Wasu daga cikin mahalarta taron
Marubutan Hausa sun xauki
xamara don gudanar da bikin marubutan Hausa na duniya. A ranar Asabar ne 6 ga
Yuni, 2015 aka gudanar da zama na farko na shire-shiryen gabatar da taron. Tunanin
shirya wannan biki ya taso ne bayan tattaunawa tsakanin marubuta ta kafofin
intanet, wanda ya biyo kafa kwamitin da zai jagoranci taron karqashin Malam Ado
Ahmad Gidan Dabino, MON. Ana sa ran taron zai haxo marubuta daga faxin duniya
musamman qasashen da suke na Hausawa da makwabtansu.
A yayin qaddamar da
kwamitin, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, ya yi bayanin amfanin ranar ga
marubutan Hausa. A cewarsa taron zai haxa tsofaffi da sababbin marubuta don
tattaunawa da musayar ra’ayin a kan cigaban adabin Hausa. A yayin taron ana sa
ran za a yi bajakolin littattafai sannan a gabatar qasidu da taron sanin
makamar aiki da karance-karance qirqirarrun labarai da waqoqi.
Marubuta daga Kano da
Katsina da Kaduna da Jigawa na daga cikin waxanda suka samu damar halarta taron
qaddamar da kwamitin da tattaunawa. Hakazalika, qungiyoyin marubuta na daga
cikin waxanda za su taka rawa a wajen ganin nasara shirin. Ana sa ran za a yi taron
a watan Oktoba na wannan shekara a garin Kano. An zavi Kano ta kasance garin da
za a gudanar da taron saboda matsayin jihar wajen raya adabin Hausa, musamman
ta vangaren haziqan marubuta da jihar ke da su da kuma rubuce-rubuce da kasuwancin
littatafai.
Akwai fatan cewa bayan
an gudanar da taron za a samu cigaba a harkar rubutun Hausa ta yadda za a shigo
da sababbin tsare-tsare da zasu inganta harkar. Musamman yadda marubuta ke kuka
na lalacewar harka a wannan lokaci. A halin yanzu marubutan Hausa ba kowa ba ne
yake iya sayar da koda kofi dubu biyu na litatttafansu duk da xinbin al’aummar
da qasar Hausa take da ita. A Kano a shekarun baya, akwai marubutan da sun
sayar da kofi sama da dubu xari shida na littafinsu a lokacin da ake ganin
Kanon ma ba ta tunbatsa ba.
An shiga wani qarni da
matasa ba sa son karance-karance, duk da cewa wasu na ganin matsalar ba ta
rashin karance-karance ba ce. Amma maganar gaskiya matasa a yanzu sun fi mayar
da hankalinsu wajen hawa kafofin yanar gizo ko intanet da kallon fina-fina,
wanda hakan ya kawo naqasu ga harkar ilimi da adabin ma. Sanin kowa ne babu
alummar da zata cigaba matuqar matasan ta basa karatu.
Ina ganin lokaci ya yi
da gwabnatin jihar Kano tare da hukomomi na ilimi za su haxa kai don jagorantar
farfaxo da harkar rubutu, ta yadda za a qarfafi marubutan mu na gida da su yi
rubuce-rubuce masu nagarta, da yin tsare-tsare da zasu inganta harkar. Misali,
sanya gasar rubuce-rubuce, xaukar nauyin yin wasu rubuce-rubuce masu fa’ida da
tarurrukan qarawa juna sani.
A wannan duniya da muke
ciki ta bani gishiri in ba ka manda, ba abin da ake buqata illa gudunmawar da
kowace al’umma za ta iya bayarwa na cikar da duniya gaba. Allah ya taimaki
rubutu na marubuta gaba xaya.
Daga,
Zaharaddeen
Ibrahim Kallah
No comments:
Post a Comment