Na taɓa sauraron lackcar Ɗan Masanin Kano, marigayi Dr. Yusuf Maitama Sule a kan rahoton wani Bature da ya zo ƙasar Hausa. Baturen na magana cewa ya je wata alƙarya mai abin mamaki, wanda saboda zaman lafiyarta idan za ka ɗorawa tsohuwa kwaryar gwal za ta taka a ƙasa daga farko gari har ƙarshensa ba tare da an tare ta ba an kwace.
Wannan shi ne tarihin ƙasar Hausa. Duk da cewa ƙasar na da nata ƙananan matsalolin tsaro, ba a taɓa mafarkin samun ƙalubale na tsaro da take ciki ba. A yau garjejen ƙato ne za a yi wa kwace a bainar jama'a a cikin birni kamar na Kano.
Masana kan yi hasashen matsalolin makamantan irin waɗanda muke ciki tun kafin su zo. Wataƙila saboda nazarin yadda duniya take tafiya da abin da zai kai ya komo. Irin waɗannan hasashe na ba wa hukumomi dama su shirya ga wasu ƙalubale, yadda tun kafin su zo an tanadi maganinsu.
Misali, gobara ba a fatan ta, amma hukuma kan tanadi motocin kashe gobara da kayan aiki saboda zuwanta. An ce lokacin da za a ƙaddamar da hukumar kashe gobara a Arewa, Sardaunan Sakkwato, Sir Ahmadu Bello ya cewa ma'aikatan cewa aikinsu na da matuƙar muhimmanci. Amma Allah kar ya kawo ranar aikin su. Wannan gaskiya ce, ba a buƙatar aikin su, amma tabbas wata rana za a buƙaci aikin nasu.
A wajen 1996 na taɓa rubuta wani littafi da ake garkuwa (kidnapping) da 'yar tauraron littafin. An zuba labarin ne a tsakanin shekara to 1991 zuwa 1992. Malam Bala Anas Babinlata da ya yi nazarin littafin a lokacin da nake rubutawa, ya kalli ɗabi'ar garkuwa da mutane ko kidnapping a matsayin baƙuwar al'ada da babu ita a Najeriya. Yau maganar kidnapping ba sabon labari ba ne a Najeriya.
Ƙasa kamar Najeriya da take da tarin al'umma da kwararru a ɓangarorin rayuwa, bai kamata a dinga yin abubuwa da ka ba. Idan za mu yi kwaikwayo, ya kamata mu yi bisa tsarin al'ada da zamantakewarmu. Ko kuma mu zamanantar da namu yadda za su dace da tsarin mu.
A yau mun yi watsi da tsarin tsaro na gargajiya da muka gada, iyaye da kakanni. Tsarin da ba mu san ɗaruruwan shekarun da aka gina shi ba. Abin takaicin shi ne ba mu iya kwaikwayon tsarin Turawan da muka aro ba yadda ya kamata. Eh mana, haka tsarin tsaro na ƙasashen Turan yake?
Babu ma'aikata babu kayan aiki, babu tsarin aiki ingantacce. Bayanai da ake tattarawa na mutane ba a iya amfani da su ta hanyar da ta dace. A Najeriya bankuna ne kawai kan kwatanta amfani da bayanai, su ma saboda harka ce ta jari hujja da duniya ta kawo.
Idan ka kalli harkar zaɓe a Najeriya da aka zuba kuɗade masu nauyi, bayanai na mutane da ake ɗauka ba a iya amfani da su. Yawanci sai mutum ya je kaɗa ƙuri'a sai a ce bayanansa ba su fito. Zai wuya ka je banki a kasa fitar da bayananka. To ko hukumomi ba da gaske suke ba ne?
Na saurarin Gwamnan Sokoto, Hon. Aminu Tambuwal yana kokawa kwamiti da shugaba ƙasa ya tura jiharsa halin da ake ciki na rashin ma'aikata da za su kare mutane sama da miliyan 200 a Najeriya.
Allah ya yi mana baiwa amma ba mu san yadda za mu more ta ba. Idan har muna so mu ga daidai dole ne mu kawar da son zuciya a nemi mutane da suka dace. Duk irin mutanen da ake buƙata a Najeriya ana da su.
Dole mu yi tunanin yi wa rashawa da cin hanci garanbawul. Tana daga cikin dalilan da ya sa ba a barin waɗanda suka dace su ja ragamar al'umma su samu gindin zama.
Daga
Zaharaddeen Ibrahim Kallah
Zaharaddeen Kallah marubuci ne, kuma tsohon shugaban Ƙungiyar Marubuta Ta Najeriya (ANA), reshen jihar Kano.
No comments:
Post a Comment