Saturday, 19 February 2022

Mijin Budurwa




Sunanta Hafsat Zakariyya, babarbarriya ce yar usuli. Tana da tsayi sannan ba ta da jiki sosai. Duk da cewa ba fara ba ce ba za a kira ta baƙa ba, domin tana da hasken fata; irin fatar da  Turawa ke kira launin cakulet. Kyakkyawa ce ajin farko, amma wannan kyau ya disashe, fararen idanunta dake zama abin so ga masu kallon su sun rikiɗe sun koma jajir. Gaba ɗaya ta rame ta fita hayyacinta kamar ba ita ba.   


Hotunansa da rubuce-rubucen sa dake zama abokan hirar ta, ta tattara ta kulle su duk saboda baƙin ciki. Zanna Bulama masoyinta da take burin aure, suna son junansu matuƙar so. Shi ne masoyin da ya fara karanta mata karatun so ya kuma ɗora ta a bisa turbar soyayya. Amma kash, ya rage sati biyu a yi bikinsu, Allah Ya karɓi ran Zanna, sakamakon haɗarin mota. 


Wannan shi ya hargitsa tunanin Hafsa, ya sauya rayuwarta. A koyaushe mutuwar kan        koma mata sabuwa fil; har wasu mutane na tsegumi kamar ita ma ta mutu ne; idan aka yi la'akari da yadda komai na ta ya sauya kuma ba sauƙi bare dangana.


Ruwan ƙwalla masu ɗumi suka zubo daga idanunta suka bi kumatunta suna zuba a kan matashin kai da take kwance. Cikin shasshekar kuka  take cewa, Masoyi kana ina, ko kana ji  na, shi kenan ka tafi, ba za ka dawo ka ganni ba. Hawayen ya cigaba da fita da sauri.


Zanna Bulama shi ma babarbare ne haifaffen Maiduguri. Matashi ne da bai wuce shekara talatin ba, kuma ƙwararren marubuci ne da yake rubutu cikin harsunan Ingilishi da Hausa. Asali ma shi ne wanda ya cusawa Hafsa sha'awar rubuce-rubuce. Sun gama tsara rayuwarsu da irin zaman da za su yi tsakanin miji da mata, da yadda bikinsu zai kasance da yayan da suke son haifa. Amma duk wannan buri ya zama tamkar gajimare a sararin samaniya da ba shi da ruwa.


Tafiya ta yi tafiya, alamarin Hafsa babu sauƙi kamar ciwon arne. Wannan ya ƙara tayar wa da iyayen Hafsa hankali. A baya kowa a danginta ya san Bakura, ɗan Aminin mahaifinta na matuƙar son ta, amma saboda Zanna ya karɓi mukullin zuciyarta, Bakura ya haƙura. Wannan hali da take ciki ne ya sa iyayenta tunanin aurar da ita ga Bakura. A ganinsu wannan hanya ce da za ta rage ma ta baƙin ciki. 


Amma ita Hafsa ta nuna ƙin amincewarta. A ganinta ta gama soyayya da wani ɗa namiji, kuma kamar ta ci amanar Zanna ne idan ta saurari wani. 

Cikin kuka take cewa, Ka tafi ka barni, yanzu za ka so wani ya aure ni alhali ni ce matarka da kake buri? Ta girgiza kai. Zanna ba zai yuwa ba, na san kana fushi da ni matuƙar wani ya karɓi zuciyata.”


Ina son ki gane zamanki ba zai yu wu haka ba, ba za mu zuba miki ido ba. Tun da kin ƙi ki ɗauki ƙaddara, na riga na yanke shawara ko kin amince ko ba ki amince ba, zan auran da ke ga Bakura. Domin haka shi ya fi dacewa da ke. Kalamin da ya fito daga bakin mahaifinta kenan bayan ya sa an kirawo ta babban ɗakin hutawarsa. 


Wannan ya sa zuciyarta ta dinga bugawa, numfashinta na tasowa sama, a daddafe ta rarrafa ta koma ɗakinta tare da faɗawa kan gado.  Nan take ta ɓarke da wani sabon kukan. Mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, nan take tunanin Zanna ya dawo ma ta sabo, ta shiga yi wa kanta tambayoyi a zuciyarta. 


Shikenan sai ta je ta auri wani wanda take ganin tsarin rayuwarta bai zo ɗaya da na shi ba. Zanna ne wanda ya ɗanɗana ma ta so, shi ne wanda ganinsa yake faranta ma ta rai, wanda yake jin ta har cikin jinin jikinsa. Duk wannan ya zama tamkar mafarki?


A wannan yanayi ne ta tuna da wata rubutacciyar waƙa da Zanna ya taɓa rubutawa mai taken Mijin Budurwa, waƙa ce da ya taɓa rubuto ma ta ita a lokaicn da ta yi fushi da shi, yayin da wata budurwa yar rigima ta taɓa cewa tana son sa. Nan ta fara tuna wasu baituka da suka daɗe a cikin ƙwaƙwalwarta.


Ni na miƙa wuya,

A yau sauraran ki nake,

Ko ki yarda ko ki ƙiya,

Ƙauna ta gare ki take.


Ni ne mijin budurwa,

Budurwar Hafsa take,

Mabuɗin soyayya ta,

Ai gurin ki yake.


Ita ma rayuwata,

Bisa soyayyar ki take,

A yau idan babu ke

Tabbas mutuwa nake.


Nan Hafsa ta sake fashewa da sabon kuka. Shin tana ganin ita son na ta bai cika ba. Domin babu Zanna amma ita tana nan a raye, har za ta auri wani. Zanna a waƙarsa yana cewa, shin ne mijin budurwa, kuma budurwar Hafsa take. Nan ta cigaba da girgiza kai, ta gamsu a yanzu ne ya zam mijin budurwa, amma Bakura ba mijin budurwar Zanna ba ne.


An doshi wata shida da mutuwar Zanna, alamarin sai ƙara zafi yake. Mahaifin Hafsa ya tsaya kai da fata sai an aurar da ita ga Bakura. Hafsa kuma ta ƙi amincewa. Cikin wannan hali ne a gidansu aka rabu gida biyu, wasu suna ganin a bar Hafsa ta koma makaranta, a ganinsu wannan zai sa ta samu sauƙin damuwarta, yin haka zai sa a yi nasara cikin sauƙi. Ɗaya ɓangaren kuma suna masu goyon bayan auren ta da Bakura ba tare da jinkiri ba shi ne mafita. 


Shigowar Burema wato babba yaya a gurin mahaifin Hafsa ya sa wa wutar ruwa, inda ya yanke hukunci Hafsa za ta koma Kano gurin antinta Hasana don ci gaba da karatu. Anti Hasana ya ce ga Burema, tana auren Hashim, wani babban maaikacin banki da ya daɗe yana zaune a Kano.


Sati uku kenan da fara karatun Hafsa a Kano, tana karanta ilimin harshen Hausa da Ingilishi a Kwalejin Kumbotso. A tsawon wannan lokaci ba ta hulɗa da kowa, hatta mata yanuwanta sallama ce kawai a tsakaninsu. Idan ba ta ɗakin ɗaukar karatu za ka gan ta ware tana bitar karatunta. Wani lokacin kuma ta kan shiga kogin tunani har da kuka idan ciwon da ke damfare a zuciyarta ya motsa. Haka rayuwarta ta cigaba a Kano, har ta zama yar gari. Kwanci tashi har ta samu wata biyu da fara karatu a Kano.


**************

Ranar wata Juma'a ce za ta makaranta, tana cikin tasi. Direban ya kunna rediyo yana sauraron tashar Rediyon Kano. Ba su jima suna tafiya ba mai gabartarwa ya sako wata rubutacciyar waƙa da wani marubuci ya rubuta ya kuma rera kayarsa.


A hankali waƙar ta isa ga ƙwaƙwalwarta, nan take sai ta  rikice. Ya Salam, mene ne a ciki da ya dunguza ta? Waƙar tana tafe a hankali kamar haka:

Ya Hayyu ya ƙayyumu,

Shi muke roƙo kullum,

Don Shi ke ƙulla soyayya.


A yau ina so ki sani,

Zuciyata na neman tsani,

Don yin ƙoli a soyayya.


Ai ita budurwa,

Allura ce cikin ruwa,

Da so ko babu soyayya.


Mai rabo kan ɗauka,

A fili ko a ɗaka,

Don haka ne muke soyayya.


Allah ne ya san mijin budurwa,

Amma zan yi iyo cikin ruwa,

Na lalubo ki ya masoyiya.


Nan fa aka famo mata ciwon da ya daɗe a zuciya. Hawaye kuwa ya dinga zuba kamar an ɓalle gulbi. Ba ta dawo hayyacinta ba sai da direban tasin ya juyo ya ce.

Hajiya, ba a nan za ki sauka ba? 


Ba ta san an kawo makarantar ba, don ta faɗa kogin tunani. Ta fidda kuɗinsa ta biya shi sannan ta shiga makaranta tana tafe a hankali kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki. 


A ranar nan karatun da ba ta yi ba kenan. Shin wane ne wannan marubuci da muryarsa take tafiya kamar ta Zanna? Wane ne wannan da yake amfani da wasu kalamai da suka yi shige da wanda aka taɓa gaya mata a baya? Wannan tunani shi ya dinga shiga ƙwaƙwalwar Hafsa yana shawagi, nan ta ɗokanta ta san wannan marubuci. To ta yaya hakan za ta yiwu, bayan waƙa ce ta ji a gidan rediyo, hasali ma ba ta ji  sunan wanda ya yi waƙar ba.

Ba a tashi ba ta fice daga makarantar, ba ta zame ko ina ba sai gidan Rediyo. 

Kina buƙatar a yi miki kwafin waƙar ne? Maaikacin da ta samu ya  buƙaci ji bayan ta yi tambaya a kan waƙar da aka sa.

Ta gyaɗa kai. Ina buƙata, amma fa ina so in san wane ne marubucin da kuma inda zan same shi.


Mutumin ya yi shiru na ɗan wani lokaci, sannan ya  ce. 

In dai waƙar da kike nufi ce, wani marubuci ne da ake kira Abba Major ya rubuta ta, sannan ya rera kayarsa. Matashin marubuci ne da ya yi suna a garin nan, amma ni kaina ban san shi ba a zahiri. Duk waƙoƙinsa muna samunsu ne ta hannu shugaban gidan rediyon nan, wanda suke da alaƙa sosai. Sai dai shi shugaban namu ya yi tafiya ƙasar waje a halin yanzu, ban san ko yaushe zai dawo ba.”


Ya sake yin shiru yana kallonta kafin ya cigaba. Amma dai na taɓa ji an ce yana cikin Ƙungiyar Marubuta Ta Najeriya (ANA) reshen Jihar Kano. Su kuma ofishinsu yana ɗakin karatu na Murtala Muhammad, dake kan titin Ahmadu Bello. Ina fatan kin san gurin?

Ta gyaɗa alamun ta sani duk da cewa ba ta taɓa zuwa wajen ba. 


Yauwa, ina ganin idan ki ka je can za su ba ki cikakken bayani.

Ta yi murmushi. 

Na gode ƙwarai, ya maganar kofin waƙar?

Ya miƙe. Wannan ba damuwa, idan kika ba ni nan da minti goma za a samo miki.


Daren wannan rana ba ta samu barci ba, domin kaset ɗin waƙar Abba  Major ne ya mamaye gurbin barcinta, da ya ƙare sai ta sake dawo da shi baya. Kashegari, ba ta samu farkawa ba sai da rana ta fito sosai. A gurguje ta shirya tana so ta tafi ɗakin karatu na Murtala Muhammad don neman bayani. 


Ta gama karyawa za ta fita sai ga Bakura ya zo gidan. Wani abu mai kama da gayan fura ya tokare mata a wuya don haushi. Ta san cewa kafin ta yakice shi ta tafi inda za ta, abin da wuya. Aikuwa kamar carbi ya tsinke ya shiga zuba ratatatta ba sayawa. Ta yi saa a wata gaɓa ta jefa masa waigi, To ni fita zan yi.


Ya yi murmushi. To mu je na kai ki, ba makaranta za ki ba?

Ta girgiza kai. 

Na gode ba makaranta za ni ba.

To Hafsa ko ina za ki ai ba kya ƙi na kai ki ba. 


Da kyar ta amince su ka fito a motarsa. Bayan sun fito daga gida ne ya dube ta ya ce. 

Ina za ki ne?

Ahmadu Bello Way za ka kai ni, ka san titin? 

Ya yi dariya Hafsa ai ba yau na fara zuwa Kano ba, ko kin manta Jamiar Bayero na yi? 


Ta ɗan yamutse fuska. Ka yi haƙuri, na manta.

A ina a Ahmadu Bello Way? Ya buƙaci ya ji.

“Murtala Muhammad Library za ka kai ni.

Okay, ashe karatu za ki.


Ba ta ƙara cewa komai ba, haka ake tafiyar iyakarta daga e, eh sai gyaɗa kai har suka zo ɗakin karatun. Tangamemen gini ne hawa huɗu, wanda ganisa ya sa ta cikin mamaki kasancewar duk girmansa an tanade shi ne don gudanar da karatu da bincike. Lalle Kano sai Kano, ta ce a ranta.


Ya ja birki ya tsaya a gurin ajiye mota. Hafsa ina iya biyo ki? Ya tambaya tare da kallon fuskarta.

Ka biyo ni, Ta nanata, Ba karatu na zo ba kenan.


Ya fashe da dariya, To shi kenan, yaushe zan dawo in ɗauke ki?

Ba ni da tsayayyen lokaci, don haka na hutaasshe ka. Ta buɗe ƙofa ta fita.

Ni dai zan zagayo. Ya ce yayin da ya sa giya.


Kanta tsaye ta nufi ƙofar shiga gabanta yana dukan  uku-uku, hanunta riƙe yake da wasu littattafai guda biyu sai jaka da ta rataya.


Ta yi sallama yayin da ta isa bakin reception ɗin. Wani mutum ne dogo ga faffaɗan ƙirji da tsare gira yake zaune a gurin. 


Don Allah ofishin ƙungiyar marubuta nake tambaya?

Mutumin ya yi nuni da yatsansa sama. 

Sama za ki hau hawa na uku daga ɓangaren dama a nan ofis ɗin na su yake.

Na gode. Ta ce sannan ta juya ta nufi inda matattakala take da sauri, tana ji a ranta kamar za ta ga Abban a can.

 

A daidai matattakalar hawa na biyu ne suka yi kiciɓis da wani matashin saurayi yana saukowa. Yana cike da ƙuruciya, fuskarsa cikin faraa  da anashuwa. Idonta ya kai ga fuskarsa, zuwa kwayar idanunsa. Ba ta san lokacin da ta kuskure sawunta ba, ta tafi rikica za ta faɗi, littattafan dake hannunta suka tarwatase a ƙasa. Cikin zafin nama matashin ya sa hanunsa ya riƙo ta, a lokacin ta ja wani gwauron numfashi.


Sannu! Sannu kin ji, ba dai ki ji ciwo ba ko?

Ta maido da numfashin, tashi ɗaya idanunta suka firfito. Ban ji ciwo ba, na na na gode. Ta ce cikin harɗewar harshe tare da haɗiyar wani yawu.


Ya sa hannu ya kwashe ma ta littattafanta da suka zube, ya miƙa mata.

Ta karɓa, Na gode, amma malam don Allah na tambaye ka?

Yi tambayarki Allah ya sa dai na sani.

Ta sake kallon shi. Kai mutumin Maiduguri ne?


Ya yi murmushi gami da girgiza kai. 

Aa, babu abin da ya haɗa ni da Maiduguri, ni ɗan Kano ne.

Shike nan da ma kana yi mini kama da wani ne, har muryar. Ta faɗa tana alajabi.

Allah Sarki.


Nan suka rabu ta hau sama shi ku ma ya yi ƙasa. Haƙiƙa Hafsa ta shiga cikin alajabi, domin a fizge saurayin da suka yi kiciɓis da shi yana ɗibar kama sosai da masoyinta Zanna. Sai dai shi ya fi Zanna tsayi, sannan yana da hasken fata da manyan idanu. 


A cikin tunani ta isa ga hawa na uku, ta yi dama har bakin inda ofis ɗin yake. A buɗe ta tarar da ofis ɗin, sai dai babu kowa a ciki, don haka sai ta tsaya a bakin ƙofa tana jira. Kusan minti biyar sai ga wani matashi baƙi mara jiki sanye da kaftani da hula ya nufo gurin da sauri. Bayan ya ƙaraso gurin ya ce. 

Yi haƙuri Hajiya, ba ki tarar da kowa ba ko, wallahi na hau sama ne. 

Ta yi murmushi, Babu komai, ai ban jima ba. 


Suka sake gaisawa bayan ta zauna, sannan matashin ya ce, Ko akwai abin da ki ke buƙata?

Ta gyaɗa kai. 

Eh, dama daga gidan Rediyo Kano aka turo ni nan. Da ma na ji wata waƙa ce da suke sanyawa, a jiya ma sun sanya ta. To na je gurinsu a kan ina so na san wannan marubucin waƙar. A can aka ce min sunansa Abba major; kuma yana wannan ƙungiyar taku. An ce dai idan na zo zan samu ƙarin bayani. To ban sani ba ko ka san Abban?”


Ya yi murmushi, Kayanki ya tsinke a gindin kaba. Abba ɗan ƙungiyarmu ne, sai dai bai jima da barin nan ba. Na san dai yau ba zai dawo ba. 


Suka yi shiru na wani lokaci zuwa can ya katse shiru da cewa, Sai dai in kina son ganin sa, to akwai taron Dandalin Marubuta da za a yi gobe Lahadi da safe, na san dole zai zo. Kina iya zuwa goben za ki gan shi.

To kamar ƙarfe nawa kenan, kuma a ina? Ta buƙaci ta ji.

Goma ake farawa, za a yi shi a nan gidan a babban hall dake ƙasa.

To na gode, goben Insha Allahu zan zo.

Sai kin zo.


A wannan rana ma ba ta samu nutsuwa ba, domin abubuwa ne suke faruwa da ita ɗaya bayan ɗaya. Haɗuwarta da saurayin da  ya riƙe ta da za ta faɗi da yadda yake magana ya sanya ta a tsohuwar gonar tunani. 


Wataƙila yanayi da ya ɗauka da Zanna shi ya ja hakan. A lokaci guda sai ta fara tunanin ko kwakwalwarta ta motsu ne, domin ta ji muryar mawaƙi a gidan rediyo ta kiɗime, sannan ga wani matashi ta gani ta rikice saboda yanayinsa da Zanna. Shin ko duk mutanen Kano kamar Zanna suke, anya ba idanuwanta ke gizau ba sannan kunnuwanta sun narke da kalaman marigayi? 


Gaba ɗaya sai tunanin Zanna ya sake bijirowa, ta dinga tuna abubuwan da suka faru, to yau ga shi ta haɗu da wani wanda yake yanayi da Zanna, yadda yake magana da yadda ya yi murmushi yayin da ƙwayar idanunsa ta haɗu da ta ta, duk sun haɗu sun sa ta a cikin wani hali wanda ita kanta ba ta san wane iri ba ne. 


Aa babu abin da ya haɗa ni da Maiduguri, ni ɗan Kano ne. Kalamin da matashin ya yi mata da yadda ya jefe ta da murmushi ta tuna. Da wannan tunani barci ya kwashe ta.


Kashegari, goma saura kwata a ɗakin karatu na Murtala Muhammad ta yi mata. Numfashinta ya fara ƙoƙarin ɗaukewa, yayin da zuciyarta ta dinga bugawa da sauri sannan jinin dake gudana a jikinta ya harba cikin sauri, a lokacin da ta yi arba da wannan saurayin da ya taimake ta a matattakalar bene. 


Shi kansa ya shaida ta, don shi ya fara ma ta magana, Ah, yau ma kin shigo gidan.

Ta yi murmushi, Wallahi na zo taron marubuta ne.

Okay, sannunki da zuwa. Ai ba a fara ba kin shigo da wuri, amma nan ba da daɗewa ba za a fara. Kya iya shiga daga ciki ɗakin taron.

A ina gurin taron yake? Ta tambaya.

Mu je na raka ki, ashe ba ki taɓa zuwa ba.

Yau shi ne zuwana na farko.”


Suka jera suna tafe, daga shi har ita wani abu na daban suka ji a tattare da su. Shi a ɓangarensa zuciyarsa ce ta dinga dukan uku-uku, duk da cewar ya sha yin muamula da manyan mata, amma bai taɓa jin yanayin da yake ji ba a tare da wannan yarinya mai kwarjini da cikar zati. 

Kina yin rubutu kenan? Ya tambaya.

Ta yi murmushi Na kan yi, amma dai ban yi ƙwari ba.

A hankali za ki yi.


A ɗakin taron mutanen da ke ciki ba su fi mutum biyar ba. Ya sama mata guri a inda mata suke zama tare da cewa.

“Sai kin ɗan yi haƙuri, ina ga za a kai 10:30 na safe kafin a fara. Kin san marubuta, ban sani ba ko rubutun dare da suke yi ne yake sanya su makara.”


Ta yi murmushi bayan ta zauna tare da cewa.

Babu komai. Amma dai Allah ya sa kuna tashi sallar asuba?

Shi da itan suka kyalkyale da dariya, dariyar da ba ta taɓa yin irinta ba tun da Zanna ya bar duniya. 

Suna yi mana, har da zikirin safe. Ya maida mata.


Kafin ya ƙara cewa komai, wani ya zo ya kira shi. Ga alama yana cikin shugabannin shirya taron. Haƙiƙa idan ka dubi fuskarsa bai so haka ba, wataƙila ya so su kasance tare har a fara taron. Tun da aka janye shi ba ta sake yi wa kowa magana ba, tana zaune ita kaɗai tana mamakin da hasashen yadda Abba Major zai kasance, har aka fara gudanar da taron.


Hafsa ta yi shiru tana sauraren yadda ake gudanar da Dandalin Marubutan, amma kuma a wani ɓangaren daga cikin zuciyarta tana tunanin a wane lokaci ya dace ta nemi wane ne Abba Major.


Yanzu za mu saurari wata rubutacciyar waƙa mai taken Taaziya’ daga bakin Abba Major. Wannan jawabin da shugaban taron ya yi shi ya ja hankalin Hafsa. 

Ta firfito da idanunta ta ga wane Abban da ta zo gani. A hankali ya taso ya ratsa cikin jamaa zuwa inda aka tanada don magana. 


Yayin da aka miƙa masa abin magana sai abin ya ba ta mamaki, ganin wane ne Abba Major. Saurayin da suka haɗu ne a jiya wanda a yau ma shi ya kai ta har inda ta zauna, tare da yin raha da shi, amma ba ta san shi ne take nema ba. Lalle biri ya yi kama da mutum, ta ce a cikin zuciyarta.


Bayan ya karɓi abin maganar ne sai ya fara da magana kamar haka. Assalamu Alaikum yan uwana marubuta. Kamar yadda kuka ji wannan waƙar ta wa sunanta ‘Taaziyya. Haƙiƙa waƙar na  rubuta don taaziyya ga abokina Zanna Bulama da Allah ya yi wa rasuwa. Ban samu labarin rasuwarsa ba, sai a watan da ya gabata. Allah ya yi masa rahama.

Ameen. Mutanen dake ɗakin suka amsa gaba ɗaya.


Nan ya shiga cikin waƙar ya dinga warwarar jigon ta. Ba ta san lokacin da ta fashe da kuka ba. Haƙiƙa tun sanda ya kira sunan Zanna gabanta ya faɗi, a yayin da kuma ya shiga cikin waƙar ne ta tabbatar Zannanta yake nufi, domin ya yanko labirinta da Zanna da labarin soyayarsu da rasuwarsa ana dab da bikinsu. Salon muryarsa da hawa da saukar baitin, kamar yadda Zanna yake rera waƙarsa ne.


Waƙar ta ratsa zukatan jamaar da ke gurin, sun yi shiru kamar ruwa ya ci su. Shasshekar kukanta sai ya ja hankalin jamaar dake gurin har aka dinga waigawa a ga mai kukan. Shi kansa Abba da ya hango ta ya tabbatar ya tayar mata da hankali. Haƙiƙa duk da ba wani saninta ya yi ba, ba ya son ya cigaba da wannan waƙa tun da ta rikita ta. Don haka ya nemi afuwa a gurin jamaa zai tsaya a nan duk da cewa bai ƙarasa ta ba. 


A lokacin Hafsa ta miƙe ta yi waje. Ganin ta fita shi ma Abba ya bi ta wajen. Ya same ta jingine da bango ta rufe fuskarta da gyalenta.

Malama ya kira a lokacin da ya zo gurin.

Ta ɗago ta dube shi, bayan ta yaye gyalen da ta rufe fuskarta. Idanunta sun yi jajur sosai a cikin ƙanƙanin lokaci. 

Ya ci gaba da cewa.

Ki yi haƙuri ban ji daɗi da ganin waƙar ta tada miki hankali ba.


Duk da kukan da ke tare da ita, bai hana ta yin tattausan murmushi ba, a lokacin da ta buɗe fuskarta tare da ganin Abba.

Abba, ni godiya zan maka saboda adduarka ga masoyina. Ko kaɗan kar ka damu da ganin ina kuka. Kawai ka tuna min da wani alamari da ya wuce ne. 


Cikin rashin fahimta ya sake dubanta tare da alajabi. 

Kina nufin kin san Zanna?

Ta gyaɗa kai gami da murmushi.

Ni ce Hafsa ɗin da ka ke magana a waƙarka. Abba tun daga ranar Jumaa da ta wuce abubuwa na mamaki ne suke faruwa da ni. Ranar Jumaa za ni makaranta na ji wata waƙa da ta yi nasaba da irin waƙoƙin da marigayi ya taɓa yi min. karin waƙar yana tafiya kamar yadda muryarsa ta ke, a ranar na kasa haƙuri na tafi gidan rediyo don sanin  wane ne wanda ya yi waƙar. Ta goge wasu hawaye da suka zubo mata kafin ta cigaba. 


“A can aka tabbatar mun Abba Major ne ya yi ta. Jiya na shigo nan don in neme shi, sai Allah ya haɗa ni da kai. Tun da na ganka sai na ga kamar marigayi, haƙiƙa ban taɓa ganin wanda ya yi kama da shi ba,  kamar ka. Mun rabu da kai na hau sama aka ce min Abba ya fita, amma in dawo yau. Ina shigowa yau da kai muka fara haɗuwa. Wai duk abin da ake, kai ne Abba Major da nake nema tun shekaranjiya. Sai ga shi ka nuna ka san marigayi wanda waƙarka ta nuna hakan.


Shi ma sai ya ji kamar ƙafafuwansa ba za su ɗauke shi ba, nan sai tausayinta ya ƙaru a zuciyarsa. Cikin murya mai cike da alhini ya fara da cewa. 

Zanna abokina ne; ta re muka gama Jamiar Ahmadu Bello Zaria. Haƙiƙa mun yi kama da juna matuƙa, wanda hakan shi ya ƙara danƙon zumunci da abotarmu. Domin mutane a makaranta kan yi zaton ko yanuwa ne mu. Kin san iko na Allah ya fi ƙarfin tunaninmu. 


“Ni da Zanna mun shiga ƙungiyar marubuta ta Jamiar Ahmadu Bello, a rana ɗaya kuma a nan muka samu aƙidar rubuce-rubuce. Hatta ɓangaren waƙa, mutum ɗaya ne ya horar da mu, wannan ya sa ki ka ji muryarmu ta zo kusan ɗaya.


Wasu hawaye suka sake biyo kuncinta, amma wadannan hawaye na farin ciki ne, domin masu sanyi ne. Cikin murmushi ta ce, Haba, shi ya sa jiya na ke tambayarka ko kai ɗan Maiduguri ne.


Ya ɗago ya sake duban idanunta. Duk da kukan da ta yi bai hana shi ganin hasken idanunta ba.

Hafsa yaya haƙuri?

Haƙuri Alhamdu Lillahi.

Allah ya ji ƙan Zanna, ya sa   Jannatul Firdausi makomarsa”.

"Ameen."


Zaharaddeen Ibrahim Kallah

dinik2003@yahoo.co.uk






Monday, 13 December 2021

Arewa Gidan Kara Da Mutunci

Na je gidan mai don shan mai, sai da aka gama zuba min, in kunna mota sai batir ya ce bai san zance ba. Aka tura gefe, wanda yake bi na a baya ya ce 'Bari a zuba min man in ba ka batir a tashi motar.'



Can wani mai mota 406 da shi ma ya sha mai, na ga ya yi fakin, ban san me yake ba sai ganinsa na yi ya ciro batir ɗin motarsa da sauri ya nufo mota, 'Buɗe gaban motar.' Ya ce.


Bawan Allah nan shi ya sanya batir ɗin, na tashi motar sannan ya mayar da nawa.


Idan ba a Arewa ba ina za a yi maka haka a Najeriya?


A wani zuwa Abuja da muka yi, muna neman wata hanya, muka tsaya muka tambayi wani mai acaba a gefen hanya. Mutumin sai hawa babur ya yi ya ce mu biyo shi, mun yi tafiya ta kai ta mil uku. Da ya nuna mana hanya sai ya ƙara mai, bai tsaya neman wani abu ba.


Amma a wata tafiya da muka yi zuwa wata jiha a kudu, babban titin gwamnatin tarayya ya ragargaje, wani lokcin sai direbobi sun sauka titi tare da ratsewa daji. Amma muna 'yar tafiya, sai ka ga matasa sun tare hanya. Sai an biya za a wuce, wai ba hanyar gwamnatin tarayya ba ce. Duk wani motsinka a irin wannan gurare sai ka biya.


Allah ya ƙarawa Arewa albarka.


Daga 


Zaharaddeen Ibrahim Kallah

TUN RAN GINI TUN RAN ZANE: MATSALAR TSARO A NAJERIYA

Na taɓa sauraron lackcar Ɗan Masanin Kano, marigayi Dr. Yusuf Maitama Sule a kan rahoton wani Bature da ya zo ƙasar Hausa. Baturen na magana cewa ya je wata alƙarya mai abin mamaki, wanda saboda zaman lafiyarta idan za ka ɗorawa tsohuwa kwaryar gwal za ta taka a ƙasa daga farko gari har ƙarshensa ba tare da an tare ta ba an kwace. 


Wannan shi ne tarihin ƙasar Hausa. Duk da cewa ƙasar na da nata ƙananan matsalolin tsaro, ba a taɓa mafarkin samun ƙalubale na tsaro da take ciki ba. A yau garjejen ƙato ne za a yi wa kwace a bainar jama'a a cikin birni kamar na Kano. 


Masana kan yi hasashen matsalolin makamantan irin waɗanda muke ciki tun kafin su zo. Wataƙila saboda nazarin yadda duniya take tafiya da abin da zai kai ya komo. Irin waɗannan hasashe na ba wa hukumomi dama su shirya ga wasu ƙalubale, yadda tun kafin su zo an tanadi maganinsu. 


Misali, gobara ba a fatan ta, amma hukuma kan tanadi motocin kashe gobara da kayan aiki saboda zuwanta. An ce lokacin da za a ƙaddamar da hukumar kashe gobara a Arewa, Sardaunan Sakkwato, Sir Ahmadu Bello ya cewa ma'aikatan cewa aikinsu na da matuƙar muhimmanci. Amma Allah kar ya kawo ranar aikin su. Wannan gaskiya ce, ba a buƙatar aikin su, amma tabbas wata rana za a buƙaci aikin nasu.


 A wajen 1996 na taɓa rubuta wani littafi da ake garkuwa  (kidnapping) da 'yar tauraron littafin. An zuba labarin ne a tsakanin shekara to 1991 zuwa 1992. Malam Bala Anas Babinlata da ya yi nazarin littafin a lokacin da nake rubutawa, ya kalli ɗabi'ar garkuwa da mutane ko kidnapping a matsayin baƙuwar al'ada da babu ita a Najeriya. Yau maganar kidnapping ba sabon labari ba ne a Najeriya.


Ƙasa kamar Najeriya da take da tarin al'umma da kwararru a ɓangarorin rayuwa, bai kamata a dinga yin abubuwa da ka ba. Idan za mu yi kwaikwayo, ya kamata mu yi bisa tsarin al'ada da zamantakewarmu. Ko kuma mu zamanantar da namu yadda za su dace da tsarin mu.


A yau mun yi watsi da tsarin tsaro na gargajiya da muka gada, iyaye da kakanni. Tsarin da ba mu san ɗaruruwan shekarun da aka gina shi ba. Abin takaicin shi ne ba mu iya kwaikwayon tsarin Turawan da muka aro ba yadda ya kamata. Eh mana, haka tsarin tsaro na ƙasashen Turan yake? 


Babu ma'aikata babu kayan aiki, babu tsarin aiki ingantacce. Bayanai da ake tattarawa na mutane ba a iya amfani da su ta hanyar da ta dace. A Najeriya bankuna ne kawai kan kwatanta amfani da bayanai, su ma saboda harka ce ta jari hujja da duniya ta kawo.


Idan ka kalli harkar zaɓe a Najeriya da aka zuba kuɗade masu nauyi,  bayanai na mutane da ake ɗauka ba a iya amfani da su. Yawanci sai mutum ya je kaɗa ƙuri'a sai a ce bayanansa ba su fito. Zai wuya ka je banki a kasa fitar da bayananka. To ko hukumomi ba da gaske suke ba ne?


Na saurarin Gwamnan Sokoto, Hon. Aminu Tambuwal yana kokawa kwamiti da shugaba ƙasa ya tura jiharsa halin da ake ciki na rashin ma'aikata da za su kare mutane sama da miliyan 200 a Najeriya. 


Allah ya yi mana baiwa amma ba mu san yadda za mu more ta ba. Idan har muna so mu ga daidai dole ne mu kawar da son zuciya a nemi mutane da suka dace. Duk irin mutanen da ake buƙata a Najeriya ana da su. 


Dole mu yi tunanin yi wa rashawa da cin hanci garanbawul. Tana daga cikin dalilan da ya sa ba a barin waɗanda suka dace su ja ragamar al'umma su samu gindin zama.


Daga

Zaharaddeen Ibrahim Kallah


Zaharaddeen Kallah marubuci ne, kuma tsohon shugaban Ƙungiyar Marubuta Ta Najeriya (ANA), reshen jihar Kano.

Friday, 2 October 2020

Shekaru Sittin Da Samun 'Yancin Kai A Najeriya: Daga Ina Aka Fito, Ina Aka Dosa?




Najeriya na daga cikin ƙasashen da Turawan Birtaniya suka yi wa mulkin mallaka, tare da bautar da su da ƙaƙaba musu haraji da kowanne baligi yake biya. 


Tun lokacin da ake gudanar da cinikin bayi, Turawan na haurowa nahiyar Afirka don sayen bayi da suke tafiya da su Turai don yin aikatau a gonakinsu da sauran manyan ayyuka. 


A lokacin da aka fara samun cigaba a duniya a ɓangaren masana'antu (Industrial Revolution), an fahimci cinikin bayi dole ya zo ƙarshe, domin injina sun maye gurbinsu a gurin aiki, sannan ɗaukar nauyinsu ma wata wahala ce. Wannan ne ya sa Birtaniya a karar kanta ta haramta cinikin bayi, sannan ta cigaba da yunƙurin saura ƙasashe su amshi wannan ƙudiri, wanda shi ne ya kawo ƙarshen cinikin bayi a duniya.


Amma ba a nan gizo ke saƙar ba, an shiga wani sabon salon cinikin bayi, wato mulkin mallaka, inda manyan ƙasashen duniya suka yi amfani da ƙarfinsu na soja wajen shiga nahiyoyin Afirka da Asia, suka mulke su don cigaba da faɗaɗa mulkin ƙasashensu. 


Kamar yadda masana suka faɗa, Turawan Birtaniya sun shigo Najeriya ne da zummar amfana da ɗinbin arzikin dake shimfiɗe a ƙasar na kayan amfanin gona da ma'adinai, wanda za su same su a arha, saɓanin yadda suke kokowarsu a ƙasashensu.


Wani abin kuma, idan sun sarrafa waɗanna kaya, akwai kasuwar da za su dawo da su a sayar. Idan suka ɗebi gyaɗa da auduga da koko, za a fitar da dangin mai iri-iri, da yadiddika da kayan shaye-shaye, a sake dawo da su Najeriya a sayar.


Turawan Birtaniya sun shigo Najeriya a 1900 tare da yin mulki daga bayan fagge (indirect rule), ta hanyar amfani da shugabannin gargajiya da suka tarar akan mulki. 


Haka nan, don jin daɗin mulkin nasu, Turawan Birtaniya sun haɗa aure tsakanin mutanen Arewa da Kudu wato (Amalgamation) a 1914. Wannan ya basu damar haɗa kan yankunan guda biyu, wajen mulkarsu cikin sauƙi.


Wannan aure an yi shi ne ba tare da la'akari da al'adu da addinai na mazauna waɗanna yankuna ba, balle kuma a kalli ɗinbin ƙabilun da suke yankunan.


An gina titunan dogo na jiragen ƙasa domin su samu ɗebo amfanin gona da ma'adinai daga loko da saƙo na ƙasar, zuwa bakin teku, don haurewa da su zuwa ƙasashen Turai.


Da tafiya ta yi nisa, mutanen Najeriya suka dinga samun ilimi da wayewa, musamman 'yan kudancin ƙasar da aka fifita ta fuskar ilimi. Hakan ya sa aka  fahimci lokaci ya yi da yakamata mutanen Najeriya su karɓi mulkin ƙasarsu. Wannan ya sa mutanen kudu suka fara yunƙurin karɓar mulki, wanda mutanen arewa a lokacin ba su goyi bayan haka ba, saboda sun fahimci ba su da 'yan boko da za su taka rawa a sabuwar Najeriya. Wannan ya sa suka yi turjiya, har sai da suka gamsu lokacin da ya dace a karɓi mulki. 


Wannan turjiya ta cigaba da rura wutar gaba tsakanin yankunan guda biyu, tare da yi wa juna kallon hadarin kaji.


A 1 ga watan Okbota,1960 aka yi bikin miƙa mulkin Najeriya ga 'yan ƙasa, don mulkar sabuwar Najeriya 'yantatciya. A wannan lokaci ana da yanki guda uku: Yankin Arewa da Yankin Kudu Maso Yamma, sai kuma Yankin Kudu Maso Gabas. Amma, bayan wasu shekaru saboda rigimar siyasa, aka sake ƙirƙirar Yankin Tsakiya na Kudu Maso Yamma.


Najeriya ta taso cikin karsashi da gasar kowanne yanki ya tsere sa'a a ɓangaren cigaba. A wannan lokaci an yi hasashen akwai ƙasashe gudu uku masu tasowa da za su yi fice a duniya ta ɓangaren ilimi, masana'antu, kasuwanci da ƙere-ƙare. Waɗannan ƙasashe sune, Najeriya da Indiya da Brazil.


Shekara shida bayan samun 'yancin kai, aka rusa harsashin sabuwar Najeriya ta hanyar kashe shugabannin siyasa da na sojoji da yawanci suka fito daga Arewa da wasu yankunan Najeriya tare da hamɓarar da jamhuriya ta farko.


Waɗanda suka yi wannan ta'asa, yawanci sun fito ne daga ƙabilar Ibo dake yankin kudu maso gabas ta Najeriya. Wannan shi ya yi sanadiyar shigowar sojoji, inda suka karɓi mulkin Najeriya, ƙarƙashin Janar Aguiyi Ironsi. 


Amma wata shida bayan wannan ta'asa, sojojin Arewa suka yi wani juyin mulkin ɗaukar fansa. A wannan karar sun hambarar da gwamnatin soja da Janar Ironsi ke mulka.


A dalilin haka ne, Janar Yakubu Gowon ya hau mulki ƙasar Najeriya. Sai dai wasu daga ƙabilar Ibo sun ƙi  miƙa wuya ga mulkinsa, suka yi tirjiya tare da barazanar ɓallewa daga Najeriya. 


Waɗanna mutane da Kanal Ojukwu ke wakilta, a ƙarshe suka bayyana ɓallewarsu daga Najeriya, tare da kafa ƙasarsu mai suna Biyafara. Wannan shi ya yi sanadiyar yaƙin basasa a ƙasar. 


Wannan yaƙi ya ɗauki tsawon wata talatin ana fafatawa, wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban rayuka da dukiya mai yawa.


Najeriya ta cigaba da shiga ƙalubalen rayuwa iri-iri da suka shafi na tattalin arziƙi, rikicin addinai da na siyasa da matsalar rashawa da cin hanci tare da rashin shugabanci ingantatce. 


A yau ana bikin cikar Najeriya shekaru sitti da samun 'yancin kai, wanda a al'adar rayuwa ya kai lokacin da zai mori abin da ya shuka. Ma'ana, Najeriya ta kai lokacin da za ta mori gumin da ta sha na tsawon shekaru. Domin 'ya'yan da ta haifa ma kafin 'yancin kai da yawansu sun yi ƙaura, ba a maganar wanda suka yi wasa tare.


A wannan lokaci da ake wannan bukukuwa, ƙasar ta samu cigaban a wasu fannoni da dama. An samu yawaitar makarantu manya da ƙanana, an samu ƙarin yawan asibitoci da faɗaɗar birane. A yanzu haka ana hasashen yawan al'umar Najeriya ya doshi miliyan ɗari biyu. Wannan yawa na al'umma Najeriya yana ƙarawa ƙasar ƙima, inda ƙasashen duniya kan yi ƙoƙarin kutso kai don ko ba komai akwai kasuwa.


Amma a wannan lokaci da ake ciki na cigaban duniya, ina Najeriya ta dosa ne? Koda ba a rusa harsashin da magabata suka dasa ba, kamata ya yi a wannan ƙarni a ce an fahimci ina ake a ƙasar da inda aka dosa. Domin an shiga wani sabon lale na yadda ake tafiyar da duniyar. Su kan su ƙalubalen da ake fuskanta sun sha banban da wanda al'umar baya suka fuskanta.


Shin wane tsari ne aka yi wa ƙasar da ake burin cimmawa? Tsari da zai kawo wani tsani da ƙasar zata tattaka har ga inda ake burin zuwa.


A lokacin shugaban ƙasa Janar Sani Abacha, ya fito da tsari na Vision 2020, wanda da an tafiyar da shi yadda aka tsara a wannan shekara da ake bikin shekara sitti za a kai ga ƙololuwar ribatar abin da aka shuka.


Shin haka za a ta yin gwamnatoci, kowa ya zo da tsarinsa, idan ya gama ya tafi da abin sa babu ɗorawa ko cigaba? A baya mun ga yadda aka yi wasu tsare-tsare irin su Green Revolution da Operation Feed the Nation da Structural Adjusment Programme (SAP), da Seven Points Agenda. Dukkanninsu ba su bada ainahin abin da ake buƙata ba.


A yanzu maganar da ake shugaba, Muhammadu Buhari ya kafa kwamiti da zai tsarawa ƙasar wani sabon harsashi da za a ci moriyarsa a 2050. Shin ta ya ya za a tabbatar wannan yunƙuri zai haifar da ɗa mai ido, tun da a karatun baya babu riba a tsare-tsaren da aka gudanar? Ai ba a kai ga cin moriyarsu ba aka yi watsi da su, duk da uwar dukiyar da aka narka akansu.


Shi kenan haka za mu ta yin bundun-bundun muna lalube a duhu, bayan muna cikin ƙarni na ashirin da ɗaya da komai ana yin sa bisa doren ilimi da lissafi? Shi kansa tsarin mulkin ƙasa mun ɗauko tsari Birtaniya na Parliamentary, daga baya aka watsar da shi aka koma tsarin Presidential. 


To shi kansa tsarin Amurka na Presidential, wanda ake da shugaba mai cikakken iko ba mu iya gudanar da shi ba yadda yakamata. Domin a tsarin, koda shugaba na da iko bai isa ya rusa wani tsari da aka gina ƙasar akai ba. A yau shugaban Amurka duk jin ikonsa, bai isa ya aiwatar da wani ƙudiri da ya sauka akan turbar da aka gina Amurka ba, koda kuwa daga wacce jam'iyya ya fito. 'Yan majalisu ba sa zama 'yan amshin shata kamar yadda namu suke.


Haka baiwar da Allah ya yi wa Najeriya za ta tafi a banza? Haka za a banzatar da arziƙin al'umma da ƙasar noma da ɗinbin ma'adinai, sai dai wasu su sha bunƙasa daga arziƙinmu. 


Ƙasashen da ake sa mu a layi ɗaya a ɓangaren cigaba irin su Indiya da Brazil sun sha gabanmu fintinkau. An wayi gari can muke zuwa neman ilimi da lafiya da kasuwanci tare da yawon buɗe ido. Hatta ƙasashe irin su Dubai da Malesiya sun zama abin misali a fagen cigaba.


A yau muna gudanar da mulkin siyasa a Najeriya, amma sai ya zamo mun fahimci siyasar a baibai. Komai mun maida shi siyasa, da abin da ya dace da wanda bai kamata siyasa ta shiga ba. Siyasa a harkar tsaro, siyasa a harkar aikin gwamnati, siyasa a makarantu, siyasa a gurin zaɓen cancanta. A tsawon wannan lokaci, waɗannan matsaloli sai ƙaruwa suke.


Cutar kai da rashin yin abin da ya dace ta sa mun wayi gari mun tsinci Talatarmu a Laraba. Lalacewar tsaro ta yi tsamari, 'yan tada ƙayar baya sun addabi ƙasar. Fashi da makami da garkuwa da mutane ya yawaita. Cin hancin da rashawa sun zama ruwan dare, talauci da masu zaman banza sai ƙaruwa yake. Rashin imani a zuciya da lalacewar tsarin gudanar da mulki shi ma ya dabaibaye ƙasar. 


A wannan lokaci da ake bikin cikar shekaru sittin da samun 'yancin kai, ya zama wajibi ga wanda jagorancin ƙasar yake hannunsu su sake lale. Dole ne a yi kallo da idon basira tare da amfani da ilimi wajen sauyawa ƙasar alƙibla. 


Ƙasar Najeriya na gaba da kowa, makomarta ce farkon abin dubawa ba masalaha ko burin wasu ba. Yakamata kwamitin da shugaban ƙasa ya kafa na samar da mihimman tsare-tsare ya ƙunshi mutane da yawa dake da ruwa da tsaki akan turakun ƙasar da sauran ɓangarorin gudanarwa da suka shafi al'umma.


Dole idan wannan tsari ya fito ya zama doka kuma wajibi a aiwatar da shi, koda kuwa za a samu sauyin gwamnati. Allah ya taimaki Najeriya ya ɗaukakata a duniya.


Zaharaddeen Ibrahim Kallah

zikallah@gmail.com

Twitter: @zikallah

Wednesday, 16 September 2020

Tun Ran Gini Tun Ran Zane: Lalacewar Tarbiyya Da Inda Aka Dosa

A yau mun wayi gari rayuwa a ƙasar Hausa ta sauya, tarbiyar yara ta lalace. Kawaici, yakana da kara da aka san mu da su, sun ɓalɓalce. Wannan ya sa muka shiga ruɗani, har ta kai muna neman manta su wane ne mu. A lokaci guda, fatara da talauci, sace-sace da zaman banza suka yi mana katutu.

A ƙasar Hausa, a ƙarni na 19 zuwa wani lokaci a ƙarni na 20, za ka ɗorawa tsohuwa kwarya cike da kuɗi ko gwala-gwalai daga wani ɓangare na gari zuwa ƙarshensa, ba tare da wani ya tare ta ba ya kwace. Amma yanzu ta kai akan bainar idon jama'a ne za a yi maka kwace ko fashi, babu wanda zai kawo maka ɗauki.

Shekaru kamar biyu baya, na ji muryar wani matashi yana kuka a gidan Freedom Radio, yana cewa a bakin ƙofar mata cikin cunkosa jiran a basu hannu, wasu matasa suka sa masa wuƙa akan ya basu wayar salularsa. 

Matashin ya yi ƙoƙarin yi musu gardama, ya fara kururuwa yana kiran ɗaukin jama'a, amma babu wanda ya kawo masa ɗauki. Nan suka yanke shi a hannu suka yi awon gaba da wayarsa. Hakan ya sa ya shigo gidan radiyon yana kuka, yake cewa "Kai jama'a, kamar ba garin musulmai ba."

Haƙiƙa da gaskiyarsa, garin Kano garin musulmi ne da aka gina shi abisa doron dangantaka da kyakkyawar makwabtaka. Abin da ya shafi makwabcinka ya shafeka gaba da baya. Tun daga tarbiyar yara, kasuwanci da tattalin arziƙi, da addini, tsaro da sauran abubuwan da suka shafi zamantakewa. 

To, amma yanzu abin ba haka yake ba. Tun da Turawan mulkin mallaka suka shigo Daular Usmaniyya, muka fara yin watsi da kyawawan ɗabi'u da al'adunmu. 

Duk wannan abin da ake, Turawan Birtaniya sun yi mulki ne na bayan fage, wato 'Indirect Rule'. Sun fahimci a lokacin irin matsalolin da za su fuskanta idan suka taɓa mana addini da al'adu.

A yau a karan kan mu, mun yi watsi da waɗannan kyawawan ɗabiu, mun rungumi na baƙin haure. Duk nacin mu fa, ba za mu iya zama Turawa ba, ko yin abin da suke a al'adunsu. Sai dai idan za mu sauka daga tsari da tarbiyar musulunci da ta iyaye da kakanni.

A wajen tarbiyyar 'ya'yanmu, a yau makwabci ba zai iya saka baki akan tarbiyar ɗan makwabcinsa ba. Sannan yaran makwabta za su iya zama ba karatun boko bare na addini, ba tare da damuwar makwabci ba.


Ta ɓangaren sana'a, ba ma koyawa 'ya'yan makwabta yadda za su dogara da kansu. Rayuwa ta zama kowa ya iya allonsa ya wanke.

Da yawan 'yan boko da suka zama baƙaƙen Turawa na jin haushi talakawa da ba su rungumi tsarin rayuwa na zamani ba. Ina da matata ɗaya da 'ya'ya uku, amma makwabcina ya tara mata huɗu da 'ya'ya ashirin a gidan haya, wanda wasu ma tare suke kwana da yaransa a ɗaki ɗaya.

Shi ma talaka na jin haushin 'yan boko kan cewa ba su da tausayi, kuma suna yi masa buƙulun jin daɗi ɗaya da yake morewa, na ya yi jima'i yadda yake so.

Wannan ya haifar da rashin jituwa da watsi da juna, har da kai an raunana makwabtaka, an wargaza harsashin tarbiya. 

Mun san yadda manzon Allah, Annabi Muhammadu (S.A.W) ya dinga bijirowa da sahabbai mihimmanci makwabtaka, har suka yi tsammani zai ce makwabci zai iya gadar makwabcisa.

Duk wannan sakacin da riƙon sakainar kashi da muka yi, shi ya kai mu ga halin da muke ciki a yanzu.

A yau matasa da suke da mafi rinjaye na yawan al'umarmu ba su da sana'a, uwa uba ba su samu cikakkiyar tarbiya ba. Wannan shi ya ƙara assasa shaye-shayen miyagun kwayoyi da suke taimakawa wajen aikata muggan laifuka.

A yanzu a garuruwanmu, musamman Kano da take babban birni kuma cibiyar mutanen Arewa, sace-sace da kwace a gurin waɗannan matasa ya ƙara ta'azzara. Akan wayar da ba ta fi N15,000 ba, za a iya kashe mutum. Satin da ya gabata mun ji labarin yadda aka kashe wani bawan Allah a unguwar Jan Bullo. Unguwar da ake ganin mazaunanta akasari ba talakawa ba ne tiƙis. 

Ta kai yanzu ana bada shawara ga mutane da su kiyayi bin wasu tituna a Kano a wasu lokuta, musamman lokutan da ƙafa ta ɗauke.

Bai fi sati biyu ba, ƙanina ya shigo babur ɗin A Daidaita Sahu, inda ya samu wata budurwa a ciki. Matuƙin babur ɗin na tare da abokinsa, wanda suke sawa a gefen direba. Suna tafe, sai wannan yarinya ta ce za ta sauka. Bayan ta sauka ne, mai babur din yake cewa abokinsa ai budurwar ga irin wayar da take riƙe da ita. 

Buɗar bakin da abokin zai yi, sai ya ce. "Ai ba ka gaya mun ba, amma wallahi da mun kwace ta." 

Jin haka ƙanina ya ce akwai mai sauka, nan ya sauka daga babur ɗin.

Wannan ita ce irin rayuwar da matasanmu ke faɗawa. Shin a haka za mu cigaba, shin me zai faru nan da shekaru ashirin masu zuwa? 

Dole mu sake tunani matuƙar muna son samun mafita.

Ana bawa mutane shawara akan yadda za su kare kan su, amma gaskiya abin ya wuce haka. Dole masana da shugabanni da duk.masu ruwa da tsaki su zauna babban taro da zai waiwayi matsalar da muke ciki, a tattauna tare da fitar da hanyoyi na ilimi da za a magance matsalar matasa. Sannan dole a zaɓi mutane da za su iya aiwatar da abin da aka fitar a bayan taron.

Duk inda za a kai a kawo, sai an yi ƙoƙarin kyautata zamantakewar mu, sannan a tsara yadda 'yan boko da masu arziƙi da talakawa za su fahimci juna, su yi aiki tare.

Dole ne mu fitar da yadda matasanmu za su samu ilimi da sana'oi. Mutumin da ya shekara sittin ko sama, idan bai samu abin da zai ci ba, zai yi wuya ya ɗau makami. Domin ba shi da ƙarfin jiki da zuciyar da zai yi haka. Amma matashi mai jini a jika, abu ne mai sauƙi a gun sa.


Zaharaddeen Ibrahim Kallah

zikallah@gmajl.com

Twitter/Instagram @zikallah


Kafuwar Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo


A watan Janairu, 1939 aka fara buga jaridar 'Gaskiya Ta Fi Kwabo'. An yi tunanin kafa ta ne don a yi martani ga farfagandar da Jamus da Hitler suke yaɗawa a yaƙin duniya na biyu da ake gwabzawa. 

An nemi Abubakar Imam ya zama editan jaridar, wanda a lokacin yana koyarwa a Katsina. An ƙara masa albashi daga fam shida da silai goma zuwa fam takwas, don a ƙarfafe shi ya karɓi aikin.

Jaridar ta maye tsohuwar jaridar da ake da ita a lokacin mai suna, 'Jaridar Nijeriya Ta Arewa' (Nothern Nigerian Newsletter), wacce ake buga ta a maɗaba'ar Gwamnatin Gargajiya ta Kano (Native Authority Kano). 



Mr L.C Giles da yake shugaban gudanarwa a Literature Bureau ya nemi shawarar Abubakar Imam ko za a sa wa jaridar suna 'Kwabo Kwabo' ko 'Kawo Kuɗi' ko kuma 'Daɗin Nazari'. Amma da Abubakar Imam ya iso Zariya, ya bada shawarar raɗa mata suna 'Gaskiya Ta Fi Kwabo' wanda shi ne sunan da aka amince da shi.

Jaridar ta fara da ƙafar dama, domin ba ya ga mayar da martani ga farfagandar Jamusawa, an shigo da labarai da rahotannin gida, wanda suka shafi wayar da kan talakawa akan ayyukan gwamnati da na masarautu. 

Zadeen Kano

Monday, 14 September 2020

Tasirin Marubuta Da Gudunmawarsu A Ƙani Na 21


Tun lokacin jahiliyya, marubuta na da mihimmanci a al'umma. Domin kowacce ƙabila na da marubutanta na musamman. A wannan lokaci, duk ƙabilar da ba ta da marubuta, yakan zama abin gori da koma baya a gare su. 

Da rubutu ne, musamman waƙa suke isar da saƙonni. Koda an taɓa ƙabilarsu, kafin a ce abu ya kai ga ɗaukar makami, marubuta ne za su fara mayar da martani.

An yi wani fitatcen mawaƙi kafin zuwa musulunci a ƙasar Larabawa da ake kira Zuhayr Bin Abi Sulma, wanda ya fito daga Banu Muzaina. Wata waƙa da ya rubuta akan haɗa kai da daina ɗaukar fansa akan yaƙe-yaƙen Larabawa ta yi shaharar da ta ɗaga mutunci da martabar ƙabilarsu. Wannan waƙa sai da aka rubuta ta da ruwa gwal aka rataye a ɗakin Ka'aba. Wanda a baya ƙabilarsu ba ta kai matsayin waɗanda suke cikin mawaƙan da ake rataye rubutunsu a Ka'aba. Saboda ɗaga darajar ƙabilarsu, sai da ya zamo duk wata bazawara a wannan ƙabila an aureta. 

Marubuta sun kasance mutane ne masu daraja a al'umma, saboda sune fitila dake haskawa al'umma yadda rayuwa ta sa gaba. Mutane ne masu hikima da fikira tare da hangen nesa. Akoyaushe suna ƙoƙarin nazartar al'umma, walau ta hanyar karace-karance ko ta nazari, kula, bibiya da tariyar baya.

A wannan zamani ma haka abin yake, domin samuwar marubuta ya taka rawa a tarihin cigaban duniya. Marubuta iri-iri sun bayar da gudunmawa, waɗanda suka ƙunshi marubutan wasan kwaikwayo, rubutun zube ko na waƙa. Kai har da marubuta a ɓangaren aikin jarida da marubutan da ba na rubutun ƙirƙira ba.

Irin waɗannan gudunmawa ta shafi ɓangarori da dama da suka shafi tattalin arziƙi, da siyasa, zamantakewa, addini da al'ada, tsaro, da ilimin sana'oi, ilimin kimiyya da fasaha da sauransu.

A wannan ƙarni na 21, abubuwa sun sauya a tarihin duniya. An shiga wani zamani da Turawa suka yi wa laƙabi da globalisation, wanda aka ɗauki duniya kamar wani ƙaramim ƙauye ne da kowanne ɓangare ya san me ɗan uwansa yake ciki, ko kuma abin da ya shafi mutum ɗaya ya shafi mutane da yawa. 

A yau, a wannan duniya da muke ciki, matsalar tsaro ta shafi kowanne ɓangare. Domin idan wata ƙasa ta shiga rikici da yaƙe-yaƙe, kafin wani lokaci sai ka ji ɓullar su a wata ƙasa. Misali, ƙasar Libya ta shiga halin yaƙi da taɓarɓarewar tsaro, wanda kafin wani lokaci, rikici da yaƙe-yaƙe sun yaɗu a wasu sassa na Afirika dake maƙwabtaka da su.

A yau matsalar sace-sace, fashi da makami, da satar mutane, fyaɗe da shaye-shaye ya zama matsalar kowa. Abubuwan da a tarihi wasu yankuna ba su san da su ba, yanzu sun addabe su. Ko a wannan lokaci da cutar Korona ta ɓulla a ƙasar Chana, ta gama game duniya, saboda cigaban da aka samu ta kowacce fuska da kasancewar duniya abu ɗaya.

A cikin wannan tafiya da ake ta sabuwar duniya a ƙarni na 21, samun bayanai da ilimi ya zama kamar ƙiftawar ido, duba ga cigaban da aka samu a kafofin sadarwa na yanar gizo da fasahar zamani a ɓangaren na'ura mai kwakwalwa. Wannan cigaban ya game kowanne ɓangaren rayuwar al'umma.

A wannan lokaci, wacce irin gudunmawa marubuta za su bayar wajen cigaban al'umma? To, gudunmawar da za su bayar ba ta da banbanci da wadda magabata suka bayar a baya. Amma a wannan zamani dole salo da tsarin isar da saƙon ya banbanta. Dole marubuta su tafi da zamani, idan suna son yin tasiri a wannan tafiya ta sabuwar duniya.

Da farko dai sai marubuta sun tafi da kafofin sadarwa na zamani da ake da su irin su Facebook, Twitter, Youtube, Instagram, linkedin, whatsapp da sauransu. A yau akwai ɗinbin manhajoji da ake hada-hada a cikinsu, wanda rubutu na kan gaba a wannan tafiya.

A cikin waɗanna kafofin sadarwa, akwai miliyoyin al'umma, wanda babu irin sharar da ba za ka samu ba. Don haka, wajibi ne marubuta su banbanta da ɗinbin mutanen dake cikin wannan kasuwa. To amma, ta ya ya za su banbanta kansu a cikin tarin mutanen dake cikin wannan tafiya?

A nan dole ne matsayinsu na masu ilimi da bincike, kuma fitilar al'umma ya yi tasiri a zuciyarsu. Wannan shi ne zai yi musu alƙibla, ya zamo duk wani abu da zai fito daga maɗallin kwamfutarsu ya zamo rubutu ne da ya sha banban da game gari. 

Dole a samu bincike, nazari, kula, bin diddigi da bibiya a cikin rubutunsu. Wannan shi zai zama gishiri ko magin rubutu, wanda zai gamsar da mai karatu.  

A nan ban yi amfani da kalmar gishiri da magi a yadda ake fassara kalmomin a rubutu ba. A'a, ina nufin dukkan abubuwa da zai gamsar da mai karatu, ya tsima shi tare da riƙe shi ko jan hankalinsa, da bashi ainahin hoton abin da marubuci ke son isarwa.

Idan kana rubutu akan rashawa da cin hanci, za ka yi nazari sosai tare da bin diddigi, yadda idan rubutun ya fito, ƙarya ne wanda aka yi akansa ya musanta. Wani marubuci Abdulaziz A. Abdulaziz, ya yi rubutu akan wata tsohuwar minista a Najeriya akan sahihancin takardun da suka sahale mata hidimar ƙasa. Wannan rubutu  da ya amsa sunansa, sai da ya yi sadadiyar wannan minista ta yi murabus. 

Haka ma wani marubucin ɗan ƙasar Ghana Anas Aremeyaw Anas da ya kware akan rubutun bincike da bin diddigi, ya bankwaɗo aikin rashawa da cin hanci a ɓangaren wasanni, wanda hakan ya yamutsa hazo sosai. Wannan bincike na shi ya sa wasu shugabanni da masu horarwa suka rasa kujerunsu. 

Irin wannan salo yakamata marubuta su yi amfani da su wajen bada gudunmawa ga al'umma. Ana da buƙatar marubuta su yi rubutu akan abin da ya shafi mulki da gudanarwa, siyasa, shari'ah, tsaro, ilimi, kasuwanci da sauransu. Akwai abubuwa na daɗi da rashinsa sosai a wannan ɓangarori. Yin rubutu zai nusar da jama'a tare da kawo sabon tunani na cigaban da aka samu a duniya.

Wannan rubutu zai iya kasancewa na ƙirƙira, ko ba ƙirƙirarre ba. Idan ka yi rubutun ƙirƙira, dole ya kasance ka gabarta da jigonka akan dukkanin tsanikan rubutu, sannan a ƙarshe ka fitar da mafita ta hanyar da tsari da dokoki suka amince  da su. 

A ƙarni na 20 an ga irin gudunmawar marubuta irin su James Hadley Chase (Rane Lodge Brabazon) da Sidney Sheldon da Abubakar Imam da Chinua Achebe da Wole Soyinka suka bayar akan rayuwar da ake ciki a wannan lokacin. Marubuta a ƙarni na 21, sai a ce muku ga fili ga mai Doki.


Daga

Zaharaddeen Ibrahim Kallah 

zikallah@gmail.com

Twitter/Instagram @zikallah