Daga Sa'adatu Baba Ahmad Leadership Hausa
31/01/2014
Hira da Marubuci Zaharaddeen Ibrahim Kallah tare da Sharhin Littafinsa Sadauki Mai Duniya....
Ya ya sunanka?
Suna na Zaharaddeen Ibrahim Kallah
Kadan daga cikin tarihin ka?
An haife ni a unguwar Fagge da ke Kano, na yi makarantar firamare na a
makarantar firamare ta Giginyu wanda daga nan kuma na koma firamare ta
Race Course da ke filin sukuwa a Kano. Bayan nan na wuce makarantar
sakandire ta Stadium don yin karatuna na gaba da firamare. Da na qare ne
sai na je kwalegin share fagen shiga jami’a ta CAS, Kano. Daga nan ne
na samu shiga jami’ar Bayero da ke Kano in da na yi digiri na karanci
abin da ya shafi ilimin zamantakewar xan adam tare da siyasa
(Sociology/Political Science). Na yi hidimar qasa ta a jihar Kwara wanda
na koyar a wata sakandire da ke Patigi. Bayan nan na fara aiki da NGO
na wani lokaci kafin na koma Jami’ar Bayero da aiki. A Bayero na koma na
yi digiri na biyu a vangaren karatun ci gaban duniya wato (Development
Studies).
Wacce shekara ka fara rubutu?
Na fara rubutu a
shekara ta 1995 bayan na qare sakandire, xan zaman da na yi kafin na
cigaba da makaranta na ga ya dace na fara rubutu.
Wacce shekara ka fara wallafa littafi?
Kafin fara buga littafi na rubutu na ya fito ne a littattafai na
gamayya na turanci a wajen 2002, littafin Hausa kuma sai a 2006
littafina “Ciki Da Gaskiya” da muka yi qarqashin hukumar A Daidaita Sahu
ya fito.
A matsayinka na marubucin Hausa da turanci, wanne rubutune ya fi ma sauki da ba ka sha'awa a cikinsu?
A matsayina na Bahaushe babu rubutun da ya fi mun sauqi kamar rubutu da
Hausa, a cikinsa ne na fara rubutu da kuma shi ne na buxi ido. Tun a
firamare a lokacin ina Monita na kan karantawa ‘yan ajina Littattafai
irinsu “Ilya Xan Mai Qarfi”da “Magana Jari Ce”.
Zuwa yanzu me ka fahimta game da salo da harshe?
Salo na nufin tsari na rubutu da marubuci ya yi amfani da shi wajen
isar da saqonsa. Salon da ake amfani da shi ya danganta da marubuci,
wani kan yi amfani da salo mai sa karsashi da jan hankali, wani kuma kan
yi amfani da salo mai wahalar da mai karatunsa.
Harshe hanya ce ta
isar da saqonni, wanda ta qunshi kalmomi da suke bada ma’ana. Marubuci
na amfani da harshe don isar da saqonsa ga jama’a wanda ya qunshi tunani
da falsafa.
Wadanne marubuta ne gwanayenka a marubutan Hausa?
A vangaren rubutun Hausa ina da gwanaye kamar su Bala Anas Babinlata da
Nazir Adam Saleh da Ibrahim Sheme da Bature Gagare da Yusuf M. Adamu
A marubutan turanci fa?
A Turanci akwai Sidney Sheldon da Abubakar Gimba da James Hadley.
Littafinka Sadauki Mai Duniya ya bambamta da littattafan wannan zamanin, menene sirrin?
Littafin Sadauki Mai Duniya labari ne da ya waiwayi shekaru sama da
xari biyu baya a lokacin da ake yaqe-yaqe a qasar Hausa. Kafin na fitar
da littafin sai da na nazarci salo daban-daban musamman littattafai
tsofaffi da suka kawo tarihi da adabi na shekaru aru-aru. Da wannan ne
na yi qoqarin fitar da littafin Sadauki Mai Duniya.
Wacce kungiya ka ke ciki?
Ina cikin Qungiyar Marubuta ta Najeriya (ANA) reshen jihar Kano, a
halin yanzu ni ne Magatakardarta. Sannan ina cikin wasu qungiyoyi da
dama waxanda ba na marubuta ba, waxanda suka haxa da na cigaban alumma.
Sharhin Littafin Sadauki mai duniya....
Sadauki mai Duniya Littafin da ya kere sa'a.
marubuci Zaharaddeen Ibrahim Kalla.
Shekarar bugu-2010
Jigon labari- Jarumta
Yawan shafuka- 150
Bugawa da yadawa- madaba'ar iya ruwa Zaria Road, Kano Nigeria.
ISBN- 987-987-087-880-3
Rabona da karanta wani labari na jarumta wanda har na ke ganin
jarumtakar ta kai Sadaukantaka tun wani Fim da na gani na shekaru dari
uku na Sarki Liyonaidas na kasar Sparta wanda ya fuskanci barazanar
murkushewa idan har k'asarsa ba ta yi mubaya'a ba ga Sarkin Zaksia ba
Azskiz wanda azzalumin shugaba ne da babu Sarki mai karfinsa a duk
duniya a kuma zamaninsa. Sun yi jayayya da Liyonaidas in da ya gaza
zubda Liyonaidas wajen kare martaba da 'yancin k'asarsa. Sun gwabza yaki
ga juna amma jarumta ta hana Liyonaidas ya yi hakuri ya janye duk da
kuwa Sarki Azskiz ya fi shi karfi tare da jama'a. A karshe dai an kashe
Sarki Liyonaidas da dubban masu da kibbau amma wajibi ne a jinjinawa
jarumtarsa da gwarzantakarsa.
A lokacin da na ke karatun littafin
Sadauki mai duniya na yi ta kamanta jarumtar Usman mai duniya da Sarki
Liyonaidas yadda a 'yan shekarunsa na kuruciya ya shiga daji ya kashe
Karen ruwa shi ma Usman mai duniya 'yan shekarunsa na kuruciya ya shiga
daji ya kashe Goggon biri.
Sadauki Mai Duniya
Wannan littafi ya
kunshi labarin wasu masarautu guda biyu masarautar Kwairanga wacce ke
karkakashin mulkin sarki Haruna wanda ke gudanar da mulkinsa cikin
jarumta da adalci da tausayin talakawa. Yayin da daya masarautar Damanga
wacce Sarki Sakimu ya ke gudanar da mulkinta cike da zalunci da izza,
ya maida rayukan talakawansa tamkar na fari saboda kisan kai da mugunta,
sannan duk wani mikirci tare da kulla salon dabarun yaki ya iya, Sarki
Sakimu na da dabi'ar bakin ciki a duk lokacin da ya ji labarin kasar da
arzikinta ya kafu ko kasar da ta shahara a fagen yaki ya kan so ya
yaketa ta dawo karkashin mulkinsa ko ta wacce hanya ne.
Lokacin da
Sarki Sakimu ya ji labarin masarautar Kwairanga ya yi tunani ya ga ba
zai iya yakarta ba sai ya shirya makirci ya tura wasu kyawawan mata
wadanda kyaunsu ya kai kyau su ka je fada a zuwan 'yan gudun hijirar
yaki wanda su ka ce Damangawa sun kashe iyayensu da mazajensu, a taimake
su da wurin zama. Sarki Haruna Kabir dai zuciyarsa ba ta kwanta da
lamarin ba saboda ya gansu tsaf-tsaf ba wahala ko gajiyar tafiya a
tattare da su amma 'yan majalisarsa su ka nuna ba wani abu. Matan nan su
kai nasarar mamaye gidajen sarakan Kwairanga in da a karshe su ka kare
musu kallon sirri a ranar wani biki na al'ada da Kwairanga ke gudanarwa
duk shekara a ka turo maza mayaka daga Damanga, ' yanmata sukashayar da
sarakai giyasu bayan sun sha sun bugu su ka hadu su ka cinyesu da yaki
da rana tsaka, su ka karkashe mutane su ka nufi fada wajen Sarki, in da
ya nuna jarumtarsa a shafi na 9 ' Maharan Damanga su ka yi ca kan Sarki
Haruna, shi kuwa gogan naka ko in kula sai faman kirari ya ke yana cewa
"Sai ni dan mutan Kwairanga kadangaren bakin tulu, a kar ka a kar tulu a
bar ka ka bata ruwa, ruwan dare dama duniya na kwairanga sai dubu ta
taru, ai kuwa nan da nan suka taru a kansa su ka kame Sarki Haruna Kabir
su ka tafi da shi garinsu su ka daure, cikin matansa kuwa akwai wata da
a ke kira Hassana wacce ta haye doki ta kubuta ta gudu tare da goyon
danta Usman, 'yar Wani sarki sadauki jarumin gaske ne a wata kasa da a
ke kira Yammaniya. Bayan ta sanar da mahaifinta yadda a ka tarwatsa
kasar maigidanta Sarki Haruna, sai ya jajanta lamarin kuma ya dauki
aniyar horar da Usmanu don ya daukarwa mahaifinsa fansar abinda a ka yi
masa.
Sarki Haruna kuwa ya na daure a can wani kurkukun karkashin
kasa a kasar Damanga in da ya shafe shekaru cikin wahala da azabtarwa
iri-iri, yayin da kuma Zubaida daya daga cikin matan da a ka tura
Kwairanga su ka yaudarar da sarakai ta kamu da ciwon son sa ta dinga
zuwa har cikin firsuna ta na taimakonsa tare da shan alwashin sai ta
fitar da shi daga halin kuncin da ya ke ciki.
Usman na da shekaru
bakwai a ka fara shigar da shi daji a na gogar da shi ilimin yaki tun
daga kan fada da mutane har zuwa dabbobi tare da koya masa dabarun fada
da takobi da mashi da iya harbi da kwari da baka da sauransu.
Ya na
da shekaru goma sha biyu ya kware sosai ya zama sadauki a fagen yaki duk
kasar yammawa an sallama masa har su na yi masa kirari a shafi na 12 su
na cewa " Usman Mai duniya na Kaura yalli, gwaggon biri makashin maza".
A lokacin ne a ka sanar da Usman labarin mahaifinsa da irin wulakancin da Damangawa su ka yiwa masarautarsa.
Ai kuwa Usman Mai duniya ya shirya tare da abokinsa Sabi'u wanda su ka
taso tare dan Kaura yalli wato kawun Usmankenan, su ka nausa daji.
Shi kuwa Sarki Haruna Kabir Zubaida ta kubutar da shi daga gidan
kurkukun sun shiga duniya, in da suka yi aure daga bisani wahalar da ya
sha a kurkuku ta kwantar da shi ciwo.
Jarumta
Usman kuwa tun
shigarsu daji ya ke nuna jarumtarsa in da ya kashe Gada suka cinye a
shafi na 23, sannan ya gwabza yaki da wasu 'yan rawar wuta a shafi na
26, ya yi gumurzu da Sarkin fawa a shafi na 27. Sun buga gumurzu da
mayakan garin Dawaki a shafi na 32 in da su ka biyo bayansu, maimakon
Usman ya gudu sai su ka tsaya suna cafe mashi da kibbau, in da ya ke yi
wa kansa kirari, "Kai arna ba ku sanni ba ne? Ni ne Usman Mai duniya,
gwaggon biri makashin maza ni ne hadari malfar duniya". Nan ya afka musu
ya karkashe su.
Haduwarsu da aljani wanda ya ba Usman takobin kakansa da suka ara su kai yaki a shafi na 33-34.
Usman ya shiga gasa a kasar Zainawa in da ya yi dauki ba dadi da mayaka abokan takara a shafi na 36.
Sannan ya gwabza da sarkin yakin garin Kaura Malle wanda manyan baraden
nahiyar ke shakkar arangama da shi saboda rashin tausayinsa, amma Usman
bai saurara ba sai da ya fatattaka jikin Kaura Malle ya cinye gasar a
shafi na 37-39.
Ya taimakawa Sarkin Zainawa sun yaki mutanen kasar
Dawaki in da ya gwabza da manyan mazaje da kauraye a shafi na 55 sannan
ya yi gumurzu da Sarkin in da ya shafe shi a doron kasa........
Za mu ci gaba a sati mai zuwa.....