Wednesday, 16 September 2020

Kafuwar Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo


A watan Janairu, 1939 aka fara buga jaridar 'Gaskiya Ta Fi Kwabo'. An yi tunanin kafa ta ne don a yi martani ga farfagandar da Jamus da Hitler suke yaɗawa a yaƙin duniya na biyu da ake gwabzawa. 

An nemi Abubakar Imam ya zama editan jaridar, wanda a lokacin yana koyarwa a Katsina. An ƙara masa albashi daga fam shida da silai goma zuwa fam takwas, don a ƙarfafe shi ya karɓi aikin.

Jaridar ta maye tsohuwar jaridar da ake da ita a lokacin mai suna, 'Jaridar Nijeriya Ta Arewa' (Nothern Nigerian Newsletter), wacce ake buga ta a maɗaba'ar Gwamnatin Gargajiya ta Kano (Native Authority Kano). 



Mr L.C Giles da yake shugaban gudanarwa a Literature Bureau ya nemi shawarar Abubakar Imam ko za a sa wa jaridar suna 'Kwabo Kwabo' ko 'Kawo Kuɗi' ko kuma 'Daɗin Nazari'. Amma da Abubakar Imam ya iso Zariya, ya bada shawarar raɗa mata suna 'Gaskiya Ta Fi Kwabo' wanda shi ne sunan da aka amince da shi.

Jaridar ta fara da ƙafar dama, domin ba ya ga mayar da martani ga farfagandar Jamusawa, an shigo da labarai da rahotannin gida, wanda suka shafi wayar da kan talakawa akan ayyukan gwamnati da na masarautu. 

Zadeen Kano

Monday, 14 September 2020

Tasirin Marubuta Da Gudunmawarsu A Ƙani Na 21


Tun lokacin jahiliyya, marubuta na da mihimmanci a al'umma. Domin kowacce ƙabila na da marubutanta na musamman. A wannan lokaci, duk ƙabilar da ba ta da marubuta, yakan zama abin gori da koma baya a gare su. 

Da rubutu ne, musamman waƙa suke isar da saƙonni. Koda an taɓa ƙabilarsu, kafin a ce abu ya kai ga ɗaukar makami, marubuta ne za su fara mayar da martani.

An yi wani fitatcen mawaƙi kafin zuwa musulunci a ƙasar Larabawa da ake kira Zuhayr Bin Abi Sulma, wanda ya fito daga Banu Muzaina. Wata waƙa da ya rubuta akan haɗa kai da daina ɗaukar fansa akan yaƙe-yaƙen Larabawa ta yi shaharar da ta ɗaga mutunci da martabar ƙabilarsu. Wannan waƙa sai da aka rubuta ta da ruwa gwal aka rataye a ɗakin Ka'aba. Wanda a baya ƙabilarsu ba ta kai matsayin waɗanda suke cikin mawaƙan da ake rataye rubutunsu a Ka'aba. Saboda ɗaga darajar ƙabilarsu, sai da ya zamo duk wata bazawara a wannan ƙabila an aureta. 

Marubuta sun kasance mutane ne masu daraja a al'umma, saboda sune fitila dake haskawa al'umma yadda rayuwa ta sa gaba. Mutane ne masu hikima da fikira tare da hangen nesa. Akoyaushe suna ƙoƙarin nazartar al'umma, walau ta hanyar karace-karance ko ta nazari, kula, bibiya da tariyar baya.

A wannan zamani ma haka abin yake, domin samuwar marubuta ya taka rawa a tarihin cigaban duniya. Marubuta iri-iri sun bayar da gudunmawa, waɗanda suka ƙunshi marubutan wasan kwaikwayo, rubutun zube ko na waƙa. Kai har da marubuta a ɓangaren aikin jarida da marubutan da ba na rubutun ƙirƙira ba.

Irin waɗannan gudunmawa ta shafi ɓangarori da dama da suka shafi tattalin arziƙi, da siyasa, zamantakewa, addini da al'ada, tsaro, da ilimin sana'oi, ilimin kimiyya da fasaha da sauransu.

A wannan ƙarni na 21, abubuwa sun sauya a tarihin duniya. An shiga wani zamani da Turawa suka yi wa laƙabi da globalisation, wanda aka ɗauki duniya kamar wani ƙaramim ƙauye ne da kowanne ɓangare ya san me ɗan uwansa yake ciki, ko kuma abin da ya shafi mutum ɗaya ya shafi mutane da yawa. 

A yau, a wannan duniya da muke ciki, matsalar tsaro ta shafi kowanne ɓangare. Domin idan wata ƙasa ta shiga rikici da yaƙe-yaƙe, kafin wani lokaci sai ka ji ɓullar su a wata ƙasa. Misali, ƙasar Libya ta shiga halin yaƙi da taɓarɓarewar tsaro, wanda kafin wani lokaci, rikici da yaƙe-yaƙe sun yaɗu a wasu sassa na Afirika dake maƙwabtaka da su.

A yau matsalar sace-sace, fashi da makami, da satar mutane, fyaɗe da shaye-shaye ya zama matsalar kowa. Abubuwan da a tarihi wasu yankuna ba su san da su ba, yanzu sun addabe su. Ko a wannan lokaci da cutar Korona ta ɓulla a ƙasar Chana, ta gama game duniya, saboda cigaban da aka samu ta kowacce fuska da kasancewar duniya abu ɗaya.

A cikin wannan tafiya da ake ta sabuwar duniya a ƙarni na 21, samun bayanai da ilimi ya zama kamar ƙiftawar ido, duba ga cigaban da aka samu a kafofin sadarwa na yanar gizo da fasahar zamani a ɓangaren na'ura mai kwakwalwa. Wannan cigaban ya game kowanne ɓangaren rayuwar al'umma.

A wannan lokaci, wacce irin gudunmawa marubuta za su bayar wajen cigaban al'umma? To, gudunmawar da za su bayar ba ta da banbanci da wadda magabata suka bayar a baya. Amma a wannan zamani dole salo da tsarin isar da saƙon ya banbanta. Dole marubuta su tafi da zamani, idan suna son yin tasiri a wannan tafiya ta sabuwar duniya.

Da farko dai sai marubuta sun tafi da kafofin sadarwa na zamani da ake da su irin su Facebook, Twitter, Youtube, Instagram, linkedin, whatsapp da sauransu. A yau akwai ɗinbin manhajoji da ake hada-hada a cikinsu, wanda rubutu na kan gaba a wannan tafiya.

A cikin waɗanna kafofin sadarwa, akwai miliyoyin al'umma, wanda babu irin sharar da ba za ka samu ba. Don haka, wajibi ne marubuta su banbanta da ɗinbin mutanen dake cikin wannan kasuwa. To amma, ta ya ya za su banbanta kansu a cikin tarin mutanen dake cikin wannan tafiya?

A nan dole ne matsayinsu na masu ilimi da bincike, kuma fitilar al'umma ya yi tasiri a zuciyarsu. Wannan shi ne zai yi musu alƙibla, ya zamo duk wani abu da zai fito daga maɗallin kwamfutarsu ya zamo rubutu ne da ya sha banban da game gari. 

Dole a samu bincike, nazari, kula, bin diddigi da bibiya a cikin rubutunsu. Wannan shi zai zama gishiri ko magin rubutu, wanda zai gamsar da mai karatu.  

A nan ban yi amfani da kalmar gishiri da magi a yadda ake fassara kalmomin a rubutu ba. A'a, ina nufin dukkan abubuwa da zai gamsar da mai karatu, ya tsima shi tare da riƙe shi ko jan hankalinsa, da bashi ainahin hoton abin da marubuci ke son isarwa.

Idan kana rubutu akan rashawa da cin hanci, za ka yi nazari sosai tare da bin diddigi, yadda idan rubutun ya fito, ƙarya ne wanda aka yi akansa ya musanta. Wani marubuci Abdulaziz A. Abdulaziz, ya yi rubutu akan wata tsohuwar minista a Najeriya akan sahihancin takardun da suka sahale mata hidimar ƙasa. Wannan rubutu  da ya amsa sunansa, sai da ya yi sadadiyar wannan minista ta yi murabus. 

Haka ma wani marubucin ɗan ƙasar Ghana Anas Aremeyaw Anas da ya kware akan rubutun bincike da bin diddigi, ya bankwaɗo aikin rashawa da cin hanci a ɓangaren wasanni, wanda hakan ya yamutsa hazo sosai. Wannan bincike na shi ya sa wasu shugabanni da masu horarwa suka rasa kujerunsu. 

Irin wannan salo yakamata marubuta su yi amfani da su wajen bada gudunmawa ga al'umma. Ana da buƙatar marubuta su yi rubutu akan abin da ya shafi mulki da gudanarwa, siyasa, shari'ah, tsaro, ilimi, kasuwanci da sauransu. Akwai abubuwa na daɗi da rashinsa sosai a wannan ɓangarori. Yin rubutu zai nusar da jama'a tare da kawo sabon tunani na cigaban da aka samu a duniya.

Wannan rubutu zai iya kasancewa na ƙirƙira, ko ba ƙirƙirarre ba. Idan ka yi rubutun ƙirƙira, dole ya kasance ka gabarta da jigonka akan dukkanin tsanikan rubutu, sannan a ƙarshe ka fitar da mafita ta hanyar da tsari da dokoki suka amince  da su. 

A ƙarni na 20 an ga irin gudunmawar marubuta irin su James Hadley Chase (Rane Lodge Brabazon) da Sidney Sheldon da Abubakar Imam da Chinua Achebe da Wole Soyinka suka bayar akan rayuwar da ake ciki a wannan lokacin. Marubuta a ƙarni na 21, sai a ce muku ga fili ga mai Doki.


Daga

Zaharaddeen Ibrahim Kallah 

zikallah@gmail.com

Twitter/Instagram @zikallah


Cin Dawisun Hakimi


Wani Hakimin ƙauye ne ya kai wa abokinsa Hakimi da yake hakimci a cikin birni ziyara. Shi wannan Hakimin birni yana da arziƙi da wadata sosai. 

A lokacin da Hakimin ƙauye ya isa gidan abokinsa, an yi masa tarba ta arziki. Don an kawo masa wani nama, wanda da ya tauna sai ya ji kunnesa ya motsa, saboda daɗi. Amma kuma ya rasa wane irin nama ne. 

Nan ya dubi abokinsa ya ce. "Ranka ya daɗe, wannan wane irin nama ne? Shi ba na kaza ba, ba kuma na zabo ba."

Hakimin birni ya yi murmushi ya ce. "Naman ya yi maka daɗi kenan, naman Ɗawisu ne."

Ya gyaɗa kai, "Gaskiya naman ya yi, amma a ina kake samun naman Ɗawisu?"

Hakimin ya ɗan kyalkyale da dariya sannan ya ce. "Akwai wani mutum da yake kawo mana, idan kana so sai a ce ya kawo maka."

"A, ina so. A ce ya kai min guda huɗu gida." Hakimin ƙauye ya nemi a kai masa.

Bayan 'yan kwanaki da zuwansai birni, sai rannan aka ce ga mai Ɗawisu ya zo daga birni, abokinsa ya aiko mai sayarwar kamar yadda suka yi alƙawari. 

Lokacin da aka shigo da shi, ko tambaya bai yi ba sai ya ce a je a yanke ɗawisan har guda huɗu gaba ɗaya. Zuwa can Hakimi ya tashi don ya ga yadda ake yankan. Ya tarar an yanka guda ɗaya, an ɗauko na biyu kenan an danne za a yanka, sai Hakimi ya tambayi mai sayarwa. "Nawa ne kuɗin kowanne?"

Mai sayarwa ya ɗago, hannunsa na riƙe da wuka ya ce. "Allah ya baka nasara, naira dubu arbain ne kowanne."

Ba tsammani sai ji aka yi Hakimi cikin ƙaraji ya ce. "Ɗaga shi, ɗaga shi dan ubanka."

Ashe shi Hakimi ya ɗauka Ɗawisun ba wata tsadar kirki ba ce da shi.

Mai sayar da ɗawisu ya ɗaga Ɗawisu yana cike da mamaki.

Cikin mazurai, Hakimin ya dubi mai Ɗawisu ya ce. "Ka kwashe kayanka, shi ma wanda ka yanka a kaiwa Ranka ya daɗen ya biya, tun da shi ya saba ci."

Lokacin da Hakimin birni ya ji labari, sai ya yi dariya har da kwalla. Tun daga wannan rana idan suka haɗu da abokinsa Hakimin ƙauye, abin da zai fara gaya masa shi ne. "Ɗaga shi dan ubanka."


(c) Zaharaddeen Ibrahim Kallah

zikallah@gmail.com

Twitter: @zikallah


Saturday, 5 September 2020

Duniya Makaranta

Allah ya bamu ikon cin jarabawarsa. Ita rayuwa, gwagwarmaya ce gaba ɗayanta. Lokacin da Abubakar Imam da takwarorinsa suka tafi Birtaniya a jirgin ruwa, sun samu aƙalla wata ɗaya akan ruwa.

Kullum sai dai su ci su sha, sannan su kwanta. Anan ne Abubakar Imam ya fahimci ashe gwagwarmayar rayuwa tana da daɗi. Ba su da matsalar abinci ko.makwanci, amma kuma duk sun takura. 

Duk wani hali da za mu shiga yana cikin gwagwarmayar rayuwa. Wani ya zage ka, ko a taka, ko a ja kaima ka ja, duk ba sabon al'amari ba ne. 

Mun yi imani za mu cigaba da gwagwarmaya, domin ita ce tushen rayuwa. Haƙika Allah maɗaukakin sarki yana tare da mu, matuƙar ba mu juya masa baya ba.

Zaharaddeen I. Kallah
zikallah@gmail.com
@zikallah

Wednesday, 26 August 2020

Ranar Hausa: Amfani Da Harshen Hausa A Manyan Tarukan Afirka


 A yau 26 ga watan Agusta, 2020 ake bikin Ranar Hausa ta duniya. Wannan biki ana yinsa a duk ranar 26 ga watan Agusta na kowace shekara. 

Harshen Hausa na daga cikin manyan harsuna a duniya, wanda a halin yanzu shi ne harshe na 11 da aka tabbatar a duniya yana mai ɗinbin masu magana da shi.

Wani mizani da ake amfani da shi wajen gane cigaba da ɗaukakar harshe, shi ne adabin wannan al'umma. A yau Hausa na da ɗinbin rubuce-rubuce tare da marubuta maza da mata. 

Tarihin rubuce-rubucen Hausawa yana da faɗi kwarai, domin magabata irin su Usman Dan Fodiyo da Nana Asma'u da Abdullahi Gwandu da Muhammad Bello da sauransu sun yi waƙe cikin harshen Hausa, a ƙoƙarinsu na yayata addinin musulunci. Rubuce-rubucensu na cikin rukunin adabi a ɓangaren waƙe.

Ko lokacin da Turawan mulkin mallaka suka shigo ƙasar Hausa, sun ɗabbaƙa rubutun adabin Hausa na zamani, inda aka fara samun ƙirƙirarrun labarai. Duk da cewa marubuta irin su Abubakar Imam da Tafawa Balewa 'yan boko ne, amma an nemi su yi rubutunsu cikin harshen Hausa. Wataƙila hakan ne zai ba wa Turawa dama su fahimci Hausawa idan suka yi rubutu da harshensu, fiye da su yi amfani da harshen aro.

A wannan ƙarni na 21 da muke ciki, harshen Hausa ya samar da marubuta da zai yi wuya a kawo adadinsu cikin sauƙi. Duk da koma bayan da ake ganin mata na da shi a duniya a ɓangarorin rayuwa, zan iya cewa a duniyar rubutu sun yi nisa a ƙasar Hausa. Misali, a kaf Najeriya, babu wata jaha da za ta yi tarayya da jihar Kano a ɓangaren marubuta mata.

A wannan shekara ta 2020, taken bikin Ranar Hausa ta bana shi ne "Buƙatar Majalisar Ɗinkin Duniya da Ƙungiyar hada kan ƙasashen Afirka ta AU da ma Ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka ta ECOWAS su mayar da harshen Hausa a matsayin na sadarwa a ƙungiyoyin."

Wannan yunƙuri zai taimaka wajen haɓaka tattalin arziki da al'adun yanki, duba ga yadda ake amfani da harshen a yankunan nahiyar.

Wannan ranar dai ta samo asali ne a shekarar 2015, a lokacin da ma'aikacin sashen Hausa na BBC, Abdulbaki Aliyu Jari da wasu abokansa na shafukan sada zumunta, musamman Mazhun Idris suka ayyana wannan rana ta 26 ga watan Agusta a matsayin Ranar Hausa, wanda masu magana da harshen Hausa suke fitowa su tattauna akan harshen tare da kallon cigabansa ko ƙalubalen da yake fuskanta a wannan ƙarni.  

A shekarar 2018 ne aka fara gudanar da bukuwan Ranar Hausa a  zahiri, wanda aka yi shi a gidan Ɗan Hausa dake Kano da wasu ƙasashe a faɗin duniya.

A ƙarshe ina taya ɗinbin Hausawa a faɗin duniya murnar wannan rana, wacce take da mihimmanci wajen ɗabbaƙa harshe, al'adu da tattalin arzikin ƙasar Hausa. Zai yi kyau mu raya ranar ta yin rubutu cikin harshen Hausa da yayata shi. Shi dai kayan aro ba ya rufe katara.

Zaharaddeen Ibrahim Kallah

zikallah@gmail.com

Tuesday, 7 January 2020

Murucin Kan Dutse...


(Tsakure daga wani sashe na sabon littafina)

Babi Na Bakwai

Babu kakkautawa ruwan bamabamai ake daga sojojin ruwa na Najeriya, wanda cikin kwana uku babu sararawa. Wai da an ji shiru, an dauka bako ya tafi ko kuma makamansa sun kare, sai a ka ji sabon hari. Ashe wannan wani salon yaki ne na sojojin Najeriya, wannan salon nasu ya sha banban da abin da suke zaton abokan hamayyarsu zasu zata.

Da farko dai sun san cewa manyan sojojin Biyafara suna gaba da mafi yawan sojojinsu, bayan wannan sun halarci makarantu na horon sojoji a Birtaniya da Amurka da Indiya zuwa Ghana tare. Don haka suna kyautata zato duk wani motsi da suka yi, watakila wannan yayyen nasu dake cikin Biyafara su fahimta. Hakan yasa dole su yi takatsantsan.

Ga yadda abubuwa suke tafiya kamar an yi yamma da kare ne, domin yayyen nasu sun gaza fahimtarsu a wannan lokaci. Wannan luguden wuta da ake ashe ana so a bawa rundunar Isaac dama ne ta isa James Town. Shi ma Akininde dake tsaunin Bonny zai yunkuro da tashi rundunar ya kawo wa Isaac dauki. Haduwarsu zai taimaka a kama James Town cikin sauki. Hakan kuwa aka yi, cikin kankanin lokaci rundunar ta 3MCDO ta danna da qarfin tsiya ta mamaye wannan gari.

Wai duk wannan dawurwura da ake ashe dai ba ita ba ce ainahin abin da ake son cimmawa, duk dai salon yaudara ne na yaki. Wannan dabara kuwa ta kara tabbatarwa sojojin Biyafara cewa lalle sojojin kasar Najeriya na kokarin cin Fatakwal ne daga Tsaunin Bonny, domin dai ga su sun danno har sun shigo James Town.

Hakan yasa suka sakankance suka firfito daga maboyarsu, musammam irin gwalalo da a kan gina saboda buya ga harsasai da ruwan bama-bamai. Cikin wannan dauki babu dadin da ake ta yi, wannan bataliya ta Najeriya ta dauke hankalinsu ga sharrin da ake kulla musu. An ce dama yaki dan zanba ne, wannan duk wata dabara ce da zata bawa ainahin sojojin Najeriyar dake tafe cikin surkikiyar daji su 35, 000  su samu damar isowa garin Oron, wanda daga nan ne zasu gangara zuwa kogin Opobo.

Amma fa dole su zamo a shirye, kuma su kula. Domin yayin da suka ba wa kogin Opobo baya, sojojin na Biyafara za su so su tarfa su, yadda idan wuta ta yi wuta su yi kokarin dannasu har sai sun dangane da ruwan dake bayansu. Watakila za su so yin abin da suka yi wa runduna ta biyu ta Najeriya, wanda suka yi kokarin sulalowa ta cikin kogin Naija a kokarinsu na shiga Asaba. Runduna ta biyu ta samu nasarar haurowa da wasu daga cikin makamansu, amma yayin da sojojin na ‘yan tawaye suka tarfa su sun kasa kare kansu, wanda da yawansu sun mutu ko dai da harsashi ko kuma sun nutse a ruwa.

Sojojin na Najeriya na samun karfin gwiwa, musamman yadda abubuwa ke tafiya daidai kamar yadda aka tsara, illa ‘yan kananan matsaloli da sukan yi kokarin magance su. Duk inda suka bullo sukan fito ne ba tare da abokan gaba sun sani ba, don haka cikin ruwan sanyi suke kama su.

Ai kuwa a cikin wannan yanayi na rashin takamaimai me yake faruwa tawagar su Sanusi ta karaso cikin duhun dare ga kuma ruwan sama da ake tafkawa. To amma kuma abin ka da baki da basu san dawan garin ba, maimakon su sauka a Oron kamar yadda aka tsara, sai sojojin suka sauka a Tsaunin Parrot, wanda yake hannun riga da Oron xin. A wannan lokaci sojojin ruwa na Najeriya sun shiga kwana na uku suna sakin wuta, wanda dole a sanar da su cewa sojojin sun iso, amma sun sauka a Tsaunin Parrot kuma ba kamar yadda aka tsara ba. Dole a sanar da su sojojin na yunkurin haurawa su karasa Oron, wanda hakan na nufin sai sojojin ruwan sun tsahirta da sakin wuta su dan sha ruwa. Hakan sai ya bawa su Sanusi damar haurawa suka shiga ainahin inda ake son su sauka.

A lokacin da sojan ruwan suka tsahirta, abin fa bai tsaya haka ba sai sojojin sama suka dauki na su ta wani salo da kwata-kwata hankalin abokan gaban zai karkata daga Oron. Ka san ginshikin sojojin dake tafe za su haura ne ta cikin ruwa, inda za a yi amfani da kwale-kwale. Don haka sai an yi da gaske, kar abokan gaba su far musu a wannan lokaci. Hakan yasa ba a yi sakaci ba, aka ba wa sojojin sama ta su damar.

Sojojin saman sun shiga nasu barin wuta ta bangaren arewa zuwa Uyo da kuma yamma da kogin Opobo. Hakan zai sa runduna guda biyu dake fuskantar abokan gaba ta dauke hankalinsu, su zaci sune ainahin babbar rundunar Najeriya, inda ake kyautata zato za su rike wuta suna mai fuskantar Oron, da kuma gabas da ita ta bangaren wani karamin gari da ake kira Okopedi, su ma su rike wuta.

Innalillahi Wa’inailahir Rajiun, wanda bai san yaki ba shi yake nemansa. Babu abin da kake ji sai qarar manyan-manyan bindigu. Wasu bindigun kana jin kararsu ka san bindugun nan ne da ake kira 2 Inch da kuma 81 mm mortars. Su kuma abokan gaba kasancewar sun san cewa zai yi wuya a shammace su ta baya, saboda yanayin gurin da ba zai ketu ba suka sakankance har ba su girke manyan bindigu kirar 2 inch da 81 mm mortars. 

Ana cikin gwabza wannan yaki, kamar daga sama sai sojojin ‘yan tawaye suka ji wani sabon hari da karar bindigu ta inda ba sa zato, su waiwaya haka sai suka ga wata runduna ce mai tarin yawa ta vallo ta bayansu tana tafe kamar bakin gajimare. Lahaula Walaquwata Illabillah, ta ina wadanna sojojin masu tarin yawa suka faso kamar aljannu. Su dai a iya saninsu babu wata hanya takamaimiya saboda ruwa da yanayi na chabi da bishiyoyi na kurmi. Wani gurin ma idan ruwa ya yo ambaliya, ya kan hadiye mutum har wuya, ko kuma irin wannan tabon mai kama da ruwan gam da kan shanye mutum a hankali yana ji yana gani.

Zaharaddeen Ibrahim Kallah

Wednesday, 19 April 2017

GASKIYA DACI GARE TA



Ina ga lokacin da zamu gaya wa kanmu gaskiya ya yi. Halin da al’umma kasar Hausa suka samu kansu ya ta’azzara. Duk wanda zai ce Arewa ba a cikin talauci da fatara da jahilci, ya yaudari kansa, kuma bai yi wa kasar Hausa adalci ba. A yadda magabata suka fada idan mutum yana da wata cuta kuma ya ki yarda yana da ita to ya shiga ukuba, kuma samun saukinsa abu ne mai wuya a gurinsa. Amma da zarar ya yarda yana da ciwon, to ana tsammanin sauki ya samu. Ko ba komai ya san me yake damunsa kuma zai tashi ya nemi magani.  

Babu dadi ga yadda wasu tsirarrun mutane ke kokarin gurbata tunani jama’a, watakila don neman suna ko wata bukata tasu ta daban da su suka santa. Amma ina mai tabbatarwa irin wadannan mutane cewa idan guguwar canji ta taso bubu wani abu da zai iya tare ta. Allah ubangiji shi ne zamani kuma shi yake juya zamani yadda ya so.  

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya yi jawabai a kan fahimtarsa bisa halin da muke ciki da yadda za a samu waraka. Kuma bana jin ya ce lalle sai an bi abin da ya fahimta.  Bukatarsa ita ce a zauna a kalli abin da ya kawo da idon basira. Abin da ban ji dadi ba  shi ne  yadda aka mayar da abin cin mutunci da tozartarwa da izgilanci. Mai makon abin ya zamo bisa doron ilimi da tattunawa ta fahimta tsakanin shugabanni da malamai da sauran al’umma.  

Ban ga dalilin da jama’a zasu yi tariyar baya ba su dauko wata mahawara tsakanin mai martaba Sarki da marigayi Sheikh Jafar Muhammad Adam, rahimullah. Wannan ya nuna jahilci da kokarin tada zaune tsaye. Muhawara ce aka yi lokaci mai tsayi da ya shude, kuma wanda suka yi ta suka fahimci junansu abin ya wuce kafin rasuwar Malam. Shin suna ganin sun yi wa Malam adalci da suka bijiro da wannan al’amari wanda ba shi da alaka da abin ake ciki a yanzu?

A satin da ya gabata mai martaba Sarki ya tura ‘yarsa Shahida ta wakilce shi a kan taron tunawa da ‘yan matan Chibok da aka sace aka yi garkuwa da su. Ga masu hangen nesa sun ga wannan wakilci a matsayin abin da ya dace, kasancewar taro ne da zai waiwayi batun yaran wadanda suke kusan sa’oi ga Shahida. Ni ina ganin hikimar wannan zai tunawa jama’a cewa iyayen wannan yara sun tura ‘ya’yansu neman ilimi, kuma burinsu su samu ilimi kamar yadda Shahida ta samu har ta iya yin wannan wakilci. Ashe mutane jira suke su ga ta inda za su yi cin mutuncinsu, sai wanda suke zato bai halarta ba. Wannan yasa suka juya ta wani bangaren cewa suturar da yarinyar ta sa ba su dace ba. Ashe dama yanzu ba irin kayan da ‘ya’yan mu da kannen mu da yayyen mu mata suke sa wa ba?  

Mai martaba ba zai zamo ma’asumi ba, a matsayinsa na adam yana da tashi gazawar. Amma a wannan hali muna bukatar gudunmawarsa don fitar da A’i daga rogo. Ai tun tuni dama mutanen Kano mutane da basa karbar sauyi cikin sauki (conservative), ba jayayya a wannan. Amma idan har suka karba suna rinjayar sauran bangarori na kasar Hausa. Ina ji a jikina wannan guguwa da ta taso zata yi tasiri wajen sauya tunanin jama’a da tabbar al’umma ingantatciya. 

A ganin wasu jama’a shi mai martaba Sarki bai kamata ya shiga wannan al’amari ba. To, wai idan irinsu ba su shige mana gaba ba su waye zasu tsamo arewa daga halin da take ciki. Wadanda ake sa ran su zasu yi wa Arewa gata sune wadanda suka kara jefa ta a rami. Tun da magabata irin su Ahmadu Bello (Sardaunan Sakkwato) suka gabata, shugabannin da suka gajesu ba su yi wa Arewa abin da ya kamata ba. Da sun rike matsayinsu na magadan su Sardauna da Aminu Kano da ba mu shiga wannan hali da muke ciki ba. Arewa ta rasa jagoranci na gaskiya. A yau su wanene shugabannin Arewa? Ban ga wani shugaba ba da zai fito ya ce a yi gabas, gaba daya mutane su bi kamar yadda muke gani a kabilu kamar na yarabawa. Shin irin wadannan mutanen da basu tsinanawa Arewa komai ba ake sa ran za su goyi bayan sabon tunani? 

Lokaci ya yi da za a daina kallon maganar gaskiya a matsayin siyasa. Komai a ce siyasa kamar mu muka fi kowa siyasa, amma mun rike kaho wasu tsirari na tatsa. Duk siyasar ta mu yau kusan shekara hamsin da bakwai da karbar mulkin kai amma har yanzu bamu iya samar da ilimi da lafiya da abin yi ga dinbin al’ummar mu ba. Su kansu alkaluma da ake fitarwa da suka nuna tsananin talauci da fatara gami da rashawa da cin hanci da suka yi mana katutu, wasu na ganin siyasa ne ko kuma tonon asiri. Ya ilahi, dama haka ake gina kishin kasa a kasashen da suka cigaba har muke sha’awarsu?

Muhammad Sanusi II, shi ne Amir na Kano wanda Allah ya dorawa shugabancin mutanen Kano. Babu wanda yake tantama cewa a matsayinsa na Sarkin Kano Allah zai tambaye shi yadda ya gudanar da mulkin talakawansa duk cewa kundin mulkin kasa ya karbe musu cikakken iko. Wai ance Sarki ya rage magana, amma kuma jama’a kullum na turereniya kai kukansu gare shi na irin cin zarafi da tauye hakkin dan adam da yake faruwa. Na tambata duk wanda ke cike da tausayi da imani idan ya ji irin kwadon da ake damawa a wannan sashi na kasar nan sai zuciyarsa ta koka. 

Kamar yadda na ce mai martaba Sarki ba ma’asumi ba ne, mutum ne kamar kowa; amma kuma Allah ya yi masa baiwa ta ilimi. Wannan ba yana nufin ina kare shi ba ne ido a makance. A’a, akwai abubuwa da yadda ya fahimce su mun yi mun yi hannun riga da shi. Misali, maganar samar da tashar jirgi ta zamani mai amfani da lantarki na kalle ta a matsayin cigaba ga jihar Kano. Bana ganin bashi ne da za a karba a kashe wajen biyar albashi ko wata sharholiya, na kalli yunkurin a matsayin abin da zai samar da aikin yi sannan ya biya kansa bashin da aka ci masa. Amma ba na shakkar mai martaba masanin tattalin arziki ne wanda ya nuna basirarsa lokacin da duniya ta shiga masassarar tattalin arziki a shekarun baya; wanda Najeriya ba ta ji radadin abin ba kamar sauran kasashe, sannan yunkurinsa ya tallafi bankunan mu daga durkushewa. Wannan ba zai sa na kasa yi masa uziri don jin mai ya taka da nashi ra’ayin. 

Amma ina mamaki a wannan zamani har wasu na tunanin a hana mai martaba Sarki magana. Haba! A wannan karni na ashirin da daya, lalle muna da sauran aiki. Gaskiya wata guguwa ce ta taso wanda Allah ne yasan inda za ta tsaya. Masu rike da madafan iko akoyaushe ba sa son kan talakawa ya waye don gudun bore. Haba, Kano ce fa wanda Malam Aminu Kano ya rayu a cikinta. Yau Malam Aminu Kano ya cika shekaru talatin da hudu da rasuwa, amma abin kunya ne a ce irin wannan al’amari na faruwa. Malam ya rasu ya bar riguna guda uku, mutumin da bai yarda an sa masa janareto ba don kar ya damu makota da kara kuma bai basu wuta ba. Maganar Malam akoyaushe ita ce talakawa da yadda za su samu waraka. Yau ina akidar NEPU wanda tasa aka azabtar da kashe da yawa daga magoya bayan tafiyar. Shin zamu koma lokaci ne da mata irin su Gambo Sawaba suka sha azaba da duka wanda har ya yi sanadin fashewar mahaifarta? 

Mutanen Arewa na bukatar mutanen da zasu fada musu gaskiya ko mun dacinta. Arewa na bukatar mutanen da zasu karfafi ilimi da bawa mata hakkinsu da musulunci ya basu. Arewa na bukatar mutane da zasu taimaka wajen yakar zaman kashe wando da shaye-shaye da miyagun ayyuka. Ba yadda za a fita daga wannan kangi idan shugabanni ba su yi yunkurin samar da ilimi ga ‘ya’yan Arewa ba. Irin wannan yunkuri ne yasa mutane irinsu Awolowo suka samu soyayyar mutanensu saboda ganin amfanin abin da suka shuka.

A lackar da aka gabatar don tunawa da Malam Aminu Kano a wannan shekara na ji dadin abin da mataimakin gwamnan Kano Prof. Hafizu Abubakar ya ce yayin jawabinsa. A cewarsa idan zamu gayawa kan mu gaskiya mun shiga wannan hali ne ba wai kawai don watsar da akidar Malam ba kawai, har da watsi da dokikin Allah. Wannan magana ce da ba kowane shugaba ba ne zai yarda da ita. Masu iya magana na cewa ita karya fure ta ke bata ‘ya’ya, don haka duk wani kyalkyal na fure da kamshinsa kar ya rude mu.

Daga
Zaharaddeen Ibrahim Kallah

Zaharaddeen Ibrahim Kallah marubuci ne cikin harshen Hausa da Turanci. A halin yanzu shi ne shugaban Kungiyar Marubuta ta Najeriya, reshen jihar Kano.