TA
ZAHARADDEEN IBRAHIM KALLAH
ZAHARADDEEN IBRAHIM KALLAH
1. Na yi godiya ga Jalla sarkin gaskiya,
Sarkin da babu kamarsa a duniya,
Mai sammai da qassai har da maliya.
2. Na yi tasbihi da sallama,
Gare shi Abban Fatima,
Xa ga Abdullahi kun jiya.
3. Na nufin nasiha ga ‘yan’uwa,
Qasidace mai gargaxi ga ‘yanuwa,
Mai hankali ya lura da duniya.
4. ‘Yan’uwa mu zubar da aikin qarya,
Mu lura mu kama hanyar gaskiya,
Mai hankali ya saurara ya jiya.
5. Wai me yake faruwa a qasar nan?
Kafin zuwan turawa qasar nan,
Mutanen mu akwai adalci da kunya.
6. Yayin zuwan turawa qasar nan,
Ya zo da sabon salo qasar nan,
Har ya zam to ba adalci a zuciya.
7. Ba ma manatawa a qasar nan,
Bautar da kakanni a qasar nan,
Wasu sun nakasa har suka bar duniya.
8. Mulkin mallakar a qasar mu ta Hausa,
Wasu ne sun ka sha vunqasa,
Wasu ko talauci, bauta, haraji kun jiya.
9. Haba mutane mu yi tunani,
Tsiya talauci yai tsanani,
Kowa ya sauya saboda duniya.
10. Mugunta da rashin adalci,
‘Yan’uwa babu zumunci,
Babu saura sai qeqasar zuciya.
11. Ta ya ya qasa za tai gaba,
Muddin ba mu sauyaba,
Don haka mu xau aniya.
12. Matsalar qasar nan ba qarama ba,
Shin su wanene suka haddasata?
Ban yi laifi ba in na ce ‘yan akuya.
13. Sun haxa makiirci a cikin qasa,
Sun haure kai sun bar qasa,
Har ya zamto babu mulkin gaskiya.
14. Abin mamaki a gidanka,
Jan Biri shi zai juyaka,
Ka zamto shafi-mu-lera ana ma dariya.
15. An daxe ana ruwa
Qasa na tsotsewa,
Mulkin mulukiya da danniya ya qi sauya.
16. An ce naka shi yake kar ka,
A gurin da babu wanda ya sanka,
Bare ace zai zamo miloniya.
17. Kura da shan duka,
Gardi da amshe kuxi duka,
Har ya washe baki don moriya.
18. ‘Yan tsaki suna kiwon su,
Aikin su shi ne su soyasu,
Su cinye har suna dariya.
19. Sun juya musu tunaninsu,
An sauya musu al’adarsu,
Har imani ya fita a zuciya.
20. Ka ji aikin na gwamna,
Na gwamma masu gidan rana,
Duniya ko shexaniya.
21. Shin wai me yake damun ‘yanuwa,
Iya yi shan alewa da kanwa,
Kowa burinsa ya tara dukiya.
22. Ta hanyar gaskiya,
Ko ta hanyar tsiya,
Cuwa-cuwa gami da danniya.
23. Arziki ne Allah yai mana,
Ina arzikin noma, sana’oin da yai mana,
Ina fetur, azurfa har zinariya.
24. Kanawa tambayata gareku?
Ina labarin dalar gyadarku,
Shin ko ta dilmiya?
25. Katsinawa Zage-zagi kuma zan zazzaga,
Ya aka yi da gero, masara har audunga,
Ko suma sun dulmiya.
26. Sakkwatawa kuma an kar ku,
Kun gudu kun bar ladanku,
Kun shiga wasoso da danniya.
27. Wannan shi ne jifar gafiyar vaidu,
An shiga wasoso an bar gandu,
Aikin noma an qiya.
28. Haxejawa har Gumalawa,
Suma sun ce sai turawa,
Barebari da Nufawa ma gaba xaya.
29. Burin turawa shi ne a rarraba,
Ta haka za su yi galaba,
Ko’ina ya zamto sai varavanbiya.
30. Sun dinga kwasar arzikin qasa,
Sun gina gadar zare,
Sun bar talakawa cikin tsiya.
31. Idan ka so ni in soka,
Idan ka qi ni in qi ka,
Amma mutanen mu “Ze dan kiya”
32. Yanzu dai an sha mu basilla,
Muna neman mafita ga Allah Ta’ala,
Shugannin mu su yi koyi da ambiya.
33. Mu gane su wane maqiyan mu,
Har mu san zuman mu,
Cikin yara da manya gaba xaya.
34. Mu tuna da kafin zuwan mu,
Akwai waxanda sun ka gabace mu,
Tun zamanin zamaniya.
35. Me suka tsira da shi anan duniya,
Babu komai sai ayyukansu a duniya,
Jallah ba ya buqatar dukiya.
36. Allah shi ne zamani,
Shi yake juya zamani,
Ka tsare mu sharrin shaixaniya.
37. Ka bamu shugabanni masu kishi,
Waxanda za su yi aiki da karsashi,
Ya zamto babu son zuciya.
38. Ni Zaharaddeen Ibrahim Kallah,
Nake roqo ga Allah,
Ya qara mana arziki da zaman lafiya.
39. Har ya zamto mun ciri tuta,
Qasa ta zamo babu sauran cuta,
Babu talauci da fariya.
40. Allah ka sada mu da alherinka,
Aljanna muke roqa gareka,
Ba don ayyukan ba na duniya.
2 ga Mayu, 2002