Sunanta Hafsat Zakariyya, babarbarriya ce yar usuli. Tana da tsayi sannan ba ta da jiki sosai. Duk da cewa ba fara ba ce ba za a kira ta baƙa ba, domin tana da hasken fata; irin fatar da Turawa ke kira launin cakulet. Kyakkyawa ce ajin farko, amma wannan kyau ya disashe, fararen idanunta dake zama abin so ga masu kallon su sun rikiɗe sun koma jajir. Gaba ɗaya ta rame ta fita hayyacinta kamar ba ita ba.
Hotunansa da rubuce-rubucen sa dake zama abokan hirar ta, ta tattara ta kulle su duk saboda baƙin ciki. Zanna Bulama masoyinta da take burin aure, suna son junansu matuƙar so. Shi ne masoyin da ya fara karanta mata karatun so ya kuma ɗora ta a bisa turbar soyayya. Amma kash, ya rage sati biyu a yi bikinsu, Allah Ya karɓi ran Zanna, sakamakon haɗarin mota.
Wannan shi ya hargitsa tunanin Hafsa, ya sauya rayuwarta. A koyaushe mutuwar kan koma mata sabuwa fil; har wasu mutane na tsegumi kamar ita ma ta mutu ne; idan aka yi la'akari da yadda komai na ta ya sauya kuma ba sauƙi bare dangana.
Ruwan ƙwalla masu ɗumi suka zubo daga idanunta suka bi kumatunta suna zuba a kan matashin kai da take kwance. Cikin shasshekar kuka take cewa, Masoyi kana ina, ko kana ji na, shi kenan ka tafi, ba za ka dawo ka ganni ba. Hawayen ya cigaba da fita da sauri.
Zanna Bulama shi ma babarbare ne haifaffen Maiduguri. Matashi ne da bai wuce shekara talatin ba, kuma ƙwararren marubuci ne da yake rubutu cikin harsunan Ingilishi da Hausa. Asali ma shi ne wanda ya cusawa Hafsa sha'awar rubuce-rubuce. Sun gama tsara rayuwarsu da irin zaman da za su yi tsakanin miji da mata, da yadda bikinsu zai kasance da yayan da suke son haifa. Amma duk wannan buri ya zama tamkar gajimare a sararin samaniya da ba shi da ruwa.
Tafiya ta yi tafiya, alamarin Hafsa babu sauƙi kamar ciwon arne. Wannan ya ƙara tayar wa da iyayen Hafsa hankali. A baya kowa a danginta ya san Bakura, ɗan Aminin mahaifinta na matuƙar son ta, amma saboda Zanna ya karɓi mukullin zuciyarta, Bakura ya haƙura. Wannan hali da take ciki ne ya sa iyayenta tunanin aurar da ita ga Bakura. A ganinsu wannan hanya ce da za ta rage ma ta baƙin ciki.
Amma ita Hafsa ta nuna ƙin amincewarta. A ganinta ta gama soyayya da wani ɗa namiji, kuma kamar ta ci amanar Zanna ne idan ta saurari wani.
Cikin kuka take cewa, Ka tafi ka barni, yanzu za ka so wani ya aure ni alhali ni ce matarka da kake buri? Ta girgiza kai. Zanna ba zai yuwa ba, na san kana fushi da ni matuƙar wani ya karɓi zuciyata.”
Ina son ki gane zamanki ba zai yu wu haka ba, ba za mu zuba miki ido ba. Tun da kin ƙi ki ɗauki ƙaddara, na riga na yanke shawara ko kin amince ko ba ki amince ba, zan auran da ke ga Bakura. Domin haka shi ya fi dacewa da ke. Kalamin da ya fito daga bakin mahaifinta kenan bayan ya sa an kirawo ta babban ɗakin hutawarsa.
Wannan ya sa zuciyarta ta dinga bugawa, numfashinta na tasowa sama, a daddafe ta rarrafa ta koma ɗakinta tare da faɗawa kan gado. Nan take ta ɓarke da wani sabon kukan. Mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, nan take tunanin Zanna ya dawo ma ta sabo, ta shiga yi wa kanta tambayoyi a zuciyarta.
Shikenan sai ta je ta auri wani wanda take ganin tsarin rayuwarta bai zo ɗaya da na shi ba. Zanna ne wanda ya ɗanɗana ma ta so, shi ne wanda ganinsa yake faranta ma ta rai, wanda yake jin ta har cikin jinin jikinsa. Duk wannan ya zama tamkar mafarki?
A wannan yanayi ne ta tuna da wata rubutacciyar waƙa da Zanna ya taɓa rubutawa mai taken Mijin Budurwa, waƙa ce da ya taɓa rubuto ma ta ita a lokaicn da ta yi fushi da shi, yayin da wata budurwa yar rigima ta taɓa cewa tana son sa. Nan ta fara tuna wasu baituka da suka daɗe a cikin ƙwaƙwalwarta.
Ni na miƙa wuya,
A yau sauraran ki nake,
Ko ki yarda ko ki ƙiya,
Ƙauna ta gare ki take.
Ni ne mijin budurwa,
Budurwar Hafsa take,
Mabuɗin soyayya ta,
Ai gurin ki yake.
Ita ma rayuwata,
Bisa soyayyar ki take,
A yau idan babu ke
Tabbas mutuwa nake.
Nan Hafsa ta sake fashewa da sabon kuka. Shin tana ganin ita son na ta bai cika ba. Domin babu Zanna amma ita tana nan a raye, har za ta auri wani. Zanna a waƙarsa yana cewa, shin ne mijin budurwa, kuma budurwar Hafsa take. Nan ta cigaba da girgiza kai, ta gamsu a yanzu ne ya zam mijin budurwa, amma Bakura ba mijin budurwar Zanna ba ne.
An doshi wata shida da mutuwar Zanna, alamarin sai ƙara zafi yake. Mahaifin Hafsa ya tsaya kai da fata sai an aurar da ita ga Bakura. Hafsa kuma ta ƙi amincewa. Cikin wannan hali ne a gidansu aka rabu gida biyu, wasu suna ganin a bar Hafsa ta koma makaranta, a ganinsu wannan zai sa ta samu sauƙin damuwarta, yin haka zai sa a yi nasara cikin sauƙi. Ɗaya ɓangaren kuma suna masu goyon bayan auren ta da Bakura ba tare da jinkiri ba shi ne mafita.
Shigowar Burema wato babba yaya a gurin mahaifin Hafsa ya sa wa wutar ruwa, inda ya yanke hukunci Hafsa za ta koma Kano gurin antinta Hasana don ci gaba da karatu. Anti Hasana ya ce ga Burema, tana auren Hashim, wani babban maaikacin banki da ya daɗe yana zaune a Kano.
Sati uku kenan da fara karatun Hafsa a Kano, tana karanta ilimin harshen Hausa da Ingilishi a Kwalejin Kumbotso. A tsawon wannan lokaci ba ta hulɗa da kowa, hatta mata yanuwanta sallama ce kawai a tsakaninsu. Idan ba ta ɗakin ɗaukar karatu za ka gan ta ware tana bitar karatunta. Wani lokacin kuma ta kan shiga kogin tunani har da kuka idan ciwon da ke damfare a zuciyarta ya motsa. Haka rayuwarta ta cigaba a Kano, har ta zama yar gari. Kwanci tashi har ta samu wata biyu da fara karatu a Kano.
**************
Ranar wata Juma'a ce za ta makaranta, tana cikin tasi. Direban ya kunna rediyo yana sauraron tashar Rediyon Kano. Ba su jima suna tafiya ba mai gabartarwa ya sako wata rubutacciyar waƙa da wani marubuci ya rubuta ya kuma rera kayarsa.
A hankali waƙar ta isa ga ƙwaƙwalwarta, nan take sai ta rikice. Ya Salam, mene ne a ciki da ya dunguza ta? Waƙar tana tafe a hankali kamar haka:
Ya Hayyu ya ƙayyumu,
Shi muke roƙo kullum,
Don Shi ke ƙulla soyayya.
A yau ina so ki sani,
Zuciyata na neman tsani,
Don yin ƙoli a soyayya.
Ai ita budurwa,
Allura ce cikin ruwa,
Da so ko babu soyayya.
Mai rabo kan ɗauka,
A fili ko a ɗaka,
Don haka ne muke soyayya.
Allah ne ya san mijin budurwa,
Amma zan yi iyo cikin ruwa,
Na lalubo ki ya masoyiya.
Nan fa aka famo mata ciwon da ya daɗe a zuciya. Hawaye kuwa ya dinga zuba kamar an ɓalle gulbi. Ba ta dawo hayyacinta ba sai da direban tasin ya juyo ya ce.
Hajiya, ba a nan za ki sauka ba?
Ba ta san an kawo makarantar ba, don ta faɗa kogin tunani. Ta fidda kuɗinsa ta biya shi sannan ta shiga makaranta tana tafe a hankali kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki.
A ranar nan karatun da ba ta yi ba kenan. Shin wane ne wannan marubuci da muryarsa take tafiya kamar ta Zanna? Wane ne wannan da yake amfani da wasu kalamai da suka yi shige da wanda aka taɓa gaya mata a baya? Wannan tunani shi ya dinga shiga ƙwaƙwalwar Hafsa yana shawagi, nan ta ɗokanta ta san wannan marubuci. To ta yaya hakan za ta yiwu, bayan waƙa ce ta ji a gidan rediyo, hasali ma ba ta ji sunan wanda ya yi waƙar ba.
Ba a tashi ba ta fice daga makarantar, ba ta zame ko ina ba sai gidan Rediyo.
Kina buƙatar a yi miki kwafin waƙar ne? Maaikacin da ta samu ya buƙaci ji bayan ta yi tambaya a kan waƙar da aka sa.
Ta gyaɗa kai. Ina buƙata, amma fa ina so in san wane ne marubucin da kuma inda zan same shi.
Mutumin ya yi shiru na ɗan wani lokaci, sannan ya ce.
In dai waƙar da kike nufi ce, wani marubuci ne da ake kira Abba Major ya rubuta ta, sannan ya rera kayarsa. Matashin marubuci ne da ya yi suna a garin nan, amma ni kaina ban san shi ba a zahiri. Duk waƙoƙinsa muna samunsu ne ta hannu shugaban gidan rediyon nan, wanda suke da alaƙa sosai. Sai dai shi shugaban namu ya yi tafiya ƙasar waje a halin yanzu, ban san ko yaushe zai dawo ba.”
Ya sake yin shiru yana kallonta kafin ya cigaba. Amma dai na taɓa ji an ce yana cikin Ƙungiyar Marubuta Ta Najeriya (ANA) reshen Jihar Kano. Su kuma ofishinsu yana ɗakin karatu na Murtala Muhammad, dake kan titin Ahmadu Bello. Ina fatan kin san gurin?
Ta gyaɗa alamun ta sani duk da cewa ba ta taɓa zuwa wajen ba.
Yauwa, ina ganin idan ki ka je can za su ba ki cikakken bayani.
Ta yi murmushi.
Na gode ƙwarai, ya maganar kofin waƙar?
Ya miƙe. Wannan ba damuwa, idan kika ba ni nan da minti goma za a samo miki.
Daren wannan rana ba ta samu barci ba, domin kaset ɗin waƙar Abba Major ne ya mamaye gurbin barcinta, da ya ƙare sai ta sake dawo da shi baya. Kashegari, ba ta samu farkawa ba sai da rana ta fito sosai. A gurguje ta shirya tana so ta tafi ɗakin karatu na Murtala Muhammad don neman bayani.
Ta gama karyawa za ta fita sai ga Bakura ya zo gidan. Wani abu mai kama da gayan fura ya tokare mata a wuya don haushi. Ta san cewa kafin ta yakice shi ta tafi inda za ta, abin da wuya. Aikuwa kamar carbi ya tsinke ya shiga zuba ratatatta ba sayawa. Ta yi saa a wata gaɓa ta jefa masa waigi, To ni fita zan yi.
Ya yi murmushi. To mu je na kai ki, ba makaranta za ki ba?
Ta girgiza kai.
Na gode ba makaranta za ni ba.
To Hafsa ko ina za ki ai ba kya ƙi na kai ki ba.
Da kyar ta amince su ka fito a motarsa. Bayan sun fito daga gida ne ya dube ta ya ce.
Ina za ki ne?
Ahmadu Bello Way za ka kai ni, ka san titin?
Ya yi dariya Hafsa ai ba yau na fara zuwa Kano ba, ko kin manta Jamiar Bayero na yi?
Ta ɗan yamutse fuska. Ka yi haƙuri, na manta.
A ina a Ahmadu Bello Way? Ya buƙaci ya ji.
“Murtala Muhammad Library za ka kai ni.
Okay, ashe karatu za ki.
Ba ta ƙara cewa komai ba, haka ake tafiyar iyakarta daga e, eh sai gyaɗa kai har suka zo ɗakin karatun. Tangamemen gini ne hawa huɗu, wanda ganisa ya sa ta cikin mamaki kasancewar duk girmansa an tanade shi ne don gudanar da karatu da bincike. Lalle Kano sai Kano, ta ce a ranta.
Ya ja birki ya tsaya a gurin ajiye mota. Hafsa ina iya biyo ki? Ya tambaya tare da kallon fuskarta.
Ka biyo ni, Ta nanata, Ba karatu na zo ba kenan.
Ya fashe da dariya, To shi kenan, yaushe zan dawo in ɗauke ki?
Ba ni da tsayayyen lokaci, don haka na hutaasshe ka. Ta buɗe ƙofa ta fita.
Ni dai zan zagayo. Ya ce yayin da ya sa giya.
Kanta tsaye ta nufi ƙofar shiga gabanta yana dukan uku-uku, hanunta riƙe yake da wasu littattafai guda biyu sai jaka da ta rataya.
Ta yi sallama yayin da ta isa bakin reception ɗin. Wani mutum ne dogo ga faffaɗan ƙirji da tsare gira yake zaune a gurin.
Don Allah ofishin ƙungiyar marubuta nake tambaya?
Mutumin ya yi nuni da yatsansa sama.
Sama za ki hau hawa na uku daga ɓangaren dama a nan ofis ɗin na su yake.
Na gode. Ta ce sannan ta juya ta nufi inda matattakala take da sauri, tana ji a ranta kamar za ta ga Abban a can.
A daidai matattakalar hawa na biyu ne suka yi kiciɓis da wani matashin saurayi yana saukowa. Yana cike da ƙuruciya, fuskarsa cikin faraa da anashuwa. Idonta ya kai ga fuskarsa, zuwa kwayar idanunsa. Ba ta san lokacin da ta kuskure sawunta ba, ta tafi rikica za ta faɗi, littattafan dake hannunta suka tarwatase a ƙasa. Cikin zafin nama matashin ya sa hanunsa ya riƙo ta, a lokacin ta ja wani gwauron numfashi.
Sannu! Sannu kin ji, ba dai ki ji ciwo ba ko?
Ta maido da numfashin, tashi ɗaya idanunta suka firfito. Ban ji ciwo ba, na na na gode. Ta ce cikin harɗewar harshe tare da haɗiyar wani yawu.
Ya sa hannu ya kwashe ma ta littattafanta da suka zube, ya miƙa mata.
Ta karɓa, Na gode, amma malam don Allah na tambaye ka?
Yi tambayarki Allah ya sa dai na sani.
Ta sake kallon shi. Kai mutumin Maiduguri ne?
Ya yi murmushi gami da girgiza kai.
Aa, babu abin da ya haɗa ni da Maiduguri, ni ɗan Kano ne.
Shike nan da ma kana yi mini kama da wani ne, har muryar. Ta faɗa tana alajabi.
Allah Sarki.
Nan suka rabu ta hau sama shi ku ma ya yi ƙasa. Haƙiƙa Hafsa ta shiga cikin alajabi, domin a fizge saurayin da suka yi kiciɓis da shi yana ɗibar kama sosai da masoyinta Zanna. Sai dai shi ya fi Zanna tsayi, sannan yana da hasken fata da manyan idanu.
A cikin tunani ta isa ga hawa na uku, ta yi dama har bakin inda ofis ɗin yake. A buɗe ta tarar da ofis ɗin, sai dai babu kowa a ciki, don haka sai ta tsaya a bakin ƙofa tana jira. Kusan minti biyar sai ga wani matashi baƙi mara jiki sanye da kaftani da hula ya nufo gurin da sauri. Bayan ya ƙaraso gurin ya ce.
Yi haƙuri Hajiya, ba ki tarar da kowa ba ko, wallahi na hau sama ne.
Ta yi murmushi, Babu komai, ai ban jima ba.
Suka sake gaisawa bayan ta zauna, sannan matashin ya ce, Ko akwai abin da ki ke buƙata?
Ta gyaɗa kai.
Eh, dama daga gidan Rediyo Kano aka turo ni nan. Da ma na ji wata waƙa ce da suke sanyawa, a jiya ma sun sanya ta. To na je gurinsu a kan ina so na san wannan marubucin waƙar. A can aka ce min sunansa Abba major; kuma yana wannan ƙungiyar taku. An ce dai idan na zo zan samu ƙarin bayani. To ban sani ba ko ka san Abban?”
Ya yi murmushi, Kayanki ya tsinke a gindin kaba. Abba ɗan ƙungiyarmu ne, sai dai bai jima da barin nan ba. Na san dai yau ba zai dawo ba.
Suka yi shiru na wani lokaci zuwa can ya katse shiru da cewa, Sai dai in kina son ganin sa, to akwai taron Dandalin Marubuta da za a yi gobe Lahadi da safe, na san dole zai zo. Kina iya zuwa goben za ki gan shi.
To kamar ƙarfe nawa kenan, kuma a ina? Ta buƙaci ta ji.
Goma ake farawa, za a yi shi a nan gidan a babban hall dake ƙasa.
To na gode, goben Insha Allahu zan zo.
Sai kin zo.
A wannan rana ma ba ta samu nutsuwa ba, domin abubuwa ne suke faruwa da ita ɗaya bayan ɗaya. Haɗuwarta da saurayin da ya riƙe ta da za ta faɗi da yadda yake magana ya sanya ta a tsohuwar gonar tunani.
Wataƙila yanayi da ya ɗauka da Zanna shi ya ja hakan. A lokaci guda sai ta fara tunanin ko kwakwalwarta ta motsu ne, domin ta ji muryar mawaƙi a gidan rediyo ta kiɗime, sannan ga wani matashi ta gani ta rikice saboda yanayinsa da Zanna. Shin ko duk mutanen Kano kamar Zanna suke, anya ba idanuwanta ke gizau ba sannan kunnuwanta sun narke da kalaman marigayi?
Gaba ɗaya sai tunanin Zanna ya sake bijirowa, ta dinga tuna abubuwan da suka faru, to yau ga shi ta haɗu da wani wanda yake yanayi da Zanna, yadda yake magana da yadda ya yi murmushi yayin da ƙwayar idanunsa ta haɗu da ta ta, duk sun haɗu sun sa ta a cikin wani hali wanda ita kanta ba ta san wane iri ba ne.
Aa babu abin da ya haɗa ni da Maiduguri, ni ɗan Kano ne. Kalamin da matashin ya yi mata da yadda ya jefe ta da murmushi ta tuna. Da wannan tunani barci ya kwashe ta.
Kashegari, goma saura kwata a ɗakin karatu na Murtala Muhammad ta yi mata. Numfashinta ya fara ƙoƙarin ɗaukewa, yayin da zuciyarta ta dinga bugawa da sauri sannan jinin dake gudana a jikinta ya harba cikin sauri, a lokacin da ta yi arba da wannan saurayin da ya taimake ta a matattakalar bene.
Shi kansa ya shaida ta, don shi ya fara ma ta magana, Ah, yau ma kin shigo gidan.
Ta yi murmushi, Wallahi na zo taron marubuta ne.
Okay, sannunki da zuwa. Ai ba a fara ba kin shigo da wuri, amma nan ba da daɗewa ba za a fara. Kya iya shiga daga ciki ɗakin taron.
A ina gurin taron yake? Ta tambaya.
Mu je na raka ki, ashe ba ki taɓa zuwa ba.
Yau shi ne zuwana na farko.”
Suka jera suna tafe, daga shi har ita wani abu na daban suka ji a tattare da su. Shi a ɓangarensa zuciyarsa ce ta dinga dukan uku-uku, duk da cewar ya sha yin muamula da manyan mata, amma bai taɓa jin yanayin da yake ji ba a tare da wannan yarinya mai kwarjini da cikar zati.
Kina yin rubutu kenan? Ya tambaya.
Ta yi murmushi Na kan yi, amma dai ban yi ƙwari ba.
A hankali za ki yi.
A ɗakin taron mutanen da ke ciki ba su fi mutum biyar ba. Ya sama mata guri a inda mata suke zama tare da cewa.
“Sai kin ɗan yi haƙuri, ina ga za a kai 10:30 na safe kafin a fara. Kin san marubuta, ban sani ba ko rubutun dare da suke yi ne yake sanya su makara.”
Ta yi murmushi bayan ta zauna tare da cewa.
Babu komai. Amma dai Allah ya sa kuna tashi sallar asuba?
Shi da itan suka kyalkyale da dariya, dariyar da ba ta taɓa yin irinta ba tun da Zanna ya bar duniya.
Suna yi mana, har da zikirin safe. Ya maida mata.
Kafin ya ƙara cewa komai, wani ya zo ya kira shi. Ga alama yana cikin shugabannin shirya taron. Haƙiƙa idan ka dubi fuskarsa bai so haka ba, wataƙila ya so su kasance tare har a fara taron. Tun da aka janye shi ba ta sake yi wa kowa magana ba, tana zaune ita kaɗai tana mamakin da hasashen yadda Abba Major zai kasance, har aka fara gudanar da taron.
Hafsa ta yi shiru tana sauraren yadda ake gudanar da Dandalin Marubutan, amma kuma a wani ɓangaren daga cikin zuciyarta tana tunanin a wane lokaci ya dace ta nemi wane ne Abba Major.
Yanzu za mu saurari wata rubutacciyar waƙa mai taken Taaziya’ daga bakin Abba Major. Wannan jawabin da shugaban taron ya yi shi ya ja hankalin Hafsa.
Ta firfito da idanunta ta ga wane Abban da ta zo gani. A hankali ya taso ya ratsa cikin jamaa zuwa inda aka tanada don magana.
Yayin da aka miƙa masa abin magana sai abin ya ba ta mamaki, ganin wane ne Abba Major. Saurayin da suka haɗu ne a jiya wanda a yau ma shi ya kai ta har inda ta zauna, tare da yin raha da shi, amma ba ta san shi ne take nema ba. Lalle biri ya yi kama da mutum, ta ce a cikin zuciyarta.
Bayan ya karɓi abin maganar ne sai ya fara da magana kamar haka. Assalamu Alaikum yan uwana marubuta. Kamar yadda kuka ji wannan waƙar ta wa sunanta ‘Taaziyya. Haƙiƙa waƙar na rubuta don taaziyya ga abokina Zanna Bulama da Allah ya yi wa rasuwa. Ban samu labarin rasuwarsa ba, sai a watan da ya gabata. Allah ya yi masa rahama.
Ameen. Mutanen dake ɗakin suka amsa gaba ɗaya.
Nan ya shiga cikin waƙar ya dinga warwarar jigon ta. Ba ta san lokacin da ta fashe da kuka ba. Haƙiƙa tun sanda ya kira sunan Zanna gabanta ya faɗi, a yayin da kuma ya shiga cikin waƙar ne ta tabbatar Zannanta yake nufi, domin ya yanko labirinta da Zanna da labarin soyayarsu da rasuwarsa ana dab da bikinsu. Salon muryarsa da hawa da saukar baitin, kamar yadda Zanna yake rera waƙarsa ne.
Waƙar ta ratsa zukatan jamaar da ke gurin, sun yi shiru kamar ruwa ya ci su. Shasshekar kukanta sai ya ja hankalin jamaar dake gurin har aka dinga waigawa a ga mai kukan. Shi kansa Abba da ya hango ta ya tabbatar ya tayar mata da hankali. Haƙiƙa duk da ba wani saninta ya yi ba, ba ya son ya cigaba da wannan waƙa tun da ta rikita ta. Don haka ya nemi afuwa a gurin jamaa zai tsaya a nan duk da cewa bai ƙarasa ta ba.
A lokacin Hafsa ta miƙe ta yi waje. Ganin ta fita shi ma Abba ya bi ta wajen. Ya same ta jingine da bango ta rufe fuskarta da gyalenta.
Malama ya kira a lokacin da ya zo gurin.
Ta ɗago ta dube shi, bayan ta yaye gyalen da ta rufe fuskarta. Idanunta sun yi jajur sosai a cikin ƙanƙanin lokaci.
Ya ci gaba da cewa.
Ki yi haƙuri ban ji daɗi da ganin waƙar ta tada miki hankali ba.
Duk da kukan da ke tare da ita, bai hana ta yin tattausan murmushi ba, a lokacin da ta buɗe fuskarta tare da ganin Abba.
Abba, ni godiya zan maka saboda adduarka ga masoyina. Ko kaɗan kar ka damu da ganin ina kuka. Kawai ka tuna min da wani alamari da ya wuce ne.
Cikin rashin fahimta ya sake dubanta tare da alajabi.
Kina nufin kin san Zanna?
Ta gyaɗa kai gami da murmushi.
Ni ce Hafsa ɗin da ka ke magana a waƙarka. Abba tun daga ranar Jumaa da ta wuce abubuwa na mamaki ne suke faruwa da ni. Ranar Jumaa za ni makaranta na ji wata waƙa da ta yi nasaba da irin waƙoƙin da marigayi ya taɓa yi min. karin waƙar yana tafiya kamar yadda muryarsa ta ke, a ranar na kasa haƙuri na tafi gidan rediyo don sanin wane ne wanda ya yi waƙar. Ta goge wasu hawaye da suka zubo mata kafin ta cigaba.
“A can aka tabbatar mun Abba Major ne ya yi ta. Jiya na shigo nan don in neme shi, sai Allah ya haɗa ni da kai. Tun da na ganka sai na ga kamar marigayi, haƙiƙa ban taɓa ganin wanda ya yi kama da shi ba, kamar ka. Mun rabu da kai na hau sama aka ce min Abba ya fita, amma in dawo yau. Ina shigowa yau da kai muka fara haɗuwa. Wai duk abin da ake, kai ne Abba Major da nake nema tun shekaranjiya. Sai ga shi ka nuna ka san marigayi wanda waƙarka ta nuna hakan.
Shi ma sai ya ji kamar ƙafafuwansa ba za su ɗauke shi ba, nan sai tausayinta ya ƙaru a zuciyarsa. Cikin murya mai cike da alhini ya fara da cewa.
Zanna abokina ne; ta re muka gama Jamiar Ahmadu Bello Zaria. Haƙiƙa mun yi kama da juna matuƙa, wanda hakan shi ya ƙara danƙon zumunci da abotarmu. Domin mutane a makaranta kan yi zaton ko yanuwa ne mu. Kin san iko na Allah ya fi ƙarfin tunaninmu.
“Ni da Zanna mun shiga ƙungiyar marubuta ta Jamiar Ahmadu Bello, a rana ɗaya kuma a nan muka samu aƙidar rubuce-rubuce. Hatta ɓangaren waƙa, mutum ɗaya ne ya horar da mu, wannan ya sa ki ka ji muryarmu ta zo kusan ɗaya.
Wasu hawaye suka sake biyo kuncinta, amma wadannan hawaye na farin ciki ne, domin masu sanyi ne. Cikin murmushi ta ce, Haba, shi ya sa jiya na ke tambayarka ko kai ɗan Maiduguri ne.
Ya ɗago ya sake duban idanunta. Duk da kukan da ta yi bai hana shi ganin hasken idanunta ba.
Hafsa yaya haƙuri?
Haƙuri Alhamdu Lillahi.
Allah ya ji ƙan Zanna, ya sa Jannatul Firdausi makomarsa”.
"Ameen."
Zaharaddeen Ibrahim Kallah
dinik2003@yahoo.co.uk
No comments:
Post a Comment