- Ya rabbana salli ala,
Muhammadun hairul ambiya.
- Nai godiya gun rabbana,
Sarkin da yai yi sammaniya.
- Shi ne ya sa so zuciya,
Har ma na so wata Gimbiya.
- Cikin dare ko safiya,
Ko ko cikin barci xaya.
- Ran haxuwa da sarauniya,
Rana ce ta ruxiya.
- Nai sallama qofar gida,
Ta fito kamar Hawainiya.
- Haske da qamshi yai gaba,
Fuska tana walainiya.
- Murmushinta na da kyau kwarai,
Balle idan ta yi dariya.
- Ta nuna so kuma zahiri,
Ta sacen dukkan zuciya.
- Hankali gare ta ‘yan uwa,
Ga tawakkali ga masoyiya.
- In ko tana zance na ta,
Tamkar a ce ‘yar masaniya.
- Tunanin wagga sahiba,
Ya zam kamar zinariya.
- Ilmi a gun ta sarauniya,
Al’amarin ba fariya.
- Kyawun diri na masoyiya,
Allahu yai wa Gimbiya.
- Tauraruwar mata ki ke,
Mai haskake mun zuciya.
- Muryarta na jan hankali,
Sanyinn idaniya Gimbiya.
- Ranar haxuwa da sahiba,
Ranar an sacen zuciya.
- Nai kira ga masoyiya,
Ta xago tana dubanniya.
- Murmushinta na jan hankali,
Na zam cikin ruxiya.
- Allah shi ya haxa mu a yau,
Ga ni ga ki ya sarauniya.
- Yau Magana ce ta gaskiya,
A bisa tafarkin gaskiya.
22. Haqiqa kin narkan zuciya,
Gavovi har ma jijiya.
- “Dalin” ka sacen zuciya,
Dare da rana bai daya.
- Begenka shi ke ja da ni,
Na zam kamar bebanniya.
- Amsarta kenan sahiba,
Wadda ke sa ni tunaniya.
- Inubi abar tsotsa garen,
Sheqi gareta da walqiya.
- Qamshi gareta Gimbiya,
Kamshi kamar na furanniya.
- Allahu roqo nai maka,
Ka ba ni sanyin zuciya.
- Nai godiya ga ilahina,
Ka sa mu riqe ta gaskiya.
- Kare mu shairin maqiya,
Masu son ganin mu tsiya-tsiya.
23 Ga Watan Afirilu, 2003.
© Zaharaddeen Ibrahim Kallah
No comments:
Post a Comment