A yau mun wayi gari rayuwa a ƙasar Hausa ta sauya, tarbiyar yara ta lalace. Kawaici, yakana da kara da aka san mu da su, sun ɓalɓalce. Wannan ya sa muka shiga ruɗani, har ta kai muna neman manta su wane ne mu. A lokaci guda, fatara da talauci, sace-sace da zaman banza suka yi mana katutu.
A ƙasar Hausa, a ƙarni na 19 zuwa wani lokaci a ƙarni na 20, za ka ɗorawa tsohuwa kwarya cike da kuɗi ko gwala-gwalai daga wani ɓangare na gari zuwa ƙarshensa, ba tare da wani ya tare ta ba ya kwace. Amma yanzu ta kai akan bainar idon jama'a ne za a yi maka kwace ko fashi, babu wanda zai kawo maka ɗauki.
Shekaru kamar biyu baya, na ji muryar wani matashi yana kuka a gidan Freedom Radio, yana cewa a bakin ƙofar mata cikin cunkosa jiran a basu hannu, wasu matasa suka sa masa wuƙa akan ya basu wayar salularsa.
Matashin ya yi ƙoƙarin yi musu gardama, ya fara kururuwa yana kiran ɗaukin jama'a, amma babu wanda ya kawo masa ɗauki. Nan suka yanke shi a hannu suka yi awon gaba da wayarsa. Hakan ya sa ya shigo gidan radiyon yana kuka, yake cewa "Kai jama'a, kamar ba garin musulmai ba."
Haƙiƙa da gaskiyarsa, garin Kano garin musulmi ne da aka gina shi abisa doron dangantaka da kyakkyawar makwabtaka. Abin da ya shafi makwabcinka ya shafeka gaba da baya. Tun daga tarbiyar yara, kasuwanci da tattalin arziƙi, da addini, tsaro da sauran abubuwan da suka shafi zamantakewa.
To, amma yanzu abin ba haka yake ba. Tun da Turawan mulkin mallaka suka shigo Daular Usmaniyya, muka fara yin watsi da kyawawan ɗabi'u da al'adunmu.
Duk wannan abin da ake, Turawan Birtaniya sun yi mulki ne na bayan fage, wato 'Indirect Rule'. Sun fahimci a lokacin irin matsalolin da za su fuskanta idan suka taɓa mana addini da al'adu.
A yau a karan kan mu, mun yi watsi da waɗannan kyawawan ɗabiu, mun rungumi na baƙin haure. Duk nacin mu fa, ba za mu iya zama Turawa ba, ko yin abin da suke a al'adunsu. Sai dai idan za mu sauka daga tsari da tarbiyar musulunci da ta iyaye da kakanni.
A wajen tarbiyyar 'ya'yanmu, a yau makwabci ba zai iya saka baki akan tarbiyar ɗan makwabcinsa ba. Sannan yaran makwabta za su iya zama ba karatun boko bare na addini, ba tare da damuwar makwabci ba.
Ta ɓangaren sana'a, ba ma koyawa 'ya'yan makwabta yadda za su dogara da kansu. Rayuwa ta zama kowa ya iya allonsa ya wanke.
Da yawan 'yan boko da suka zama baƙaƙen Turawa na jin haushi talakawa da ba su rungumi tsarin rayuwa na zamani ba. Ina da matata ɗaya da 'ya'ya uku, amma makwabcina ya tara mata huɗu da 'ya'ya ashirin a gidan haya, wanda wasu ma tare suke kwana da yaransa a ɗaki ɗaya.
Shi ma talaka na jin haushin 'yan boko kan cewa ba su da tausayi, kuma suna yi masa buƙulun jin daɗi ɗaya da yake morewa, na ya yi jima'i yadda yake so.
Wannan ya haifar da rashin jituwa da watsi da juna, har da kai an raunana makwabtaka, an wargaza harsashin tarbiya.
Mun san yadda manzon Allah, Annabi Muhammadu (S.A.W) ya dinga bijirowa da sahabbai mihimmanci makwabtaka, har suka yi tsammani zai ce makwabci zai iya gadar makwabcisa.
Duk wannan sakacin da riƙon sakainar kashi da muka yi, shi ya kai mu ga halin da muke ciki a yanzu.
A yau matasa da suke da mafi rinjaye na yawan al'umarmu ba su da sana'a, uwa uba ba su samu cikakkiyar tarbiya ba. Wannan shi ya ƙara assasa shaye-shayen miyagun kwayoyi da suke taimakawa wajen aikata muggan laifuka.
A yanzu a garuruwanmu, musamman Kano da take babban birni kuma cibiyar mutanen Arewa, sace-sace da kwace a gurin waɗannan matasa ya ƙara ta'azzara. Akan wayar da ba ta fi N15,000 ba, za a iya kashe mutum. Satin da ya gabata mun ji labarin yadda aka kashe wani bawan Allah a unguwar Jan Bullo. Unguwar da ake ganin mazaunanta akasari ba talakawa ba ne tiƙis.
Ta kai yanzu ana bada shawara ga mutane da su kiyayi bin wasu tituna a Kano a wasu lokuta, musamman lokutan da ƙafa ta ɗauke.
Bai fi sati biyu ba, ƙanina ya shigo babur ɗin A Daidaita Sahu, inda ya samu wata budurwa a ciki. Matuƙin babur ɗin na tare da abokinsa, wanda suke sawa a gefen direba. Suna tafe, sai wannan yarinya ta ce za ta sauka. Bayan ta sauka ne, mai babur din yake cewa abokinsa ai budurwar ga irin wayar da take riƙe da ita.
Buɗar bakin da abokin zai yi, sai ya ce. "Ai ba ka gaya mun ba, amma wallahi da mun kwace ta."
Jin haka ƙanina ya ce akwai mai sauka, nan ya sauka daga babur ɗin.
Wannan ita ce irin rayuwar da matasanmu ke faɗawa. Shin a haka za mu cigaba, shin me zai faru nan da shekaru ashirin masu zuwa?
Dole mu sake tunani matuƙar muna son samun mafita.
Ana bawa mutane shawara akan yadda za su kare kan su, amma gaskiya abin ya wuce haka. Dole masana da shugabanni da duk.masu ruwa da tsaki su zauna babban taro da zai waiwayi matsalar da muke ciki, a tattauna tare da fitar da hanyoyi na ilimi da za a magance matsalar matasa. Sannan dole a zaɓi mutane da za su iya aiwatar da abin da aka fitar a bayan taron.
Duk inda za a kai a kawo, sai an yi ƙoƙarin kyautata zamantakewar mu, sannan a tsara yadda 'yan boko da masu arziƙi da talakawa za su fahimci juna, su yi aiki tare.
Dole ne mu fitar da yadda matasanmu za su samu ilimi da sana'oi. Mutumin da ya shekara sittin ko sama, idan bai samu abin da zai ci ba, zai yi wuya ya ɗau makami. Domin ba shi da ƙarfin jiki da zuciyar da zai yi haka. Amma matashi mai jini a jika, abu ne mai sauƙi a gun sa.
Zaharaddeen Ibrahim Kallah
zikallah@gmajl.com
Twitter/Instagram @zikallah
No comments:
Post a Comment