GUZURIN MARUBUCIN WAQA[1]
DAGA
NASIRU G. AHMAD ‘YAN AWAKI
Gabatarwa
Duk inda na ji wani taro na ilmantuwa kan adabin Hausa irin wannan, musamman in zai tavo fannin waqa, lallaizan yi qoqarin ganin na halarce shi, ko da a gayyar soxi ne. Dalili na farko, saboda sha’awa da nake da ita kan adabin Hausa a dunqule, da fannin waqa musmman rubutacciya a kevance. Na biyu, saboda kasancewata xalibin adabi da ke kan bincike a adabin Hausa fannin waqa. Amma sai na tsinci kaina a matsayin wanda zai gabatar da takarda a wannan taro.
Na amsa wannan gayyata a matsayi biyu. Na farko, a matsayin xalibin adabi da zai bijiro da wani abu daga darussan da ya koya, don sanya shi a hanya in ya kuskure. Na biyu, a matsayin marubucin waqa. Amma fa ba wanda yak wan biyu kana bin ba, sai dai ko kwana xaya.
Na daxe da lura da cewa matasan marubutanmu na da sha’awar rubuta waqoqi, suna kuma yin bakin qoqarinsu wajen rubutawa da gabatarwa. Sai dai kash! Suna da buqatar sanin dokokin rubutacciyar waqa, da yadda ya kamata a shirya ta, don ta amsa sunan waqa rubutatta. Dalili ke nan a dandalin marubuta na wata-wata da wannan qungiya ke shiryawa, wanda aka yi cikin watan Janairun 2006, na gabatar da wata waqa mai suna “Sinadari” don ba da shawarwari ga masu son rubuta waqa, game da yadda ya dace a riqa tsara ta.
A wannan takarda, na yi qoqarin tattaro abubuwan da masana suka rubuta ne kan dabarun rubuta waqar Hausa, na yi xna gajeren sharhi tare da kawo misalai daga wasu waqoqin magabata a wuraren da ke buqatar hakan.
1. Ma’anar Waqa
Masana daban daban sun ba da ta’arifin waqa rubutacciya, wanda za mu iya cewa duk sun haxu kan cewa maganar hikima ce. Tsara ta ake yi. Ana zaven kalmomin da za a gina ta da su. Zance ne mai reruwa, kuma ya sava da magana ta yau da kullum. Ga kaxan daga cikinsu:
“Waqa, wani salo ne da aka gina shi kan tsararriyar qa’ida ta baiti, xango, rerawa, kari (bahari), amsa-amo (qafiya), da sauran qa’idojin da suka shafi daidaita kalmomi, zaven su da amfani da su cikin sigogin da b a lallai ne haka suke a maganar baka ba.” (Xangambo: 2007)
“Waqa ta bambanta da taxi na yau da kullum. Abu ce da ake shirya maganganu daki-daki cikin azanci da nuna qwarewar harshe. Harshen waqa cikakke ne, duk da yakan kauce wa wasu qa’idojin nahawu.” (Gusau: 2001)
“Rubutacciyar waqa ita ce wadda aka tsara, aka rubuta ta a takarda don a karanta.” (Sa’id: 1981)
“Waqa dai ita ce tsararriyar maganar hikima, da ta qunshi saqo cikin zavavvun kalmomi masu azanci, da aka auna don maganar ta reru, ba wai a iya faxar ta ba kawai.” (Yahaya, A.B: 2001)
“Rubutacciyar waqa wata hanya ce ta gabatar da wani saqo a cikin qayyadaddun kalmomi da aka zava, waxanda ake rerawa a kan kari da qafiya a cikin baitoci.” (Muktar: 2006)
“Waqa ta qunshi qololuwar hikima da tunanin xan Adam, ta yin amfani da qwayoyin muryoyi aunannu, cikin kalmomi zavavvu, waxanda ake jerantawa cikin tsari fitacce, qayyadadde, rattababbe, ta yadda za ta fa’idantar da abin nufi a taqaice, akasin zance, ko hira, ko labari, ko magana wadda take kara-zube.” (Yahaya, I.Y: 1985)
2. Amfanin Waqa
Game da amfanin waqa ma, na ga ba abin da ya fi illa na bar mu da Farfesa Xandatti Abdulqadir a gabatarwar xaya daga cikin littattafansa. Ga abin da ya ce:
“Ta hanyar waqa za a iya gane halayen mutane, da al’adunsu, da xabi’unsu na da da na yanzu. Har ma wani lokaci takan bayyana yanayin wuri da tarihinsa, da abincin mutanen wurin, da arziqinsu, da sana’o’insu, da koguna, da ma’adinai. Ka ga waqa ta zama madubin da ake leqawa a ga abubuwan da suka faru, ko ma waxanda suke faruwa a cikin al’umma.
“Har ila yau, waqa tana taimakawa wajen bunqasa harshe da raya shi, saboda sauqin shiga kai da faranta zuciyar mai sauraron ta. Bugu da qari, waqa takan kare harshe daga gurvacewa. Ta hanyar waqa ne zalaqa da fasaha da hikimar Hausa suke bayyana. Kuma ta nan ne ake koyon tatattar Hausa, domin yawaicin mawaqa gwanaye ne wajen sarrafa harshen Hausa, musamman da yake sai sun zavi kalmimin da za su yi amfani da su. Ta duban waxannan abubuwa ne za a tabbatar da cewa, ashe amfanin waqa ya shige a ce wai don rerawa kawai.” (Abdulqadir: 1979 :10)
3. Marubucin Waqa
Masana sun bayyana marubucin waqa da cewa ma’abocin xayan wasu halaye uku ne. Halayen su ne:
3.1 Jibiliyya
Wato xabi’a da akan halicci mutum da ita. Akwai mutanen da tsara waqa a xabi’arsu take. Sukan ji waqa na zuwar musu kamar wahayi ko wata ilhama, a duk sa’ad da suka buqace ta. Wani sa’in ma haka kawai za su ji tana zuwar musu.
3.2 Koyo
Wasu mutanen kan zamo marubuta waqa ne sakamakon zama da mawaqa da yin hulxa da su, musamman wadda ta shafi harkar waqa. Ta haka sukan laqanci hanyoyi da dabarun rubuta waqar, har su ma su kai ga rubuta nasu waqoqin, ko su zamo qwararrun masu ba da shawarwari kan waqa.
3.3 Larurar Rayuwa
Wasu mutanen kan zamo marubuta waqoqi ne sakamakon wani matsanancin halin rayuwa da suka shiga, wanda ya yi matuqar sosa musu zuciya, suka yi qoqarin fito da wannan abu da ke damun su. Sai su tsinci kansu ga yin waqa kan wannan abu. Daga nan kuma su xore da rubuta waqoqi kan sauran fannonin rayuwa.
4. Sigogin Waqa
A nan ina son jero wasu siffofin rubutacciyar waqa ne da ta kevantu da su, waxanda suke bambanta ta da magana ta yau da kullum, har ma da waqar baka wadda ba rubutacciya ba, waxanda ya kamata marubucin waqa ya riqa lura da su a duk sa’ad da ya tashi rubuta waqa.
4.1 Ma’auni/Kari
Ana so rubutacciyar waqa ta zamo an gina ta bisa wani Karin murya da aka shirya kalmominta kansu, yadda ba za su gaza yawan gavovin wannan ayyanannen kari ba ko su zarta shi, cikin dukkan baitocin waqar. Karin rubutacciyar waqar Hausa kan iya zamowa xaya daga cikin ma’aunan waqoqin Larabci da akan aro a gina waqoqin Hausa kansu, ko kuma wani kari daban da mai rubuta waqa ya zava, kamar na waqoqin makaxa, waqoqin gaxa, na tatsuniyoyi, na tashe, da makamantansu. Idan waqa ta aunu bisa Karin da aka gina ta kansa, to wanin marubucin waqar zai iya rera ta, ko da bai ji ta daga bakin mawaqin ba.
4.2 Xango
Xango na nufin saxara ko layi guda na rubutacciyar waqa. Sau da yawa xangon waqa shi kaxai kan ba da ma’ana cikakkiya, ba tare da dogaro da wanda ke gabaninsa ko bayansa ba. Misali:
Ximuwa ta same ni na ruxe,
Na yi tunani in zana zancen ta.
(Waqar “Mairi” ta Halliru Wuno)
4.3 Baiti
Xangogi su ne ke haxuwa sub a da baitin rubutacciyar waqa. Baiti kan zo cikin tsarin gunduwoyi (layuka). Gunduwa guda ita ake kira “xango.”
Nau’o’in Baiti
Ana so tsarin baitocin rubutcciyar waqa ya zamo xayan waxannan nau’o’i:
i- Gwauruwa
Ita ce waqa mai xango xai xai a kowane baiti nata. Misali:
Alhamdu lillahi mun samo fita haxari.
Wancena jan zamani da ke sa maza waxari.
Jama’a musulmi ku ce amin mu zam shukuri.
(Waqar “Addakari” ta Sa’adu Zungur)
ii- ‘Yar Tagwai
Ko “Mai Qwar biyu.” Ita ce waqar da ke da xango bi-biyu a kowane baiti. Misali:
Na so ka Xaha kamar ido ga makauniya,
Na so in je ni gare ka ko da sau xaya.
Na so ziyara ga ni ba ni da fiffike,
Qaqa nikai in gano masoyin zuciya?
(Waqar “Begen Muhammadu” ta Sheikh Nasiru Kabara)
iii- Mai Qwar Uku
Wato waqa mai xango uku-uku a kowane baiti nata. Misali:
Da safe jikina idan nai sitati,
Bikina idonki shi yi mini saiti,
Zama a loton nikan samu haiba.
(Waqar “Hikayar Zuciya” ta A.B. Yahaya)
iv- Mai Qwar Huxu
Ita ce waqa mai xango hurhuxu a kowane baiti. Misali:
Ga abin da hali yak kawo,
An yi dauri yau kuma ya dawo,
Na qudurta buri na sawo,
Rabbana nufe ni da dacewa.
(Wazirin Gwandu Umaru Nassarawa)
v- Mai Qwar Biyar
Wato waqa mai xango biyar-biyar a kowane baiti nata. Misali:
Ga ruwa gulbi ban zuwa tafki,
Ga akwatina ban bixar taiki,
Ga masallaci ban bixar gunki,
Ba ni cin gwaza ga su alkaki,
Tela riga tun bara nib ba ka.
(Waqa Amre ta Halliru Wurno)
vi- Tahmisi
Kalmar “Tahmisi” na nufin biyartawa. Wato waqa ce mai qwar biyu da wani mawaqi ya rubuta. Daga baya sai wani mawaqin daban ya qara xango uku-uku a kowane baiti nata, ta zama mai xango biyar-biyar. Kamar waqar “Arewa Mulukiya ko Jamhuriya” ta Sa’adu Zungur, wadda Yusufu Kantu Isa ya yi wa tahmisi, da “Waqar zuwa birnin Kano” ta Malam Yahaya Gusau, wadda Bello Gixaxawa ya yi wa tahmisi. Misali:
Ina gode Allah da yai qaddara,
Ya sanya niz zo ni birnin Kano.
(Yahaya Gusau)
Ina yin wasiqa zuwa mai basira,
Ina gai da shi gaisuwa mai ibara,
Ina so in samu dukan sutura,
Ina gode Allah da yai qaddara,
Ya sanya niz zo ni birnin Kano.
(Bello Gixaxawa)
vii- Tarbi’i
Tarbi’i na nufin huxuntawa. Kamar tahmisi ne, sai dai a nan bayan mawaqi na farko ya yi waqarsa bisa xango bi-biyu, sai mawaqi na biyu ya qara wasu xango bi-biyun a kowane baiti, ta zamo mai xango hurhuxu. Kamar waqar Isa xan Shehu wadda Muhammad Awwal ya yi wa Tarbi’i. Misali:
‘Yan musulmi kui mana hanzari,
A mu zam ka yabo gun Gafiri,
A mu gode baxini zahiri,
Jama’ag ga Karimi Qadiri.
4.4 Amsa-amo (Qafiya)
Amsa-amo shi ne dacewar sautin gavar qarshen kowane baiti na waqa. Dukkan manazarta sun haxu kan cewa rubutacciyar waqa ce kaxai ke da amsa-amon baqi, wanda ta aro daga waqoqin Larabci.
Ire-iren Amsa-amo
i. Babban Amsa-amo (Na waje)
Shi ne wanda kowane baitin waqa ke qarewa da shi. Misali
Aikin tiyata masu ilmu suke yi,
Mai hattara shi ne da qulla abawa.
Ba za ka zamto malamin ofis ba,
Sai mai yawan ilimi yake aikawa.
(Waqar “Kadaura babbar inuwa” ta Aqilu Aliyu)
ii. Qaramin Amsa-amo (Na ciki)
Ana samun qaramin amsa-amo ne a waqar da ke da xango (layi) uku zuwa sama a kowane baiti. Misali:
Ga yawan kwanci ba ta son aiki,
Ban da ci kullum sai ka ce doki,
Ga guwayyunta kama da Tankarki,
Ga dufun rai ga kissa gun aiki,
Gun baqin rai ba mace tamkatta.
(“Waqar Amre” ta Halliru Wurno)
iii. Amsa-amon Farawa
Shi ma akan same shi ne a waqa mai fiye da xango biyu a baitukanta. Kuma iri biyu ne:
- Kalmar farko za ta fara da harafi iri xaya a kowane layi mai amsa amon ciki. Misali, waqar da ke qarshen wannan takarda.
- Wannan kuwa harafinfarko ne na xangon baiti kan farad a shi, ya kuma qare da shi, sannan a gina babban amsa-amo da shi. Misali:
Kafilun ishi bayinka,
Ka ishe ni da girmanka,
Ka faxi nakiraye ka,
Ka ji na faxi sunanka,
Kai da kaya duk naka.
(Waqar “Daren Babbar Salla” ta Aqilu Aliyu)
iv. Amsa-amon Karin Sauti
Shi ne dacewar Karin sautin kalmomin qarshe na baitocin waqa. Ana samun sa cikin kowane nau’ina waqar; rubutacciya da ta baka. Misali:
Ina wani in ba ilmu ba,
Da in lamari ya dagule.
Ya kwakkwave ya davalvale,
Yana neman ya jagwalgwale.
(Waqar “Qalubale” ta Aqilu Aliyu)
4.5 Jigon Waqa
Jigon waqa shi ne manufarta. Wato babban saqon da marubuci ke son isarwa, wanda shi ne dalilin rubuta waqar. Ana so mawaqi ya gabatar da babbar manufar rubuta waqarsa a baitukan farko, bayan sallama ko addu’ar buxewa. Misali:
Na sake komowa a wannan shekara,
Gun alhazanmu na nan Kano baki xaya.
Ya alhazai yau na iso don sallama,
Kuma zan yiwo saqo gare ku gaba xaya.
(Waqar “Bankwana da alhazai na 1961” ta Mudi Sipikin)
4.6 Wargarar Jigo
Bayan mawaqi ya gabatar da jigon waqarsa, sai kuma ya shiga bayani filla-filla kan wannan batu da yake son isarwa ga jama’a. A nan akan samu qananan jigogi masu alaqa da babban jigon waqa, waxanda su ne ke harhaxuwa su tashi babban jigon. Misali, waqar da aka shirya kan “Dashen Itatuwa,” tana iya qunsar qananan jigogi irin su bayani kan Hamada da haxarinta, illar sare itatuwa barkatai, amfanonin da wadatar itatuwa ke kawowa, da makamantansu.
4.7 Sunan Mawaqi da Tarihin Rubuta Waqa
Ana so marubucin waqa ya ambaci sunansa a qarshen waqarsa, da tarihin lokacin da ya rubuta ta, don taimaka wa masu nazari wajen tantance wanda ya yi waqar, da sauqin alaqanta irin abubuwan da ya faxa a cikin waqar da zamanin da aka yi ta. Rashin irin wannan bayani cikin waqa ne ya sa manazarta suka sha fama da matsanancin bincike yayin tantance mawallafan wasu rubutattun waqoqin Hausa na dauri, irin su “Waqar Yaqin Badar” ta Wali xan Masani, da waqar “Gangar Wa’azu” ta Malam Muhammadu na Birnin Gwari, da ire-irensu.
4.8 Amfani da harshe
Shi ne yadda marubucin waqa ya sarrafa kalmomi wajen isar da saqonsa. Abin so ne marubucin waqa ya yi amfani da kalmomi masu qarfi da kama jiki da ratsa tunani cikin waqarsa. Amma kada hakan ya kai shi ga kallafa wa kansa zuwa da abin da bai zamo dole ba, ko amfani da kalmomin da za su wahalar da mai karatu ko sauraro wajen fahimtar saqon waqar. Marubucin waqa na iya sanya adon harshe da gishirin zance don qawata waqarsa. Wato kamar amfani da Karin magana, da salon magana, da irin su muqabala (kawo abu da kishiyarsa), da salon tambaya da amsa, da sauran irinsu. Sannan marubucin waqa na iya yin qara ko ragi a jikin kalma.
5. Ingancin Waqa
Akwai wasu abubuwa waxanda samun su a waqa ke qara mata kyau da armashi, yadda za ta amsa sunanta. Rashinsu kuma kan naqasta waqa, ya rage mata qima da daraja. Ga wasu daga ciki:
i- Sulluvewar Harshe
Yana nufin karantuwar waqa tar-tar daga bakin mawaqi ba tare da in-ina ba, ko jan murya fiye da qima, ko wucewar sauri ga wasu kalmomi, a qoqarinsa na tafiyar da karin waqar.
ii- Daidaiton Amsa-amo
Wato qafiyar waqar. Ma’ana gavovin kowane baiti su zamo da harafi iri xaya babu savawa, har zuwa qarshen waqar. Idan baitocin masu xango fiye da biyu ne, to amsa-amon ciki na kowane baiti su daidaita, amma ba lallai su zamo iri xaya a kowane baiti ba. Babban amsa-amo (na waje) kuwa, lallai ya zamo iri xaya a qarshen kowane baiti, har zuwa qarshen waqar.
iii- Tsayayyun Baitoci.
Abin nufi shi ne adadin xangwayen kowane baiti na waqa su daidaitu, ba tare da savawar yawansu a wani baiti ba. Irin wannan baiti ne akan kira “Taqadarin baiti” wato wanda ya sava da ‘yan uwansa.
iv- Xango ya cika Ma’anarsa
Wato shi kaxai in aka karanta shi, ya zamo zai iya ba da cikakkiyar ma’ana, ba tare da ya ratayu da magabacinsa ko mabiyinsa ba. Na ba da misalin irin wannan a baya wajen bayanin xango (shafi na uku / 4.2).
v- Gaskiya daga Mawaqi
Ana nufin abubuwan da mawaqi ya faxa ya zamo daga cikin zuciyarsa suka fito. Wato abin da ke xamfare cikin zuciyarsa ne ya fito da shi. Marigayi Farfesa Aliyu Na’ibi Suwaid, a wani littafinsa “Kaifa natazawwaq Al-Adab Al-Arabiy” ya bayyana waqa da cewa “Wani zance ne aunanne, mai amsa-amo, da ya dace da abin da ke cikin zuciyar mawaqi.”
vi- Ta zamo mai Reruwa
Rerawa na daga cikin muhimman abubuwan da ke bambanta waqa da magana ta yau da kullum. Ana so rubutacciyar waqa ta zamo wadda za a iya rera ta. Ba ga mawaqin kaxai ba, so ake duk wanda ya dube ta a rubuce, ya zamo zai iya rera ta, ba kuwa lallai da irin Karin da marubucin zai rera ta ba. Ba abin da zai ba waqa wannan matsayi kuwa sai daidaituwar kalmominta bisa ma’aunin da aka xora ta kansa.
vii- Samun Kalmomin Fannu
Kalmomin fannu ko dangantakakkun kalmomi, su ne kalmomi masu alaqa da babban jigon waqa. Misali, a waqar da ke Magana kan ilimi, za a so a sami kalmomi irin su Jahilci, Makaranta, Karatu, Xalibi/xalibta, Malami, Jarrabawa, da makamantansu.
6. Abubuwan da ke Vata Waqa
Akwai kuma wasu abubuwa waxanda samun su cikin rubutacciyar waqa kan tauye mata daraja da qima da kwarjini, idan ma suka yi yawa su vata waqar baki xaya, ta kasa amsa sunan rubutacciyar waqa. Abubuwan sun haxa da:
1. Maimaita Kalma
Wannan na nufin yawan maimaita wata kalma ko wasu kalmomi cikin waqa, musamman a qarshen baitukanta (amsa-amo), ba tare da wata manufa ta musamman ba. Idan aka yi amsa-amo da wata kalma, to in so samu ne kada a sake samun irinta sai bayan aqalla baiti shida. Amma idan da wata ma’anar ne ba irin ta farko ba, wannan wani qarin armashi ne ga waqar. Misali, goge (shafe), goge (sunan abin kixa), goge (qwarewa), ds.
2. Rashin Amsa-amo ko Daidaituwarsa
Samun amsa-amo (qafiya) cikin rubutacciyar waqa na daga muhimman abubuwan da ke bambanta ta da waqar baka. Rashin samun sa ko daidaituwarsa cikin baitukan waqa ba tare da wata manufa ta musamman ba yana vata waqa, har ta nemi fita daga sahun rubutattun waqoqi zuwa na waqoqin baka.
3. Amfani da Kalma a Wurin da bai Dace ba
Sau da yawa irin wannan na furuwa ne yayin neman kalmar da za ta dace da qafiyar waqa ko daidaituwar awonta. Sakamakon haka sai ka ga ma’anar waqar na neman bauxewa, saqonta ya kasa fita kamar yadda ya kamata.
4. Karyewar Karin Waqa ko Qaruwarsa
Karyewar kari na nufin gazawar yawan gavovin kalmomin da aka zuba wa xangon waqa ga ma’aunin da ake rubuta waqar kansa. Qaruwar kari kuwa shi ne zuba kalmomi su zarta adadin gavovin da ake buqata a ma’aunin (Karin) waqar. Sakamakon haka sai ka ji mawaqi na jan muryarsa don cike gurbin gavovin da babu (karyewar kari), ko ka ji yana yi wa wasu kalmomi shigar sauri sakamakon qaruwa da gavovin da awon ke buqata suka yi.
Naxewa
Wannan takarda ta duba ma’anar rubutacciyar waqar Hausa da amfaninta, da yadda marubucin waqa kan samu. Ta xan faxaxa bayani kan sigogin waqa. Sai bayanin abubuwan da kan qara mata inganci da waxanda ke vata ta.
Abin nufi shi ne ba da haske ga matasan marubutanmu da ke da sha’awar rubuta waqoqi, don laqantar muhimman abubuwan da akan yi la’akari da su yayin rubuta waqa, don su ma su ba da tasu gudummawar a wannan babban fanni na adabin Husa.
Ina miqa gwaggwavar godiya ga shugabannin reshen jihar Kano na qungiyar marubuta ta qasa, bisa ba ni wannan dama don ba da tawa ‘yar gudummawa a wannan taro, duk da rashin kasancewata ahali ga abin. Wassalamu alaikum.
Rataye
WAQAR SINADARI
Daga
Nasiru G. Ahmad ‘Yan awaki
1. Bi hamdi Allah nai godiya, Bisa ga baiwa da shiriya,
Bixar daxi zan Ilahiya, Bi jahi Sidi na Mariya,
Bin sa tafarki na gaskiya.
2. Yau wata waqa na shirya yi, Yadda ya dace mutum ya yi,
Ya tsara waqa ya kyauta yi, Ya rera waqar ba laulayi,
Ya miqa saqonnin da ya yi.
3. Abu na farko ce sha'awa, Akanta waqar za ka yi wa,
Abin da duk ba ka sha'awa, Ai in ka yi shi bai kyautuwa,
A zam kulawa ya 'yan uwa.
4. Karanta waqoqin na gaba, Ka rinqa ji ba ka bar su ba,
Ka san salalensu 'yan gaba, Kari dabaru ba wanke ba,
Ka zam cira babu fargaba.
5. Sam shi rubutu bai samuwa, Sai an karatu da qaruwa,
Sanin dabaru na daxuwa, Sai ka ga an kai ga goguwa,
Samun ya kai na wahaltuwa.
6. Ta fari waqar da za ka yo, Ta bin kari za ka kwaikwayo,
Ta wata waqa da anka yo, Ta ba ka shawa to sai ka yo,
Ta bin awonta za ka biyo.
7. Batun da ka zamto da sani, Ba wanda zai ba ka tsanani,
Ba kansa za kai ta bayyani, Ba mai tsayi sai ka zam gani,
Baitinka ba za sui laulayi.
8. Waqa daban zance ko daban, Wajen awo waqa ta yi ban,
Wancan ba a yin sa da awan, Wato kari ne awo ku san,
Wanda shirin waqa ke bixan.
9. Ka zavi kalmomi kan ka sa, Ka xora kalmomin a bisa,
Kari na waqar kar ka gusa, Kan yai yawa zance ne ka sa,
Kan yai kaxan ta yi naqqasa.
10. Amsa-amo kan ce qafiya, A can gavar qarshe kan biya,
A dukka baiti ya zam xaya, Alal misali "Wa" ko ko "Ya" Amma ka zam yin tunaniya.
11. Daxi a kalma kana iya, Da yin ragi ma halaliya,
Don auna baiti yai bai xaya, Da tsai da sauti na qafiya, "Dashe" ya zamto shi "Dashiya."
12. Har keta dokar nahawu ma, Halal ga mai waqar hikima,
Haure idan ta yi gardama, Haka gidaden qudan zuma,
Har qatuna sun yi rigima.
13. Kalma daxaxxu ka bincika, Ka sa a waqar ya fi maka,
Ka adana yadda an maka, Ka ga na bai sa qaru da ka,
Ka taimaka wa harshe naka.
14. Ba wai fa kalmomin zamani, Ba a saka su ko qanqani,
Banda yawaita su ka sani, Ba takalifi ko tsanani,
Bixo sawaba tsakankani.
15. Idan adon zance za ya hau, Idan ka sa waqar ta yi kyau,
Idan da shi sai ka ji ta rau, Idan awon ko ba za shi xau,
Idan ka sa za ta rasa kyau.
16. Laifi ba zai zam gare ka ba, Lanqaya kalma ba tamu ba,
Larabci Turanci Yaruba, Lallai kaxan ba tulinsu ba,
"La ba'asa" ba za a qi ba.
17. Waqa idan har ta aunu ta, Waninka zai rera maka ta,
Wajen kari ba shi quntata, Wani daban zai iyai mata,
Wanda ya zam ba shi kai mata.
18. Mai tsara waqa mutum yake, Mai nazarin halin da ake,
Mai tsokaci shawara yake, Mai hanga nesa da bincike,
Mai tsawatar varna da ake.
19. Ka zam madubi na al'uma, Ka zam kira don yin azama,
Kai faxakarwa da hikima, Ka zam haxawa da kanka ma,
Ka qaurace hanyar rigima.
20. Waqa fa baiwa ce mayyawa, Wadda Tabara kai ya yi wa,
Wato a nan ba shi kyautuwa, Wani ka zaga zambatuwa,
Wani yabo nai ka zarmuwa.
21. Shi fa rubutu in ka yi shi, Shi ma hisabi za ai mashi,
Shina da kyau ko ko babu shi, Shina cikin ayyukanka shi,
Shiri na amsa mu zam da shi.
22. A nan nake so za na tsaya, Allah ya qare mu lafiya,
Abinci har ma yawan xiya, Albarkacin Manzon shiriya,
A kowashe ya Ilahiya.
23. Mai tsara waqarku Nasiru, Mai amsa G. Ahmad sha'iru,
Mai son ya zamto shi mahiru, Mai yin fito gefen baharu,
Mai xan sani fannin shi'iru.
24. Baiti huxu sau shida na yi, Bayar da haske kawai na yi,
Babba da yaro mai son ya yi, Ba wahala waqa maza yi,
Ba don makoyi ya za a yi?
Alhamdu Lillahi
Manazarta
Abdulqadir, X. (1976), The Role of Hausa Poet A cikin Harsunan
Nijeriya VI, CSNL, B.U.K
Abdulqadir, X. (1979), Zavavvun Waqoqin da da na Yanzu, Lagos:
Thomas Nelson (Nig.) Limited
Ahmad, S.A. (2005), Mata a Idon Marubuta Waqoqin Hausa, Kundin
neman digirin farko, Jami’ar Usmanu Xanfodiyo, Sokoto.
Aliyu, A.A. (1978), Fasaha Aqiliya, Zaria: N.N.P.C.
C.N.H.N. (1977), Waqa a Bakin Mai Ita I, Zaria: N.N.P.C.
C.N.H.N. (1979), Waqa a Bakin Mai Ita II, Zaria: N.N.P.C.
Xangambo, A. (2007), Xaurayar Gadon Fexe Waqa, Zaria: Amana
Publisher Limited
Gixaxawa, B. (2006), Bargon Hikima, Sokoto: Usmanu Xanfodiyo
University Press
Gusau, S.M. (2001), Tsakure Kan Sanabe-sanaben Rubuta da Nazarin
Rubutattun Waqoqi na Hausa, Takarda da ya gabatar a taron sanin makamar
aiki don marubuta a harsunan Nijeriya, wanda qungiyar marubutu ta Nijeriya
ta shirya, a Rock Castle Hotel Tiga, Kano, 20-24/3/2001
Ibrahim, M.S. (1982), Rubutattun Waqoqin Hausa Kafin Zamanin Shehu
Usman Xanfodio. A cikin Harsunan Nijeriya XII, C.S.N.L., B.U.K.
Muhammad, X. (1979), Interaction between the Oral and the Literate
Traditions of Hausa Poetry. A cikin Harsunan Nijeriya IX, Kano:
C.N.H.N., Jami’ar Bayero Kano
Mukhtar, I. (2006), Gudummawar Rubutattun Waqoqin Hausa wajen
Adana Tarihin Siyasar Nijeriya, A cikin Algaita, Vol. I No 4, Sept. 2006
Sa’id, B. (1978), Salo da Tsarin Rubutacciyar Waqar Hausa ta Qarni na Goma
sha Tara. A cikin Studies in Hausa Language, Literature and Culture I, Kano:
C.S.N.L., B.U.K.
Sa’id, B. (1981), Bambancin Waqar Hausa ta Baka da Rubutacciya, A
cikin, Studies in Hausa Language, Literature and Culture II, Kano:
C.S.N.L., B.U.K.
Wurma, A.G. (1999), Waqa Rubutacciya: Muhimman Hanyoyin Nazarin
ta da Abubuwan da ke Vata ta. A cikin Jakadiya: A Journal of
Research in African Languages and Literature, Vol. I, No I, March
1999, Zaria: Dept. of Nigerian and African Languages, A.B.U.
Yahaya, A.B. (2001), Dangantakar Waqa da Tarbiyyar ‘Ya’yan Hausawa.
A cikin Harsunan Nijeriya XIX, Kano: C.S.N.L., B.U.K.
Yahaya, I.Y. (1985), Tarihin Rayuwa da Havakar Rubutattun Waqoqi a
Qasar Hausa, A cikin littafin “Dandalin Hikima” na qungiyar
marubuta da manazarta waqoqin Hausa ta Nijeriya, 1985.
[1] Takarda da aka gabatar a taron sanin makamar aiki da reshin jihar Kano na qungiyar marubuta ta Nijeriya ya shirya, a ran 1ga Janairu, 2012 a xakin karatu na Murtala Muhammad, Kano.
No comments:
Post a Comment