai da sauransu.

Idan za a samu waxannan halaye zai taimaka wajen samuwar soyayya mai qarfi, wanda za ta xinke barakar da ake da ita. Domin samuwar ingantatciyar soyayya ne zai kai ga auren nan na “mutu ka raba”. Wani masanin soyayya ya ce “So ya kan tura saiwoyinsa cikin zuciya ne, saboda haka idan aka tunbuko shi, shi ma sai ya tunbuko zuciya.” Tabbas idan akwai makamancin irin wannan So, mutum ba zai so rabuwa da masoyinsa ba.

A qarshe nake jan hankalin mutane da su daina kyamar kalmar “So” domin ba qarya ba ce. Allah da ya halarci xan adam ya sanya masa xabi’a ta so, zamu iya ganin hakan a cikin littafinsa mai tsarki.
“Kuma yana daga cikin ayoyinsa, da ya halitta muku matanku daga jinsin ku domin ku rayu (tare da su) cikin nutsuwa, ya kuma sanya soyayya da jin kai a tsakaninku.”
 Zaharaddeen Ibrahim Kallah