Friday, 2 October 2020

Shekaru Sittin Da Samun 'Yancin Kai A Najeriya: Daga Ina Aka Fito, Ina Aka Dosa?




Najeriya na daga cikin ƙasashen da Turawan Birtaniya suka yi wa mulkin mallaka, tare da bautar da su da ƙaƙaba musu haraji da kowanne baligi yake biya. 


Tun lokacin da ake gudanar da cinikin bayi, Turawan na haurowa nahiyar Afirka don sayen bayi da suke tafiya da su Turai don yin aikatau a gonakinsu da sauran manyan ayyuka. 


A lokacin da aka fara samun cigaba a duniya a ɓangaren masana'antu (Industrial Revolution), an fahimci cinikin bayi dole ya zo ƙarshe, domin injina sun maye gurbinsu a gurin aiki, sannan ɗaukar nauyinsu ma wata wahala ce. Wannan ne ya sa Birtaniya a karar kanta ta haramta cinikin bayi, sannan ta cigaba da yunƙurin saura ƙasashe su amshi wannan ƙudiri, wanda shi ne ya kawo ƙarshen cinikin bayi a duniya.


Amma ba a nan gizo ke saƙar ba, an shiga wani sabon salon cinikin bayi, wato mulkin mallaka, inda manyan ƙasashen duniya suka yi amfani da ƙarfinsu na soja wajen shiga nahiyoyin Afirka da Asia, suka mulke su don cigaba da faɗaɗa mulkin ƙasashensu. 


Kamar yadda masana suka faɗa, Turawan Birtaniya sun shigo Najeriya ne da zummar amfana da ɗinbin arzikin dake shimfiɗe a ƙasar na kayan amfanin gona da ma'adinai, wanda za su same su a arha, saɓanin yadda suke kokowarsu a ƙasashensu.


Wani abin kuma, idan sun sarrafa waɗanna kaya, akwai kasuwar da za su dawo da su a sayar. Idan suka ɗebi gyaɗa da auduga da koko, za a fitar da dangin mai iri-iri, da yadiddika da kayan shaye-shaye, a sake dawo da su Najeriya a sayar.


Turawan Birtaniya sun shigo Najeriya a 1900 tare da yin mulki daga bayan fagge (indirect rule), ta hanyar amfani da shugabannin gargajiya da suka tarar akan mulki. 


Haka nan, don jin daɗin mulkin nasu, Turawan Birtaniya sun haɗa aure tsakanin mutanen Arewa da Kudu wato (Amalgamation) a 1914. Wannan ya basu damar haɗa kan yankunan guda biyu, wajen mulkarsu cikin sauƙi.


Wannan aure an yi shi ne ba tare da la'akari da al'adu da addinai na mazauna waɗanna yankuna ba, balle kuma a kalli ɗinbin ƙabilun da suke yankunan.


An gina titunan dogo na jiragen ƙasa domin su samu ɗebo amfanin gona da ma'adinai daga loko da saƙo na ƙasar, zuwa bakin teku, don haurewa da su zuwa ƙasashen Turai.


Da tafiya ta yi nisa, mutanen Najeriya suka dinga samun ilimi da wayewa, musamman 'yan kudancin ƙasar da aka fifita ta fuskar ilimi. Hakan ya sa aka  fahimci lokaci ya yi da yakamata mutanen Najeriya su karɓi mulkin ƙasarsu. Wannan ya sa mutanen kudu suka fara yunƙurin karɓar mulki, wanda mutanen arewa a lokacin ba su goyi bayan haka ba, saboda sun fahimci ba su da 'yan boko da za su taka rawa a sabuwar Najeriya. Wannan ya sa suka yi turjiya, har sai da suka gamsu lokacin da ya dace a karɓi mulki. 


Wannan turjiya ta cigaba da rura wutar gaba tsakanin yankunan guda biyu, tare da yi wa juna kallon hadarin kaji.


A 1 ga watan Okbota,1960 aka yi bikin miƙa mulkin Najeriya ga 'yan ƙasa, don mulkar sabuwar Najeriya 'yantatciya. A wannan lokaci ana da yanki guda uku: Yankin Arewa da Yankin Kudu Maso Yamma, sai kuma Yankin Kudu Maso Gabas. Amma, bayan wasu shekaru saboda rigimar siyasa, aka sake ƙirƙirar Yankin Tsakiya na Kudu Maso Yamma.


Najeriya ta taso cikin karsashi da gasar kowanne yanki ya tsere sa'a a ɓangaren cigaba. A wannan lokaci an yi hasashen akwai ƙasashe gudu uku masu tasowa da za su yi fice a duniya ta ɓangaren ilimi, masana'antu, kasuwanci da ƙere-ƙare. Waɗannan ƙasashe sune, Najeriya da Indiya da Brazil.


Shekara shida bayan samun 'yancin kai, aka rusa harsashin sabuwar Najeriya ta hanyar kashe shugabannin siyasa da na sojoji da yawanci suka fito daga Arewa da wasu yankunan Najeriya tare da hamɓarar da jamhuriya ta farko.


Waɗanda suka yi wannan ta'asa, yawanci sun fito ne daga ƙabilar Ibo dake yankin kudu maso gabas ta Najeriya. Wannan shi ya yi sanadiyar shigowar sojoji, inda suka karɓi mulkin Najeriya, ƙarƙashin Janar Aguiyi Ironsi. 


Amma wata shida bayan wannan ta'asa, sojojin Arewa suka yi wani juyin mulkin ɗaukar fansa. A wannan karar sun hambarar da gwamnatin soja da Janar Ironsi ke mulka.


A dalilin haka ne, Janar Yakubu Gowon ya hau mulki ƙasar Najeriya. Sai dai wasu daga ƙabilar Ibo sun ƙi  miƙa wuya ga mulkinsa, suka yi tirjiya tare da barazanar ɓallewa daga Najeriya. 


Waɗanna mutane da Kanal Ojukwu ke wakilta, a ƙarshe suka bayyana ɓallewarsu daga Najeriya, tare da kafa ƙasarsu mai suna Biyafara. Wannan shi ya yi sanadiyar yaƙin basasa a ƙasar. 


Wannan yaƙi ya ɗauki tsawon wata talatin ana fafatawa, wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban rayuka da dukiya mai yawa.


Najeriya ta cigaba da shiga ƙalubalen rayuwa iri-iri da suka shafi na tattalin arziƙi, rikicin addinai da na siyasa da matsalar rashawa da cin hanci tare da rashin shugabanci ingantatce. 


A yau ana bikin cikar Najeriya shekaru sitti da samun 'yancin kai, wanda a al'adar rayuwa ya kai lokacin da zai mori abin da ya shuka. Ma'ana, Najeriya ta kai lokacin da za ta mori gumin da ta sha na tsawon shekaru. Domin 'ya'yan da ta haifa ma kafin 'yancin kai da yawansu sun yi ƙaura, ba a maganar wanda suka yi wasa tare.


A wannan lokaci da ake wannan bukukuwa, ƙasar ta samu cigaban a wasu fannoni da dama. An samu yawaitar makarantu manya da ƙanana, an samu ƙarin yawan asibitoci da faɗaɗar birane. A yanzu haka ana hasashen yawan al'umar Najeriya ya doshi miliyan ɗari biyu. Wannan yawa na al'umma Najeriya yana ƙarawa ƙasar ƙima, inda ƙasashen duniya kan yi ƙoƙarin kutso kai don ko ba komai akwai kasuwa.


Amma a wannan lokaci da ake ciki na cigaban duniya, ina Najeriya ta dosa ne? Koda ba a rusa harsashin da magabata suka dasa ba, kamata ya yi a wannan ƙarni a ce an fahimci ina ake a ƙasar da inda aka dosa. Domin an shiga wani sabon lale na yadda ake tafiyar da duniyar. Su kan su ƙalubalen da ake fuskanta sun sha banban da wanda al'umar baya suka fuskanta.


Shin wane tsari ne aka yi wa ƙasar da ake burin cimmawa? Tsari da zai kawo wani tsani da ƙasar zata tattaka har ga inda ake burin zuwa.


A lokacin shugaban ƙasa Janar Sani Abacha, ya fito da tsari na Vision 2020, wanda da an tafiyar da shi yadda aka tsara a wannan shekara da ake bikin shekara sitti za a kai ga ƙololuwar ribatar abin da aka shuka.


Shin haka za a ta yin gwamnatoci, kowa ya zo da tsarinsa, idan ya gama ya tafi da abin sa babu ɗorawa ko cigaba? A baya mun ga yadda aka yi wasu tsare-tsare irin su Green Revolution da Operation Feed the Nation da Structural Adjusment Programme (SAP), da Seven Points Agenda. Dukkanninsu ba su bada ainahin abin da ake buƙata ba.


A yanzu maganar da ake shugaba, Muhammadu Buhari ya kafa kwamiti da zai tsarawa ƙasar wani sabon harsashi da za a ci moriyarsa a 2050. Shin ta ya ya za a tabbatar wannan yunƙuri zai haifar da ɗa mai ido, tun da a karatun baya babu riba a tsare-tsaren da aka gudanar? Ai ba a kai ga cin moriyarsu ba aka yi watsi da su, duk da uwar dukiyar da aka narka akansu.


Shi kenan haka za mu ta yin bundun-bundun muna lalube a duhu, bayan muna cikin ƙarni na ashirin da ɗaya da komai ana yin sa bisa doren ilimi da lissafi? Shi kansa tsarin mulkin ƙasa mun ɗauko tsari Birtaniya na Parliamentary, daga baya aka watsar da shi aka koma tsarin Presidential. 


To shi kansa tsarin Amurka na Presidential, wanda ake da shugaba mai cikakken iko ba mu iya gudanar da shi ba yadda yakamata. Domin a tsarin, koda shugaba na da iko bai isa ya rusa wani tsari da aka gina ƙasar akai ba. A yau shugaban Amurka duk jin ikonsa, bai isa ya aiwatar da wani ƙudiri da ya sauka akan turbar da aka gina Amurka ba, koda kuwa daga wacce jam'iyya ya fito. 'Yan majalisu ba sa zama 'yan amshin shata kamar yadda namu suke.


Haka baiwar da Allah ya yi wa Najeriya za ta tafi a banza? Haka za a banzatar da arziƙin al'umma da ƙasar noma da ɗinbin ma'adinai, sai dai wasu su sha bunƙasa daga arziƙinmu. 


Ƙasashen da ake sa mu a layi ɗaya a ɓangaren cigaba irin su Indiya da Brazil sun sha gabanmu fintinkau. An wayi gari can muke zuwa neman ilimi da lafiya da kasuwanci tare da yawon buɗe ido. Hatta ƙasashe irin su Dubai da Malesiya sun zama abin misali a fagen cigaba.


A yau muna gudanar da mulkin siyasa a Najeriya, amma sai ya zamo mun fahimci siyasar a baibai. Komai mun maida shi siyasa, da abin da ya dace da wanda bai kamata siyasa ta shiga ba. Siyasa a harkar tsaro, siyasa a harkar aikin gwamnati, siyasa a makarantu, siyasa a gurin zaɓen cancanta. A tsawon wannan lokaci, waɗannan matsaloli sai ƙaruwa suke.


Cutar kai da rashin yin abin da ya dace ta sa mun wayi gari mun tsinci Talatarmu a Laraba. Lalacewar tsaro ta yi tsamari, 'yan tada ƙayar baya sun addabi ƙasar. Fashi da makami da garkuwa da mutane ya yawaita. Cin hancin da rashawa sun zama ruwan dare, talauci da masu zaman banza sai ƙaruwa yake. Rashin imani a zuciya da lalacewar tsarin gudanar da mulki shi ma ya dabaibaye ƙasar. 


A wannan lokaci da ake bikin cikar shekaru sittin da samun 'yancin kai, ya zama wajibi ga wanda jagorancin ƙasar yake hannunsu su sake lale. Dole ne a yi kallo da idon basira tare da amfani da ilimi wajen sauyawa ƙasar alƙibla. 


Ƙasar Najeriya na gaba da kowa, makomarta ce farkon abin dubawa ba masalaha ko burin wasu ba. Yakamata kwamitin da shugaban ƙasa ya kafa na samar da mihimman tsare-tsare ya ƙunshi mutane da yawa dake da ruwa da tsaki akan turakun ƙasar da sauran ɓangarorin gudanarwa da suka shafi al'umma.


Dole idan wannan tsari ya fito ya zama doka kuma wajibi a aiwatar da shi, koda kuwa za a samu sauyin gwamnati. Allah ya taimaki Najeriya ya ɗaukakata a duniya.


Zaharaddeen Ibrahim Kallah

zikallah@gmail.com

Twitter: @zikallah

No comments:

Post a Comment